MATSALAR BOKO HARAM(Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi)

·

·

Assalamu Alaikum Ya Jama’ah.
Abin da ni ban yi imani da shi ba,
shine, ɓoye- ɓoye da rashin
bayyana gaskiya alhali kuwa yin
ha ka ya kan jawo rasa rayuka da
salwantar dukiyar mutane.
Allah Ya hana mu yin zalunci da
cutar da juna da jama’a. Manzon
Allah- tsira da amincin su tabbata
a gare shi yana cewa:
“ﺍﻟﻤﺴﻠﻢ ﻣﻦ ﺳﻠﻢ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻮﻥ ﻣﻦ ﻟﺴﺎﻧﻪ ﻭﻳﺪﻩ
ﻭﺍﻟﻤﻬﺎﺟﺮ ﻣﻦ ﻫﺠﺮ ﻣﺎ ﻧﻬﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ” ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ
“Mutun Musulmi shine wanda
musulmai suka tsira daga
harshensa da kuma hannunsa,
kuma mai hijira shi ne wanda ya yi
hijira daga abin da Allah ya hana
aikata shi”
Watau kome niyar mutum ta
neman alheri, ayyukansa ka da su
kai sa ga cutar da muslumi da
wanda bai ji ba bai gani ba. Shi
yasa Manzon Allah- tsira da
amincin su tabbata a gare shi ya
ce:
” ﺇﻥ ﺃﻋﻈﻢ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﻓﻰ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﺟﺮﻣﺎ ﻣﻦ
ﺳﺄﻝ ﻋﻦ ﺃﻣﺮ ﻟﻢ ﻳﺤﺮﻡ ﻓﺤﺮﻡ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻣﻦ ﺃﺟﻞ
ﻣﺴﺄﻟﺘﻪ ” ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺣﻤﺪ ﻭﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ
“Mafi girman mujurimin (watau
maɓannacin) musulmi a cikin
musulmai sh ine wanda ya yi
tambaya a kan wani alamari
wanda ba a haramta shi ba sai
daga baya aka haramta shi akan
mutane domin tambayar da yi”
Kun ga a nan, mutumin ya nemi
fatawa ce domin gyara addininsa,
amma da ya ke abu ne an bar
mutane ba hunkunci akansa, sai
domin tambayar wannan mutum
aka haramtashi a kan mutane, to
wannan ya zama mafi girman
mujurimi a cikin musulmi.
To ya ya halin wanda zai aikata
wani abin da zai kai ga a kama
musulmai a kasha su ko a ƙuntata
masu ko a kama su a tsare su ko
kuwa a lalata kasuwancin su da
tattalin arzikin su?
Kun ga ke nan babban mujurimi
ne ba bawan Allah ba ne, domin
ya aikata wani abu wanda
sakamakon sa zai kai ga a kashe
musulmi ko a kange musu ‘yancin
su da tsare hanyoyin su da
wulakanta su.
To a halin yanzu, mun gane cewa,
akwai wasu maƙiyan addinin Allah
da sukan ɓoye da sunnan boko
haram suna kai hari da farmaki da
yin ɓarna a cikin ƙasa domin ace
Musulmai ne kuma a ƙuntata
musu.
Amma tambaya nan shi ne:
1. Shin da gaske ne akwai a
tsakanin mu musulmai ‘yan Boko
Haram waɗanda sukan kai
wannan hari dudda ko cewa sun
sani cewa Musulmai ne za a
ƙuntatawa daga ƙarshe?
2. Yaya musulmi zasu fuskanci
wannan fitina?

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: