Hadin Kan Musulmai Akan Gaskiya

·

·

Assalaamu Alaikum warahmatullah A hakikanin gaskiya al’ummar musulmai a halin da ake ciki ana neman hadin kai aduk inda suke, domin baabu yadda za’ayi a samu cimma nasara ba tare da hadin kan al’ummah ba. Allah(s.w.t) ya fada acikin surah ta biyar ayah ta 103…
ﻭﭐﻋﺘﺼﻤﻮﺍ ﺑﺤﺒﻞ ﭐﻟﻠﻪ ﺟﻤﻴﻌﺎ ﻭﻟﺎ ﺗﻔﺮﻗﻮﺍ.
Allah yace: ‘kuyi riko da igiyar Allah baki. daya kada ku rarraba,.
Anan mecece igiyar Allah? Ya tabbata cikin hadisin da tumuzi ya rawaito. Manzon Allah(saw) yace: ‘Littaafin Allah itace igiyar da Allah ya ziro daga sama zuwa kasa’… Toh kaga anan da akace igiyar Allah ana nufin Qur’ani mai Girma. Dolene kan musulmai bazai taba haduwa ba dole sai sun sanya qur’ani mai girma ya zama alkalinsu, da zarar kunsaamu tsabaani a tsakaninku toh ba shiru zakuyi kowa ya rike nashi ba, A’a inhar kunason hadin kai mai inganci toh dole sai kun mayar da littaafin Allah ya zama shine alkalinku tare da hadi da hadisan manzon Allah(saw)… Allah yake cewa:
ﻓﺈﻥ ﺗﻨﺰﻋﺘﻢ ﻓﻰ ﺷﻰﺀ ﻓﺮﺩﻭﻩ
ﺇﻟﻰ ﭐﻟﻠﻪ ﻭﭐﻟﺮﺳﻮﻝ ﺇﻥ ﻛﻨﺘﻢ ﺗﺆﻣﻨﻮﻥ ﺑﭑﻟﻠﻪ ﻭﭐﻟﻴﻮﻡ
ﭐﻝﺀﺍﺧﺮ ﺫﻟﻚ ﺧﻴﺮ ﻭﺃﺣﺴﻦ ﺗﺄﻭﻳﻠﺎ.
In kuka saamu tsaabaani tsakaaninku toh ku maidashi zuwa ga Allah da manzonsa inhar kun kasance kunyi imani da Allah da manzonsa.. Ma’anan ku maidashi zuwa ga Allah da manzonsa shine ku maidashi zuwa ga Qur’aani da Hadisi. Toh kaga anan duk mai imani da Allah da ranan tashin qiyaama bazai taba cewa azo a hadu kawai. ba akan kitaab wa sunnah ba. Abin farin ciki ne ace musulmai su hade, amma ahade kan gaskiya hadewar da zata daure ta kuma kaimu ga tsira… Amma abinda nake ga ya dace ayi shine, kaman kasa irin nigeria ya daace ace musulmai su hade kai a karkashin kalmar la’ilaha illallah’ sannan inda aka rabu kuma ta fannin aqeedah sai kowa ya rike tashi ya cigaba da tallatata da hujjah, masu hankali sai su fahimta, baabu zagi ko cin mutunci. Bawai ayi shiru ba. A’a ayita bayaani wanda Allah ya nufeshi da ganewa sai ya gane. Wanda kuma daama Allah yayishi batacce ne kaga babu yadda za’a iya dashi… Dama akwai wanda Allah ya haliccesu kawai domin wuta. Kaman inda Allah ya bada labari acikin sura ta 7 ayah ta 179.
ﻭﻟﻘﺪ ﺫﺭﺃﻧﺎ ﻟﺠﻬﻨﻢ ﻛﺜﻴﺮﺍ ﻣﻦ ﭐﻟﺠﻦ ﻭﭐﻟﺈﻧﺲ ﻟﻬﻢ
ﻗﻠﻮﺏ ﻟﺎ ﻳﻔﻘﻬﻮﻥ ﺑﻬﺎ ﻭﻟﻬﻢ ﺃﻋﻴﻦ ﻟﺎ ﻳﺒﺼﺮﻭﻥ ﺑﻬﺎ
ﻭﻟﻬﻢ ﺀﺍﺫﺍﻥ ﻟﺎ ﻳﺴﻤﻌﻮﻥ ﺑﻬﺎ ﺃﻭﻟﺌﻚ ﻛﭑﻟﺄﻧﻌﻢ ﺑﻞ ﻫﻢ
ﺃﺿﻞ ﺃﻭﻟﺌﻚ ﻫﻢ ﭐﻟﻐﻔﻠﻮﻥ.
Allah yace: ‘hakika mun shuka wa jahannama da yawa daga cikin aljan da mutaane, suna da zuciya wanda baasu fahimta da’ita sannan sunada idanu wanda basu gani da’ita suna da kuma kunne wanda basuji da’ita, wa’innan sunanan kaman dabbobi, kaima sunfi dabbobi bata, kuma wa’innan sune rafkanannu’ toh kaaga irin wannan babu yadda mutum zai iya dasu na wurin ya gamsar dasu hakikanin musulunci…
*sannan kuma in muka koma cikin Qur’ani zamuga yadda Allah yayi ta mana gargadi na kada mu rarraba, ya tsawatar sosai. Kuma a hakikanin gaskiya abinda ya jawo karfinmu da kwarjininmu ya zube kenan. Rarrabuwa da mukayi.. Allah yace: a sura ta 8 ayah ta 46
ﻭﺃﻃﻴﻌﻮﺍ ﭐﻟﻠﻪ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪۥ ﻭﻟﺎ ﺗﻨﺰﻋﻮﺍ ﻓﺘﻔﺸﻠﻮﺍ
ﻭﺗﺬﻫﺐ ﺭﻳﺤﻜﻢ ﻭﭐﺻﺒﺮﻭﺍ ﺇﻥ ﭐﻟﻠﻪ ﻣﻊ ﭐﻟﺼﺒﺮﻳﻦ.
Kuyi wa Allah da manzonsa biyayyah, kada kuyi jayayya da juna,sai ku rarrabe,sai karfinku ya gushe, kuyi hakuri Allah yana tare da masu haquri. Ayoyi sunanan da yawa wanda sukayi ta bayaani akan hadin kan musulmai. Amma ayoyin duk basu maganan hadin kai bisa karya da son zuciya. Suna magana ne akan a hada kai bisa tafarkin gaskiya. Sannan kuma ‘yan’uwa kusani rarrabuwar musulmai, wannan wata kaddara ce da Allah ya kaddara dole sai ta rarrabu, kaman yadda annabi ya nuna a hadisi cikin sahih turmuzi li albani hadisi na 2129. Annabi yace: ‘hakika bani isara’ila sun rabu zuwa hanyoyi saba’in da daya,haka kuma al’ummah ta zata rabu zuwa kashi saba’in da uku. Duka suna wuta sai kashi daya. Sai aka tambayeshi waccece wannan kashi dayan? Sai yace ‘sune wanda suke kan abinda nake akai yau da sahabbaina’… Toh kaga anan dolene ya zamewa duk maison tsira da ya bincika ya ga shin waccece wannan kashi dayan da zasu tsira? Sai ya bisu. Kaga wannan hadisin tana zamewa duk wanda yace babu ruwanshi da aqeedah Qalubale.. sannan Allah domin ya fayyace mana komai a fili sai ya sake bayyana hanyarsa ta gaskiya a sura ta 6 ayah ta 153.
ﻭﺃﻥ ﻫﺬﺍ ﺻﺮﻃﻰ ﻣﺴﺘﻘﻴﻤﺎ ﻓﭑﺗﺒﻌﻮﻩ ﻭﻟﺎ ﺗﺘﺒﻌﻮﺍ
ﭐﻟﺴﺒﻞ ﻓﺘﻔﺮﻕ ﺑﻜﻢ ﻋﻦ ﺳﺒﻴﻠﻪۦ ﺫﻟﻜﻢ ﻭﺻﻯﻜﻢ ﺑﻪۦ
ﻟﻌﻠﻜﻢ ﺗﺘﻘﻮﻥ.
Wannan ityace hanyaata mikakkiya, kubishi kada kubi wasu kanaanan hanyoyi sai su raba ku da hanya ta.
Kaga duk wata hanya da zakabi ka kiraata da suna ko na meye in bata daace da wannan hanyar da Allah ya fada ba, toh hakika ta zamo daga cikin wa’innan kananun hanyoyin. Saboda haka ‘yan’uwa musulmai kuzo mu hade kan littaafin Allah da manzonsa. Mubar bid’ah da shirka. Mu koma mubi tafarkin magabaata, annabi da sahabbai… Domin Allah yace: a sura ta 4 ayah ta 115.
ﻭﻣﻦ ﻳﺸﺎﻗﻖ ﭐﻟﺮﺳﻮﻝ ﻣﻦ ﺑﻌﺪ ﻣﺎ ﺗﺒﻴﻦ ﻟﻪ ﭐﻟﻬﺪﻯ
ﻭﻳﺘﺒﻊ ﻏﻴﺮ ﺳﺒﻴﻞ ﭐﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﻧﻮﻟﻪۦ ﻣﺎ ﺗﻮﻟﻰ
ﻭﻧﺼﻠﻪۦ ﺟﻬﻨﻢ ﻭﺳﺎﺀﺕ ﻣﺼﻴﺮﺍ.
Allah(s.w.t) yace: ”Duk wanda ya tsabawa manzon Allah(s.a.w) bayan shiriya ta bayyana a gareshi ya kuma bi tafarkin da ba na muminai ba, zamu jibinta masa abinda ya jawo wa kansa, sannan mu shigar dashi jahannama, makoma tayi muni”
Toh anan ya dace mu kula… Shin da farko tafarkin annabi mukebi? Sannan irin imaninmu da irin ibadarmu ta dace da ta muminan farko? Domin babu yanda za’ayi imaninmu ta cika har sai munbi tafarkin muminan farko, wanda wannan kalman tana fara gaskata akan sahabban manzon Allah(s.a.w). Toh inkanaso ka gane aqeedah ta gaskiya, sai ka koma ka dubi aqeedar da muminan farko suke kai.. Itace aqeedah sahiha… Allah ya taimakemu yasa mudaace… Allah ka rabamu da ketare iyaaka. Ka nuna mana gaskiya ka bamu daman binta. Ka nuna mana karya ka bamu daman kaurace mata. Allah ka hada kan musulmai akan gaskiya… Wassalaatu wassalaamu Alaa Rasulillah.

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: