Bayani Na Adalci kan Dangale Tufafi

·

·

Bismillahirrahmanirraheem
..Da yawa daga cikin mutane suna tuhumar wasu musulmai a dalilin dangale tufafinsu kada ya wuce idon sawu, ko kwabri. Wanda wannan kuskure ne, wasu masu tuhumar suna tuhumar ne saboda son zuciya wasu kuma sunayi ne saboda jahilci.. Sunji an fada suma sai suka fada. Saboda haka nake kira ga ‘yan’uwa musulmai masu wannan hali da suji tsoron Allah su daina. Domin hakan ka iya jawo musu fushin Allah. Domin hakika dangale tufafi kada ya wuce idon sawu sunnar annabi ce. Kuma annabi yace : ‘Duk wanda ya kyamaci sunnah ta toh baya tare damu’…. Wato a hakikanin gaskiya hadisai sunzo da yawa wanda suke nuna cewa annabi baya barin tufafinsa suja kasa.ko su wuce idon sawu Sannan kuma har umarni ma yayi da kada a bari tufafin su zarce idon sawu inso samune ma su tsaya a kwabri… Sannan wasu hadisan kuma suka nuna yayi maganane akan masu takama. Sannan abiinda yake bada faka ga masu son zuciya acikin wannan mas’ala itace duk hadisan da sukazo suna zuwa ne da kalmar kwarjalle… ‘Izaar’ amma basu zuwa da kalmar wando ‘sirwaal’ toh abinda ya dace mu fahimta anan shine lokacin annabi akwai wando. Amma da yawan mutane har shi kansa annabi suna amfani ne da kwarjalle. Toh inhar ansamu annabi a rayuwarsa ga irin tufafin da yasa. Kuma ga irin yanayin kalan tsarin da ya sakata. Toh mu abinda zamu lura anan tunda mu tsarin tufafinmu tasha bambam da tasu , zamu lura ne da tsarin da ya saka ta. Ga kadan daga cikin hadisan da suke fayyace mana zancen adalci game da tufafi .
ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺁﺩﻡ، ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺷﻌﺒﺔ، ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺳﻌﻴﺪ ﺑﻦ ﺃﺑﻲ
ﺳﻌﻴﺪ ﺍﻟﻤﻘﺒﺮﻱ، ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ ـ ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻨﻪ ـ ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ ” ﻣﺎ
ﺃﺳﻔﻞ ﻣﻦ ﺍﻟﻜﻌﺒﻴﻦ ﻣﻦ ﺍﻹﺯﺍﺭ ﻓﻔﻲ ﺍﻟﻨﺎﺭ.
Annabi(s.a.w) yace: ‘duk abinda ya wuce idon sawu na kwarjalle toh yana wuta’
Kaga wannan hadisi annabi bai nuna don takama ba.
Sannan kuma ya sake cewa.
ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺳﻌﻴﺪ ﺑﻦ ﻋﻔﻴﺮ، ﻗﺎﻝ ﺣﺪﺛﻨﻲ ﺍﻟﻠﻴﺚ، ﻗﺎﻝ
ﺣﺪﺛﻨﻲ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺑﻦ ﺧﺎﻟﺪ، ﻋﻦ ﺍﺑﻦ ﺷﻬﺎﺏ،
ﻋﻦ ﺳﺎﻟﻢ ﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ، ﺃﻥ ﺃﺑﺎﻩ، ﺣﺪﺛﻪ ﺃﻥ ﺭﺳﻮﻝ
ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ ” ﺑﻴﻨﺎ ﺭﺟﻞ ﻳﺠﺮ
ﺇﺯﺍﺭﻩ، ﺧﺴﻒ ﺑﻪ، ﻓﻬﻮ ﻳﺘﺠﻠﻞ ﻓﻲ ﺍﻷﺭﺽ ﺇﻟﻰ
ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ.
Annabi (s.a.w) yace: ‘wani mutum yana jan kwarjallensa. Sai Allah ya nitsar dashi. Yana cigaba da gangarawa har zuwa ran tashin qiyaama..
Toh kaga wa’innan hadisai sam basuyi magana kan taqama ba.
Sannan ya sake cewa:
ﻭﻋﻦ ﺃﺑﻰ ﺫﺭ ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ: “ﺛﻼﺛﺔ ﻻ ﻳﻜﻠﻤﻬﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﻮﻡ
ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ، ﻭﻻ ﻳﻨﻈﺮ ﺇﻟﻴﻬﻢ ، ﻭﻻ ﻳﺰﻛﻴﻬﻢ، ﻭﻟﻬﻢ
ﻋﺬﺍﺏ ﺃﻟﻴﻢ” ﻗﺎﻝ: ﻓﻘﺮﺃﻫﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺛﻼﺙ ﻣﺮﺍﺭ. ﻗﺎﻝ ﺃﺑﻮ ﺫﺭ : ﺧﺎﺑﻮﺍ
ﻭﺧﺴﺮﻭﺍ ‍ ﻣﻦ ﻫﻢ ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ؟ ﻗﺎﻝ” :ﺍﻟﻤﺴﺒﻞ،
ﻭﺍﻟﻤﻨﺎﻥ، ﻭﺍﻟﻤﻨﻔﻖ ﺳﻠﻌﺘﻪ ﺑﺎﻟﺤﻠﻒ ﺍﻟﻜﺎﺫﺏ” .
Mutane uku Allah bazaiyi musu magana ba, bazai kallesu ba, kuma bazai tsarkakesu ba, kuma suna da azaba mai radadi… manzon Allah ya fada sau uk: sai abu zarri yace: ‘sun tabe, sunyi hasara, suwaye wannan ya rasulillah? Sai yace
1. Mai jan tufafinsa ,
2. Mai Gori.
3. Mai cika mudunsa da rantsuwar karya.
Anan ma bai kira sunan kwarjalle ba, sannan bai kira sunan taqama ba.
Sannan a wata hadisin kuma.
ﻭﻋﻦ ﺃﺑﻰ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ: ﺑﻴﻨﻤﺎ
ﺭﺟﻞ ﻳﺼﻠﻰ ﻣﺴﺒﻞ ﺇﺯﺍﺭﻩ، ﻗﺎﻝ ﻟﻪ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ: “ﺍﺫﻫﺐ ﻓﺘﻮﺿﺄ” ﻓﺬﻫﺐ
ﻓﺘﻮﺿﺄ، ﺛﻢ ﺟﺎﺀ ﻓﻘﺎﻝ “: ﺍﺫﻫﺐ ﻓﺘﻮﺿﺄ” ﻓﻘﺎﻝ
ﺭﺟﻞ ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﺎ ﻟﻚ ﺃﻣﺮﺗﻪ ﺃﻥ ﻳﺘﻮﺿﺄ ﺛﻢ
ﺳﻜﺖ ﻋﻨﻪ؟ ﻗﺎﻝ: “ﺇﻧﻪ ﻛﺎﻥ ﻳﺼﻠﻰ ﻭﻫﻮ ﻣﺴﺒﻞ
ﺇﺯﺍﺭﻩ، ﻭﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻻ ﻳﻘﺒﻞ ﺻﻼﺓ ﺭﺟﻞ ﻣﺴﺒﻞ.
Abu huraira yace:’wani mutum yana sallah kwarjallensa yana jan kasa. Sai manzon Allah(s.a.w) yace tafi kaje kayi alwala, sai ya tafi yaje yayi alwala, ya dawo sai manzon Allah(s.a.w) yace: je kayi alwala. Sai wani mutum yace; ‘yaa manzon Allah meyasa kake umartanshi yayi alwala’ sai manzon Allah yayi shiru: sai yace: ‘ya kasance yana sallah tufafinsa yana jan kasa. Kuma Allah baya karban sallan mutum mai jan tufansa’….
Kunga anan ma bai kira sunan takama ba…kuma wannan hadisi tana da hadari sosai, domin annabi yaace ba’a karban sallan mai jan tufansa akasa. Bai kira sunan taqama ba.
Sannan kuma meyasa akece a dage tufa zuwa kwabri? Ga dalili.
ﻭﻋﻦ ﺃﺑﻰ ﺳﻌﻴﺪ ﺍﻟﺨﺪﺭﻯ ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ:
ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ: “ﺇﺯﺍﺭﺓ
ﺍﻟﻤﺴﻠﻢ ﺇﻟﻰ ﻧﺼﻒ ﺍﻟﺴﺎﻕ، ﻭﻻ ﺣﺮﺝ -ﺃﻭ ﻻ
ﺟﻨﺎﺡ- ﻓﻴﻤﺎ ﺑﻴﻨﻪ ﻭﺑﻴﻦ ﺍﻟﻜﻌﺒﻴﻦ، ﻓﻤﺎ ﻛﺎﻥ ﺃﺳﻔﻞ
ﻣﻦ ﺍﻟﻜﻌﺒﻴﻦ ﻓﻬﻮ ﻓﻲ ﺍﻟﻨﺎﺭ، ﻭﻣﻦ ﺟﺮ ﺇﺯﺍﺭﻩ ﺑﻄﺮﺍ
ﻟﻢ ﻳﻨﻈﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺇﻟﻴﻪ”.
Manzon Allah(s.a.w) yace: ‘kwarjallen musulmi tana tsayawa ne a kwabri, amma babu laifi ta tsaya a tsakaninsa da idon sawu. Duk abinda ya wuce haka toh yana wuta, sai kuma yace: ‘duk wanda ya ja tufarsa a kasa don taqama Allah bazai kalleshi ba, ma’ana ran tashin qiyama.
A wannan hadisin ta kunshi magana biyu ne, na farko baiyi magana akan jan tufa ba, yayi magana ne akan dangale ta. Akarshe kuma sai ya tike da maganar janta. A kula da wannan hadisin sosai.
Sannan kuma ga wata hadisi wanda zan tike da ita…
ﻭﻋﻦ ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻤﺎ ﻗﺎﻝ: ﻣﺮﺭﺕ
ﻋﻠﻰ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﻓﻰ
ﺇﺯﺍﺭﻱ ﺍﺳﺘﺮﺧﺎﺀ، ﻓﻘﺎﻝ: “ﻳﺎ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ، ﺍﺭﻓﻊ
ﺇﺯﺍﺭﻙ” ﻓﺮﻓﻌﺖ ﺛﻢ ﻗﺎﻝ: “ﺯﺩ”، ﻓﺰﺩﺕ، ﻓﻤﺎ ﺯﻟﺖ
ﺃﺗﺤﺮﺍﻫﺎ ﺑﻌﺪ. ﻓﻘﺎﻝ ﺑﻌﺾ ﺍﻟﻘﻮﻡ: ﺇﻟﻰ ﺃﻳﻦ ؟ ﻓﻘﺎﻝ:
ﺇﻟﻰ ﺃﻧﺼﺎﻑ ﺍﻟﺴﺎﻗﻴﻦ.
Dan umar yace: ‘na wuce gaba garen manzon Allah(s.a.w) acikin kwarjalle na akwai dan jaa sai annabi yace ya abdullah dage kwarjallenka. Sai na dage ta, sai yace: kara, sai na kara, ban gushe ba ina janta baya, sai wasu mutane sukace, zuwa ina? Sai manzon Allah yace: ‘zuwa kwabri’….
Saboda haka ‘yan’uwa inzamu kawo hadisai ne na maganar dangale tufa, kuma wanda babu kalmar taqama aciki suna da yawa amma bari mu tsaya anan… Sannan da yawa mutane suna mana mummunan fahimta na cewa mu muna dangale wando ne kawai, ko munace a dangale wando. A’a, tufafi ko wata irice ba’a yadda ka barta ta wuce idon sawu ba. Riga ce ko wando…
Sai kuma duk maison bin gaskiya sai ya koma cikin littafin malamin hadisinnan. annawawy..’Riyadussaliheen’ yayi babi wanda sunan babin kawai inka fahimta zai yaye maka duk shubuhar da kake tattare dashi’ ku duba kitabullibaas. Babi na 119. Shafi na 251. Ku bincika ku gani. Allah yasa mudace… Domin akwai hadari kaga muatane suna yaqi da sunnar annabi…
Sannan sannan daga karshe akwai wasu suna ganin irin wa’innan rubuce rubucen da suka shafi aqeedah bai dace adinga rubutasu ba domin a ganinsu, zai jawo rarrabuwar al’ummah. Ba haka bane, da al’ummah ta hadu akan karya gwanda bata hadu ba. Kuma a irin wannnan maganganun ne wasu ke fahimtar addini, in aka samu ja inja. Wannan yace kaza wannan yace kaza sai ayi bayaani. Wanda yafi hujjah sai ya sami nasara…. Allah ya taimakemu.

10 responses to “Bayani Na Adalci kan Dangale Tufafi”
 1. sagiru ibrahim Avatar
  sagiru ibrahim

  Ina yi maka Addu’a,Ta fatan Alkairi,Allah yakaramuku Basira da wayar da kan mutane da kukeyi.Allah yanuna mana Gaskiya,Gaskiyace yabamu ikon yin aiki da’ita.Allah yanuna mana Qarya,Qaryace yabamu ikon Qaurace mata.Allah ya yafemana kura-kurenmu.

 2. Adam abualamin Avatar
  Adam abualamin

  ALLAH YASAKA DA ALHERI YAKARAMANA RIKO DA SUNNAR ANNABI S A W.

 3. guziri Avatar

  Jazakallahu Khair

 4. Habib Alhaji Avatar

  Assalam warahmatullahi ta’ala wabarakatuhu, bayanhaka hakika a’irin wannan rayuwar damuke ciki yaxamawajibi mugyara tsakanimmuda Allah (s.w.a) tayarda daxaka tambayi wanda yadamfarewa Allah yakiyaye dokokinsa sannan yakebin duk abin da yai’umarni, xakasameshi cikin nutsuwa dawalwala,watakila kuma kokeke bashidashi, amma wanda shiyarabuda Allah yata6e sannan yayi’asara, shikenan cikin kunci bawalwala arayuwarsa, komeyake dashibaya wadatarsa, kuma koduniyar xa’abashi baxatawadace shiba, xakaganshi cikin xundumemiyar mota ga easi amma ioyay wani gwaurannumfashin gumiyake, dukmeyajawo wannan rashin akida da tauhidi ganiyake dabararsa datsarinsa shike kawonutsuwa, yabikururur shaidan, yan uwana mubi Allah muxauna lafiya, musami nanduniya sannan musami lahira, Allah yasamu dace, Amin.

 5. Nibras Avatar

  Ameen. Allah Ya saka muku da Alheri.

  1. Abdurahman Avatar
   Abdurahman

   Allah taimaki duk mai taimakon muslunci

 6. Abdurahman Avatar
  Abdurahman

  Godiya ya tabbata ga ALLAH da bamu Muslunci

 7. Sani Taheer Kobi Avatar
  Sani Taheer Kobi

  Allah madaukakin sarki ya saka muku da alkhairi.

 8. NAFIU SANI Avatar

  ALLAH YATAIMAKI DA AWAR SUNNAH KUMA YA ALBARKACETA
  KUMA YABA MU IKON BITA KAREMU KARMUFADA SHIRKA DA BI,DI,AH DA FASIQANCI
  YAJIQAN MALAMAN MUSULUNCI WANDA SUKA GA BATA
  YATAI MAKI WANDA SUKERAYE YAKARESU DAGA SHARRIN YAHUDU DA NASARA
  ALLAHU AKHABAR

 9. Abu Jafar sakpe Avatar
  Abu Jafar sakpe

  sallam Allah ya sakawa mallam da alheri. Ama ina ba mallam shawara ya editing, ya inserting sunaye Hadith da nanbobesu for easy references.

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: