Fadakarwa Zuwa Ga 'yan'uwa Musulmai

·

·

Domin neman ƙarin bayani danna nan

Assalaamu Alaikum ‘Yan’uwa musulmai, a zahiri kaman yanda muka sani akwai dadaddar gaaba tsakanin duk musulmi da kafiri, haka tsakaanin maison Gaskiya da wanda ke kiyayya da’ita gaskiyar. Wannan haka take gudana tun farko. Annabi yasha gwagwarmaya sosai wurin tabbatar da hasken Da Allah ya turoshi dashi, haka suma kuma kafirai da munafukai sukayi ta kokarin dishar da hasken Da Allah ya turo manzonsa dashi. Amma Allah ya kunyataasu ta yadda suna ji suna gani musulunci tazo ta mamayesu. Toh wannan kiyayya tana nan har abada tsakaanin duk musulmi da kafiri da munafuki. Wanda bazasu gushe ba suna amfani da duk wata dama da suka samu na su cutar da mumini . Dun haka ‘yan’uwa a kula, misaali. Arna makiya addini suna amfani da hanyar sadarwa ta zamani wurin yada abubuwa da zai tada hankalin musulmai ya bata musu rai, kaman yanda muka gani ya faru a kwanannan. Kwanakin baya yawancin masu bincike wanda ina daya daga cikinsu sunga wani fim da akayishi akaci zarafin annabi. Acikin fim din aka nuna wai cewa annabi yana wuta, acikin fim din aka nuna cewa yana ta wasu kalamai wanda basu da dadin ji. Kiyayewar Allah wannan fim din bai yadu kowa yaganshi ba. Banda wanda akayishi a amerika. sannan wannan maqiya Allah suna amfani da wannan fasaha wurin rubuta qur’ani amma suna jirkita wasu harrufa nashi…. Sannan kuma suna sake yin amfani da wannan fasaha wurin daukar muryar wani malami sananne ga al’ummah. Sannan sai suyi amfani dashi wurin kirkirar zantuka na karya su dangana da cewa shi ya fadesu, kaman yanda ya faru a indonesia Wanda a zahiri in aka bincika zaka samu ba haka bane… Duka wannan kadanne daga cikin hanyoyi da wa’innan maqiya musulunci sukebi wurin bata addininmu… Saboda haka ‘yan’uwa a kula sosai a sanya ido. Kuma a dage da karantar ilimi da ya jibanci han’yar sadarwa ta zamani… Wannan itace zata fishemu… Yaa Allah ka nuna mana gaskiya ka bamu daman binta, ka nuna mana karya ka bamu daman kauce mata….

4 responses to “Fadakarwa Zuwa Ga 'yan'uwa Musulmai”
 1. Falalu Ahmad Aliyu Shanono Avatar
  Falalu Ahmad Aliyu Shanono

  Allah ya tai maki addini musulunci da musulmai.

 2. patric idrees Avatar
  patric idrees

  yayi kyau malam

 3. mohammed dlakwaj Avatar

  Allah bada lada, ya kuma hada kan musulmai baki daya.

 4. mohammed dlakwaj Avatar

  Allah kara Ilimin fadakar da musulmai.

Leave a Reply

Latest updates
Categories