FATAWA KAN SALLAR IDI A RANAR JUMA'A(Dr Ibrahim Jalo Jalingo)

·

·

Domin neman ƙarin bayani danna nan

SALLAR IDI A RANAR JUMA’A:
Akwai hadithai kamar biyar cikin
wannan mas’ala ta haduwar idi da
juma’a, muna so ne mu kawo su
cikin wannan takaitaccen rubutu
namu saboda al’ummar Musulmi
su rika yin addininsu a bisa basira,
Mai shiriya ya shiriya a bisa hujjah,
shi ma mai bata ya mace amma
bayan shiriya ta zo masa. Allah ya
taimake mu, Ya ba mu ikon yin aiki
da sahihiyar Sunnah cikin dukkan
kome. Ameen.
(1) Imam Abu Dawud ya ruwaito
hadithi na 1,070 da Imam Ibnu
Majah hadithi na 1,326 da isnadin
da Imamul Albaanii ya inganta
daga Iyas Dan Abii Ramlah ya ce:-
(( ﺷﻬﺪﺕ ﻣﻌﺎﻭﻳﺔ ﺑﻦ ﺍﺑﻲ ﺳﻔﻴﺎﻥ ﻭﻫﻮ ﻳﺴﺎﻝ ﺯﻳﺪ ﺑﻦ
ﺃﺭﻗﻢ ﻗﺎﻝ: ﺃﺷﻬﺪﺕ ﻣﻊ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﻋﻴﺪﻳﻦ ﺍﺟﺘﻤﻌﺎ ﻓﻲ ﻳﻮﻡ؟ ﻗﺎﻝ: ﻧﻌﻢ. ﻗﺎﻝ: ﻓﻜﻴﻒ
ﺻﻨﻊ؟ ﻗﺎﻝ: ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻌﻴﺪ ﺛﻢ ﺭﺧﺺ ﻓﻲ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ،
ﻓﻘﺎﻝ: ﻣﻦ ﺷﺎﺀ ﺍﻥ ﻳﺼﻠﻲ، ﻓﻠﻴﺼﻞ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Na halarci Mu’awiyah
Dan Abii Sufyaan yana tambayar
Zaid Dan Arqam ya ce: Ko ka
halarci Idi biyun da suka hadu a
rana guda tare da Manzon Allah?
Sai ya ce: Na’am. Sai ya ce: to
yaya ya yi? Sai ya ce: Ya yi sallar
Idin sannan ya rangwanta yin
sallar juma’a, ya ce: Wanda ya so
yin sallar sai ya yi sallar)). Intaha.
(2) Imam Ibnu Majah ya ruwaito
hadithi na 1,329, sannan Imamul
Albaanii ya inganta shi, daga
Abdullahi Dan Umar ya ce:-
(( ﺍﺟﺘﻤﻊ ﻋﻴﺪﺍﻥ ﻋﻠﻰ ﻋﻬﺪ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ، ﻓﺼﻠﻰ ﺑﺎﻟﻨﺎﺱ ﺛﻢ ﻗﺎﻝ: ﻣﻦ ﺷﺎﺀ ﺍﻥ
ﻳﺄﺗﻲ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﻓﻠﻴﺄﺗﻬﺎ، ﻭﻣﻦ ﺷﺎﺀ ﺍﻥ ﻳﺘﺨﻠﻒ
ﻓﻠﻴﺘﺨﻠﻒ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Idi biyu sun hadu a
zamanin Manzon Allha mai tsira da
amincin Allah, sai ya yi wa mutane
salla sannan ya ce: Wanda ya so
tafiya juma’a to sai ya je ta, wanda
kuma ya so zaman gida to sai ya
zauna)). Intaha.
(3) Imam Abu Dawud ya ruwaito
hadithi na 1,073, da Imam Ibnu
Majah ya ruwaito hadith na 1,327,
kuma Imam Albaanii ya inganta
isnadin sahihin, daga Sahaabii
Abu Hurairah cewa:-
(( ﺍﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ: ﻗﺪ
ﺍﺟﺘﻤﻊ ﻓﻲ ﻳﻮﻣﻜﻢ ﻫﺬﺍ ﻋﻴﺪﺍﻥ، ﻓﻤﻦ ﺷﺎﺀ ﺃﺟﺰﺃﻩ ﻣﻦ
ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ، ﻭﺍﻧﺎ ﻣﺠﻤﻌﻮﻥ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Manzon Allah mai tsira
da amincin Allah ya ce: Hakika Idi
biyu sun hadu a wannan rana taku
wanda ya ga dama (hakan) ya isan
masa yin juma’a, amma lalle mu za
mu yi sallar Juma’a)). Intaha.
Wannan hadithi yana nuna mana
cewa: Su limaman juma’a
mustahabbi ne su je sallar juma’an
saboda masu bukatar yin sallar
juma’a su samu damar yin ta.
(4) Imam Abu Dawud ya ruwaito
hadithi na 1,071, sannan Imam
Albaanii ya inganta isnadinsa,
daga Ataa Dan Abi Rabah ya ce:-
(( ﺻﻠﻰ ﺑﻨﺎ ﺍﺑﻦ ﺍﻟﺰﺑﻴﺮ ﻓﻲ ﻋﻴﺪ ﻓﻲ ﻳﻮﻡ ﺟﻤﻌﺔ ﺍﻭﻝ
ﺍﻟﻨﻬﺎﺭ، ﺛﻢ ﺭﺣﻨﺎ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﻓﻠﻢ ﻳﺨﺮﺝ ﺇﻟﻴﻨﺎ، ﻓﻌﻠﻴﻨﺎ
ﻭﺣﺪﺍﻧﺎ، ﻭﻛﺎﻥ ﺍﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ ﺑﺎﻟﻄﺎﺋﻒ، ﻓﻠﻤﺎ ﻗﺪﻡ ﺫﻛﺮﻧﺎ
ﺫﻟﻚ ﻟﻪ، ﻓﻘﺎﻝ: ﺃﺻﺎﺏ ﺍﻟﺴﻨﺔ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Abdullahi Dan Zubair ya
yi mana salla cikin wani Idi a ranar
juma’a a farkon yini, sannan sai
muka tafi juma’a sai kuma (a
matsayinsa na liman) bai fito zuwa
gare mu ba, (saboda haka) sai
muka yi salla kowa shi kadansa. (a
lokacin) Ibnu Abbas yana Taa’if to
da ya dawo sai muka gaya masa
abin da ya faru, sai ya ce: (Abullahi
Dan Zubair) ya dace da Sunnah)).
Intaha.
Lalle wannan hadithin yana nuna
mana cewa: Limaman juma’a ma
ba dole ba ne su fita zuwa
masallatan juma’a a wannan ranar.
(5) Imam Abu Dawud ya ruwaito
hadithi na 1,072, kuma Imam
Albaanii ya inganta isnadinsa,
daga Ataa Dan Abii Rabah ya ce;-
(( ﺍﺟﺘﻤﻊ ﻳﻮﻡ ﺟﻤﻌﺔ ﻭﻳﻮﻡ ﻓﻄﺮ ﻋﻠﻰ ﻋﻬﺪ ﺍﺑﻦ
ﺍﻟﺰﺑﻴﺮ، ﻓﻘﺎﻝ: ﻋﻴﺪﺍﻥ ﺍﺟﺘﻤﻌﺎ ﻓﻲ ﻳﻮﻡ ﻭﺍﺣﺪ،
ﻓﺠﻤﻌﻬﻤﺎ ﺟﻤﻴﻌﺎ، ﻓﺼﻼﻫﻤﺎ ﺭﻛﻌﺘﻴﻦ ﺑﻜﺮﺓ ﻟﻢ ﻳﺰﺩ
ﻋﻠﻴﻬﻤﺎ ﺣﺘﻰ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻌﺼﺮ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Ranar juma’a da ranar
karamar salla sun hadu a zamanin
Ibnu Zubair, sai ya ce: Idi biyu sun
hadu a rana guda, sai ya hada su
gaba daya ya sallace su raka’a
biyu da safe, bai kara wata salla a
kan su ba har ya yi sallan La’asar))
. Intaha.
Shi kuwa wannan aiki na Sahabi
Abdullahi Dan Zubair yana nuna
mana cewa: Ba dole ba ne wanda
ya sallaci, sannan bai je sallar
juma’a ba, ba dole ba ne ba ne a
kan shi ya sallaci sallar Azahar ma,
a wannan ranar.
Muna rokon Allah Madaukakin
Sarki ya nuna mana gaskiya
gaskiya ce ya ba mu ikon bin ta, Ya
kuma nuna mana karya karya ce
ya ba mu ikon guje mata. Ameen.

6 responses to “FATAWA KAN SALLAR IDI A RANAR JUMA'A(Dr Ibrahim Jalo Jalingo)”
  1. aminu Avatar
    aminu

    DAGA. USTAZ YAKUQ MUHAMMAD JAMA`AREبسم الله الرحمن الرحيم
    DUK WANDA YANUNA YANA SON SHUGA BANCI AMUSULUNCI BAYA HALATTA ABASHI.
    ANNABI ( SAW) YACE : AMUSULUNCI DUK WANDA YANUNA YANA KWADAYIN SHUGABANCIKAR’ABASH , HAKA WANDA YAROKI ABASHI BA’ABASHI . BUKARI HADISI NA 7149
    ANNABI (SAW) YACEWA ABDURRAHMAN BN SUMRA KADA KANEMI ABAKA SHUGABANCI , IDAN KUMA KANEMA AKA BAKA, SAI ALLAH YABARKA DA SHUGABANCIN , BAZAI TAI MAKEKABA .
    AMMA DAZA’ABAKA BATARE DAKANEBA TO ALLAH SAI YA TAIMAKEKA AKAI . BUKARI HADISI NA 7147
    KUMA ANNABI (SAW) YACE : LALLAINE MUTANE ZASUNUNA KWADAYINSU AKAN SHUGABANCI, KUMAZATA ZAME MUSU NADAMA RANAR KIYAMA , LOKACIN DASUKA NEMA SUKA SAMU ZASUYITA FARINCIKI , DAGA MUTUWARSU KUMAZASU SHIGA UKU . BUKARI HADISI NA 7148
    SABODA WADANNAN HADISAI DAWADAN SUNSUMASU YAWA , LALLE BAYA HALATTA GA MUSULMI , YANUNA SHI YANASO ASHUGABANTAR DASHI AKAN AL’UMMA , WANDA KUMA YAFITO YANUNA YANASO ASHUGABANTARDAS HI BA’A SAURARONSA SAM SABODA IDAN YANEMA AKA BASHI, BA’ABINDA ZAI’IYA, SAIDAI YACUCI KANSA YACUCI AL’UMMA, DON HAKA MUNA FATA ALLAH YASTAREMU
    بسم الله الرحمن الرحيم
    DUK WANDA YANUNA YANA SON SHUGA BANCI AMUSULUNCI BAYA HALATTA ABASHI.
    ANNABI ( SAW) YACE : AMUSULUNCI DUK WANDA YANUNA YANA KWADAYIN SHUGABANCIKAR’ABASH , HAKA WANDA YAROKI ABASHI BA’ABASHI . BUKARI HADISI NA 7149
    ANNABI (SAW) YACEWA ABDURRAHMAN BN SUMRA KADA KANEMI ABAKA SHUGABANCI , IDAN KUMA KANEMA AKA BAKA, SAI ALLAH YABARKA DA SHUGABANCIN , BAZAI TAI MAKEKABA .
    AMMA DAZA’ABAKA BATARE DAKANEBA TO ALLAH SAI YA TAIMAKEKA AKAI . BUKARI HADISI NA 7147
    KUMA ANNABI (SAW) YACE : LALLAINE MUTANE ZASUNUNA KWADAYINSU AKAN SHUGABANCI, KUMAZATA ZAME MUSU NADAMA RANAR KIYAMA , LOKACIN DASUKA NEMA SUKA SAMU ZASUYITA FARINCIKI , DAGA MUTUWARSU KUMAZASU SHIGA UKU . BUKARI HADISI NA 7148
    SABODA WADANNAN HADISAI DAWADAN SUNSUMASU YAWA , LALLE BAYA HALATTA GA MUSULMI , YANUNA SHI YANASO ASHUGABANTAR DASHI AKAN AL’UMMA , WANDA KUMA YAFITO YANUNA YANASO ASHUGABANTARDAS HI BA’A SAURARONSA SAM SABODA IDAN YANEMA AKA BASHI, BA’ABINDA ZAI’IYA, SAIDAI YACUCI KANSA YACUCI AL’UMMA, DON HAKA MUNA FATA ALLAH YASTAREMU

  2. Umar M Assalafi Avatar
    Umar M Assalafi

    FATAWA KAN SALLAR IDI IDAN SUN HADU DA JUMA’A.

    1. Nibras Avatar

      Bari ayi gyara. Allah ya saka.

  3. Masha Allah. Duk hujjar da malam yabayar ta bangaren hadisan Manzon Allah s.a.w. Hujja ce mai karfi. Ta’ishemu ishara da cewa gaskiya itace gaskiya, bidiah kuma hanyace wacce mutum yazauna ya kirkireta. Saboda haka bin Allah da manzonsa shine mafita. Bissalam

  4. nawa Avatar

    barakallahu walaka

  5. nawa Avatar

    allah yabiya

Leave a Reply to aminuCancel reply

Latest updates
Categories