FADAKARWA KAN BID'AH!!!!!

·

·

FADAKARWA KAN BID’AH!!!!!
‘YAN’UWA GA WATA SABUWA!
وفي الكتاب الإمام إبن زكريا يحيى بن شرف ألنواوي في شرح الحديث النهي عن البدعة. ألحديث المشحور، حديث أمنا عائشة‎ ‎ألذي رواه الإمامين ألبخاري ومسلم في صحيحيهما. قالت قال رسول الله صلى الله عليه وسلم(من أ حدث في أمرنا هذا ما ليس منه فهو رد.) قال الشيخ (أي من أحدث في الإسلام ما ليس من الإسلام في شيئ ولم يشهد له أصل من أصوله فهو مردود ولا يلتفت إليه. وهذا الحديث قاعدة من قواعد الدين الجليلة فينبغي حفظه وإشاره في إبطال المحدثات والبدع) .
Acikin Littafin malamin Hadisinnan Annawawi, a karkashin sharhin hadisinnan wanda ya shahara wanda yake hani da bid’ah. Hadisin ummuna Aisha(r.a) tace: manzon Allah(saw) yace: ‘duk wanda ya kirkiro wani abu ya sanya cikin wannan lamari namu na addini wanda baya cikinsa toh an mayar masa.’ Sai akace: ‘duk wanda ya kago wani abu ya sanya cikin addinin musulunci wanda kuma babu wannan abu aciki sannan bashi da wani asali da zai danganta wannan abu zuwa gareshi, wannan abu ya zamto abune wanda za’a mayar masa sannan bazama akoma a kalleshi ba. Sannan kuma wannan hadisi ta zama ka’ida daga cikin ka-dojin addini daukakakkiya yana zama tilas kiyayeta da kuma nuni dashi wurin bata duk wasu sababbin abubuwa da bid’oi. Haka take a rubuce kaman yanda kuka gani, ku duba riyaadussaliheen shafi na 77. Saboda haka ‘yan’uwa musulmai nake kira a gareku da ku zamto wayayyu a addini, ku zamto masu budaddun zukaata wurin karban gaskiya.
Haka kuma sanannen malaminnan wato imam malik, ga zancensa game da bid’ah…
Yace: ”duk wanda ya kirkiri bid’ah ya kirata kyakkyawa toh tamkar yana riya cewa annabi ya ha’ince annabtan da aka bashi ne bai isar duka ba’ sannan ya sake cewa ‘duk wani abu da bai zama addini ba lokacin annabi toh yanzu bashi yiwuwa ta zama addini’ duba al-I’tisaam kasha mamaki.
Sannan a aqeedah ta imam malik mai bid’ah ko sallama baza ayi masa ba. Duba A l-Ibaanah na ibn Battah,
441. Toh ‘yan’uwa masu girma ku dubi irin wa’innan zantuka masu tsada… A hakikanin gaskiya akan wannan mas’ala ta bid’ah ansamu tsabani sosai tsakanin ‘yan’uwa musulmai wanda wasu suke ganin cewa akwai bid’ah mai kyau, akwai wasu kuma da suke ganin babu wata bid’ah mai kyau. Toh a hakika ‘yan’uwa in za’abi ka’ida ta addinin musulunci, babu wata bid’ah kyakkyawa. Duk wata bid’ah acikin addini batace…
Manzon Allah(saw) yace kullu bid’atin dalaala. Saboda haka dole mu dauki wannan ka’idar. Domin inka duba zakaga toh shin yaushe muka kammala da duk abinda annabi yazo mana dashi da har zamuyi shisshigi mu kirkiri naamu?ga wata hadisi ta Manzon Allah(saw)
ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺇﺳﻤﺎﻋﻴﻞ، ﺣﺪﺛﻨﻲ ﻣﺎﻟﻚ، ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺍﻟﺰﻧﺎﺩ،
ﻋﻦ ﺍﻷﻋﺮﺝ، ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ، ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ ” ﺩﻋﻮﻧﻲ ﻣﺎ ﺗﺮﻛﺘﻜﻢ، ﺇﻧﻤﺎ
ﻫﻠﻚ ﻣﻦ ﻛﺎﻥ ﻗﺒﻠﻜﻢ ﺑﺴﺆﺍﻟﻬﻢ ﻭﺍﺧﺘﻼﻓﻬﻢ ﻋﻠﻰ
ﺃﻧﺒﻴﺎﺋﻬﻢ، ﻓﺈﺫﺍ ﻧﻬﻴﺘﻜﻢ ﻋﻦ ﺷﻰﺀ ﻓﺎﺟﺘﻨﺒﻮﻩ، ﻭﺇﺫﺍ
ﺃﻣﺮﺗﻜﻢ ﺑﺄﻣﺮ ﻓﺄﺗﻮﺍ ﻣﻨﻪ ﻣﺎ ﺍﺳﺘﻄﻌﺘﻢ.
Manzon Allah yace.Ku barni kan abinda nabarku akai, domin abinda ya halaka wa’inda suke gabaaninku tambayoyinsu, da kuma tsabawa annabawansu. Duk abinda na hanaku ku gujeshi, abinda kuma nayi muku umarni ku kawoshi dai dai gwargwado.
To ku duba fa ku gani ‘yan’uwa annabi yace babu wata bid’ah mai kyau kai kaazo kace akwai, kaga ka tsabawa annabi. Sanan kuma acikin ayah Allah yake cewa:
ﻭﻣﻦ ﻳﺸﺎﻗﻖ ﭐﻟﺮﺳﻮﻝ ﻣﻦ ﺑﻌﺪ ﻣﺎ ﺗﺒﻴﻦ ﻟﻪ ﭐﻟﻬﺪﻯ
ﻭﻳﺘﺒﻊ ﻏﻴﺮ ﺳﺒﻴﻞ ﭐﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﻧﻮﻟﻪۦ ﻣﺎ ﺗﻮﻟﻰ
ﻭﻧﺼﻠﻪۦ ﺟﻬﻨﻢ ﻭﺳﺎﺀﺕ ﻣﺼﻴﺮﺍ.
Allah(s.w.t) yace: ”Duk wanda ya tsabawa manzon Allah(s.a.w) bayan shiriya ta bayyana a gareshi ya kuma bi tafarkin da ba na muminai ba, zamu jibinta masa abinda ya jawo wa kansa, sannan mu shigar dashi jahannama, makoma tayi muni”. Toh ya dace ‘yan’uwa musulmai mu kula mudinga bin abu bisa ka’ida kada wani ya rudamu…
Sannan akwai wasu masu bin son zuciya, inkace musu duk bid’ah batane toh sai suyi ta kawo maka tawilce tawilce wanda bashi da asali, ko suce maka toh ai kaima kana bid’ah. Toh shikenan don inayin bid’ah ta zama maka hujjah kaima kayi? Ko kuma ka samu wasu suna kawo wani
zance wanda irin wannan zancen kawoshi ma jahilci ne, misali wa’inda basu ma fahimci ainihin me ake nufi da bid’ah ba. Sai su rika cewa… Toh kana shiga jirgi kaje makkah, kana yin visa kaje makka kuma duka annabi baiyi ba. Ko suce shiga mota ko amfani da waya da dai sauran shirme da suke kawowa. Toh irin wannan sai mu basu uzurin jahilci. Domin in akace bid’ah babu kyau toh ana zancen bid’ah cikin addini ne ba ta duniyarmu ba.. Abinda ya shafi duniyarmu annabi ya bamu cin gashin kai yace ‘ku kukafi sani game da lammurar duniyarku, saboda haka wani yazo ya lissafo bid’ar duniya cikin jerin munanan bid’ah wannan jahilci ne. Ko kuma su kawo maka karshen nassin hadisin umar(r.a) da yace ni’imatil bid’ati haazihi sai su tsaya anan. Kaga duk wanda ya kawo irin wannan zance a bisa dalili na kirkirar bid’ah toh ya cancanci hukunci…ga nassini hadisin cikakke da suke boyewa
‘ﻭﻋﻦ ﺍﺑﻦ ﺷﻬﺎﺏ، ﻋﻦ ﻋﺮﻭﺓ ﺑﻦ ﺍﻟﺰﺑﻴﺮ، ﻋﻦ ﻋﺒﺪ
ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻘﺎﺭﻱ، ﺃﻧﻪ ﻗﺎﻝ ﺧﺮﺟﺖ ﻣﻊ
ﻋﻤﺮ ﺑﻦ ﺍﻟﺨﻄﺎﺏ ـ ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ـ ﻟﻴﻠﺔ ﻓﻲ
ﺭﻣﻀﺎﻥ، ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ، ﻓﺈﺫﺍ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺃﻭﺯﺍﻉ
ﻣﺘﻔﺮﻗﻮﻥ ﻳﺼﻠﻲ ﺍﻟﺮﺟﻞ ﻟﻨﻔﺴﻪ، ﻭﻳﺼﻠﻲ ﺍﻟﺮﺟﻞ
ﻓﻴﺼﻠﻲ ﺑﺼﻼﺗﻪ ﺍﻟﺮﻫﻂ ﻓﻘﺎﻝ ﻋﻤﺮ ﺇﻧﻲ ﺃﺭﻯ ﻟﻮ
ﺟﻤﻌﺖ ﻫﺆﻻﺀ ﻋﻠﻰ ﻗﺎﺭﺉ ﻭﺍﺣﺪ ﻟﻜﺎﻥ ﺃﻣﺜﻞ. ﺛﻢ
ﻋﺰﻡ ﻓﺠﻤﻌﻬﻢ ﻋﻠﻰ ﺃﺑﻰ ﺑﻦ ﻛﻌﺐ، ﺛﻢ ﺧﺮﺟﺖ
ﻣﻌﻪ ﻟﻴﻠﺔ ﺃﺧﺮﻯ، ﻭﺍﻟﻨﺎﺱ ﻳﺼﻠﻮﻥ ﺑﺼﻼﺓ ﻗﺎﺭﺋﻬﻢ،
ﻗﺎﻝ ﻋﻤﺮ ﻧﻌﻢ ﺍﻟﺒﺪﻋﺔ ﻫﺬﻩ، ﻭﺍﻟﺘﻲ ﻳﻨﺎﻣﻮﻥ ﻋﻨﻬﺎ
ﺃﻓﻀﻞ ﻣﻦ ﺍﻟﺘﻲ ﻳﻘﻮﻣﻮﻥ. ﻳﺮﻳﺪ ﺁﺧﺮ ﺍﻟﻠﻴﻞ، ﻭﻛﺎﻥ
ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻳﻘﻮﻣﻮﻥ ﺃﻭﻟﻪ’
Allah yasa mudaace zan tsaya anan. Domin khairul kalaam ma qalla wa dalla walam yadul fa yumil…
Amma. Daga karshe inaso inja hankalin ‘yan’uwa masu karanta irin wannan post din da dun Allah akiyaye jawo husuma tsakaanin al’ummah. Inkakaranta baka gane ba sai ka nemi karin bayaani, inkuma ka gamsu dun Allah banda tawili. Wassalaamu alaikum. Allah ya kara wa annabi yarda.

2 responses to “FADAKARWA KAN BID'AH!!!!!”
  1. Umar Muhammad Avatar
    Umar Muhammad

    Assalamu Alaikum!
    Akwai mutanen da suke kawo hujjar cewa sahabbai ma sun yi bidi’a. Misali suna cewa Ibn Abbas shi ya fara tafsirin Qur’an a masallancin Busra kuma Annabi bai yi ba. Ko kuma tabi’i ne ya rubuta hadithai, ko kuma saka ma dakin Ka’aba riga bayan mutuwar Annabi ne aka yi. Abin ya daure min kai.

  2. AlLAH KA NUNAMA NA GASKIYA GASKIYA CE KA BAMU IKON BINTA KA BAMU IKON GUJEWA A BIDI,A AMEEN MASU YINTA ALLAH KASHIRRESU ameeen

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: