Nasiha Ga Masu Wa'azi(Dr Ibrahim Jalo Jalingo)

·

·

Alhafiz Ibnu Rajab wanda ya mutu
a shekarar hijira ta 795 watau yau
shekaru 630 ke nan da suka wuce,
ya yi wa malamai wata maga da ya
kamata a rubuta ta da ruwan zinari,
ya ce cikin littafinsa mai suna
Alhikamul Jadiratu Bil Iza’ah shafi
na 12:-
(( ﻓﺎﻟﻮﺍﺟﺐ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﻣﻦ ﺑﻠﻐﻪ ﺍﻣﺮ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﻋﺮﻓﻪ ﺍﻥ ﻳﺒﻴﻨﻪ ﻟﻼﻣﺔ ﻭﻳﻨﺼﺢ ﻟﻬﻢ
ﻭﻳﺄﻣﺮﻫﻢ ﺑﺎﺗﺒﺎﻉ ﺃﻣﺮﻩ ﻭﺍﻥ ﺧﺎﻟﻒ ﺫﻟﻚ ﺭﺃﻱ ﻋﻈﻴﻢ
ﻣﻦ ﺍﻻﻣﺔ؛ ﻓﺎﻥ ﺍﻣﺮ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﺍﺣﻖ ﺍﻥ ﻳﻌﻈﻢ ﻭﻳﻘﺘﺪﻯ ﺑﻪ ﻣﻦ ﺭﺃﻱ ﺍﻱ ﻣﻌﻈﻢ
ﻗﺪ ﺧﺎﻟﻒ ﺃﻣﺮﻩ ﻓﻲ ﺑﻌﺾ ﺍﻻﺷﻴﺎﺀ ﺧﻄﺎ، ﻭﻣﻦ ﻫﻨﺎ
ﺭﺩ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﻭﻣﻦ ﺑﻌﺪﻫﻢ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﻣﺨﺎﻟﻒ ﺳﻨﺔ
ﺻﺤﻴﺤﺔ، ﻭﺭﺑﻤﺎ ﺍﻏﻠﻈﻮﺍ ﻓﻲ ﺍﻟﺮﺩ ﻻ ﺑﻐﻀﺎ ﻟﻪ، ﺑﻞ
ﻫﻮ ﻣﺤﺒﻮﺏ ﻋﻨﺪﻫﻢ ﻣﻌﻈﻢ ﻓﻲ ﻧﻔﻮﺳﻬﻢ، ﻭﻟﻜﻦ
ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﺣﺐ ﺍﻟﻴﻬﻢ ﻭﺃﻣﺮﻩ ﻓﻮﻕ ﺍﻣﺮ ﻛﻞ
ﻣﺨﻠﻮﻕ، ﻓﺈﺫﺍ ﺗﻌﺎﺭﺽ ﺍﻣﺮ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﻭﺃﻣﺮ ﻏﻴﺮﻩ
ﻓﺄﻣﺮ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﺍﻭﻟﻰ ﺍﻥ ﻳﻘﺪﻡ ﻭﻳﺘﺒﻊ ﻭﻻ ﻳﻤﻨﻊ ﻣﻦ
ﺫﻟﻚ ﺗﻌﻈﻴﻢ ﻣﻦ ﺧﺎﻟﻒ ﺃﻣﺮﻩ ﻭﺍﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﻐﻔﻮﺭﺍ ﻟﻪ،
ﺑﻞ ﺫﻟﻚ ﺍﻟﻤﺨﺎﻟﻒ ﺍﻟﻤﻐﻔﻮﺭ ﻟﻪ ﻻ ﻳﻜﺮﻩ ﺍﻥ ﻳﺨﺎﻟﻒ
ﺃﻣﺮﻩ ﺍﺫﺍ ﻇﻬﺮ ﺍﻣﺮ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﺑﺨﻼﻓﻪ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((wajibi ne a kan dukkan
wanda umurnin Manzon Allah mai
tsira da amincin Allah ya isa zuwa
gare shi, ya kuma san shi, ya
bayyana shi ga Al’ummah, ya
musu nasiha, ya umurce su da bin
umurninsa koda kuwa hakan ya
saba wa ra’ayin wani babba a cikin
Al’ummah, saboda umurnin
Manzon Allah mai tsira da amincin
Allah shi ya fi cancantar a girmama
shi, kuma a yi koyi da shi a kan
ra’ayin dukkan wani wanda ake
girmamawa amma kuma
umurninsa ya saba wa umurnin shi
cikin sashin lamura cikin kure,
wannan shi ya sa ma Sahabbai da
wadanda suka biyo bayansu suka
yi wa dukkan wanda ya saba wa
Sahihiyar Sunnah raddi, wani
lokaci ma raddi mai kaushi, ba wai
kuma saboda suna nuna kiyayya
ba ce gare shi, a’a yana nan abin
so a gare su kuma abin
girmamawa a cikin rayukansu, to
amma Manzon Allah shi ne mafi
soyuwa a gare su, sannan
umurninsa shi yake sama da
umurnin ko wace halitta. Saboda
haka idan umurnin Manzon Allah
ya yi karo da umurnin waninsa, to
umurnin Manzon Allah shi ya fi
cancantar a gabatar kuma a bi,
wannan kuwa ba zai hana a
girmama mutumin da ya saba wa
umurnin Manzon Allah ba matukar
dai ana gafarta wa kuren cikin
Sahari’ah, kuma shi wannan da ya
yi sabon cikin kure ba zai nuna
kyamar a saba wa umurninsa
matukar dai umurnin Manzon Allah
mai tsira da amincin Allah ya
bayyana a matsayin mai saba
masa)). Intaha.
Sannan shi ma Shehu Uthmanu
Dan Fodiyo ya yi wata magana mai
kyawun gaske wacce za ta
amfanar da masu wa’azi a cikin
littafin Ihya’us Sunnah shafi na 8:-
(( ﻗﺪ ﺍﻧﻌﻘﺪ ﺍﻹﺟﻤﺎﻉ ﻋﻠﻰ ﺍﻥ ﺁﺭﺍﺀ ﺍﻟﻤﺠﺘﻬﺪﻳﻦ ﻛﻠﻬﺎ
ﻣﺴﺎﻟﻚ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺠﻨﺔ ﻭﻃﺮﻕ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺨﻴﺮﺍﺕ ﻓﻤﻦ ﺳﻠﻚ
ﻣﻨﻬﺎ ﻃﺮﻳﻘﺎ ﻭﺻﻠﻪ ﺍﻟﻰ ﻣﺎ ﻭﺻﻠﻮﺍ ﺍﻟﻴﻪ ﺣﻘﺎ ﻭﻣﻦ
ﻋﺪﻝ ﻋﻨﻪ ﻗﻴﻞ ﻟﻪ ﺳﺤﻘﺎ! ﻭﻳﺠﻮﺯ ﺗﻘﻠﻴﺪﻫﻢ ﻓﻲ ﻛﻞ
ﺭﺃﻱ ﺍﻻ ﻣﺎ ﺧﺎﻟﻒ ﻧﺺ ﺍﻟﻘﺮﺍﻥ ﺍﻭ ﻧﺺ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﺍﻭ
ﺍﻟﻘﻮﺍﻋﺪ ﺍﻭ ﺍﻟﻘﻴﺎﺱ ﺍﻟﺠﻠﻲ، ﻓﺎﻓﻬﻢ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Ijma’i ya kullu a kan
cewa: dukkan ra’ayoyin Mujtahidai
mashiga ce ta zuwa Aljanna, kuma
hanyoyi ne na alkhairai, wanda duk
ya bi wata hanya cikinsu tabbas za
ta kai shi inda suka kai, wanda
kuma ya baude ga barin su sai a
ce da shi tir. Sannan yana halatta a
yi koyi da su cikin ko wane ra’ayi,
amma banda abin da ra’ayin da ya
saba wa nassin Alkur’ani, ko
nassin Hadithi, ko saba wa
Ka’idodi, da Ijma’i, ko Kiyasi Jaliyyi,
ka fahimta)). Intaha.
Dukkan abin da mutum ya san
cewa: Annabi mai tsira da amincin
Allah ya yi umurni da yin sa, to
wajibi ne ya bayyanar da shi ga
Al’ummah, da kuma za a samu
wani mai son zuciya da zai yi
kokarin hana shi yin hakan to ba
zai saurara masa ba, wannan shi
ne daidai kuma shi ne hanyar
Annabi da sauran Maluman
Sunnah kamar su Babban masani
a ilmin Hadithi Ibnu Rajab.
Haka nan haramun ne a kan
kowane Musulmi ya bi ijtihadin
wani malami komin girmansa
matukar dai ijtihadin ya saba wa
nassin Alkur’ani, ko nassin Hadithi,
ko nassin Ijma’i, ko Kiyasi Jaliyyi,
kamar dai yadda Shehu Dan
Fodiyo ya bayyana mana a yanzu.
Hakika, mun sani sau da dama
karkatattu -mazansu da matansu,
ubanninsu da ‘ya’yansu,
malumansu da jahilansu- cikin ko
wane zamani suna amfani da
lafazin “wane na raba kan
Al’umma” ko “Wane ba ya son
hadin kan Al’umma” saboda
neman rufe wata barna da Sari’ar
Musulunci ta ce a bayyana ta, ko
saboda kare wata barna da Sari’ah
ta ce yake ta, to amma irin wannan
jinsi na mutane ba za a saurare su
ba saboda dillacin Duniya ne yake
gabansu. Lalle rashin sauraron
wadannan ‘yan hayaniya, shi ne
hanyar Annabi mai tsira da aminci
Allah, kuma shi ne hanyar
Kungiyar Izala tun lokacin
kafuwarta.
Alhafizu Ibnu Katheer ya ce cikin
littafinsa Albidayatu wannihayah
3/55-56:-
(( ﻋﻦ ﺳﻌﻴﺪ ﺑﻦ ﺟﺒﻴﺮ ﻭﻋﻜﺮﻣﺔ ﻋﻦ ﺍﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ
ﻗﺎﻝ: ﺍﺟﺘﻤﻊ ﻋﻠﻴﺔ ﻣﻦ ﺍﺷﺮﺍﻑ ﻗﺮﻳﺶ ﻭﻋﺪﺩ
ﺃﺳﻤﺎﺀﻫﻢ ﺑﻌﺪ ﻏﺮﻭﺏ ﺍﻟﺸﻤﺲ ﻋﻨﺪ ﻇﻬﺮ ﺍﻟﻜﻌﺒﺔ،
ﻓﻘﺎﻝ ﺑﻌﻀﻬﻢ ﻟﺒﻌﺾ: ﺍﺑﻌﺜﻮﺍ ﺍﻟﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﻓﻜﻠﻤﻮﻩ،
ﻭﺧﺎﺻﻤﻮﻩ ﺣﺘﻰ ﺗﻌﺬﺭﻭﺍ ﻓﻴﻪ، ﻓﺒﻌﺜﻮﺍ ﺍﻟﻴﻪ ﺍﻥ
ﺍﺷﺮﺍﻑ ﻗﻮﻣﻚ ﻗﺪ ﺍﺟﺘﻤﻌﻮﺍ ﻟﻚ ﻟﻴﻜﻠﻤﻮﻙ، ﻓﺠﺎﺀﻫﻢ
ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺳﺮﻳﻌﺎ، ﻭﻫﻮ
ﻳﻈﻦ ﺍﻧﻪ ﻗﺪ ﺑﺪﺍ ﻟﻬﻢ ﻓﻲ ﺃﻣﺮﻩ ﺑﺪﺀ، ﻭﻛﺎﻥ ﺣﺮﻳﺼﺎ
ﻳﺤﺐ ﺭﺷﺪﻫﻢ ﻭﻳﻌﺰ ﻋﻠﻴﻪ ﻋﻨﺘﻬﻢ، ﺣﺘﻰ ﺟﻠﺲ ﺍﻟﻴﻬﻢ.
ﻓﻘﺎﻟﻮﺍ: ﻳﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﺍﻧﺎ ﻗﺪ ﺑﻌﺜﻨﺎ ﺇﻟﻴﻚ ﻟﻨﻌﺬﺭ ﻓﻴﻚ، ﻭﺍﻧﺎ
ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻻ ﻧﻌﻠﻢ ﺭﺟﻼ ﻣﻦ ﺍﻟﻌﺮﺏ ﺍﺩﺧﻞ ﻋﻠﻰ ﻗﻮﻣﻪ ﻣﺎ
ﺃﺩﺧﻠﺖ ﻋﻠﻰ ﻗﻮﻣﻚ؛ ﻟﻘﺪ ﺷﺘﻤﺖ ﺍﻵﺑﺎﺀ ﻭﻋﺒﺖ ﺍﻟﺪﻳﻦ،
ﻭﺳﻔﻬﺖ ﺍﻵﻟﻬﺔ ﻭﻓﺮﻗﺖ ﺍﻟﺠﻤﺎﻋﺔ، ﻭﻣﺎ ﺑﻘﻲ ﻣﻦ
ﻗﺒﻴﺢ ﺍﻻ ﻭﻗﺪ ﺟﺌﺘﻪ ﻓﻴﻤﺎ ﺑﻴﻨﻨﺎ ﻭﺑﻴﻨﻚ ..)).
Ma’ana: ((Daga Sa’id Da Jubair da
Ikrimah, daga Dan Abbas ya ce:
Shugabannin Quraishawa sun
hadu a Dakin Ka’abah, sannan
suka aika wa Annabi mai tsira da
amincin Allah cewa suna bukatar
zama da shi, nan-da-nan Annabi
mai tsira da amincin Allah ya je ya
same su saboda tsammanin da
yake yi na cewa za su musulunta
ne, domin shi har kullum yana son
musu alheri ne kuma ba ya son
abin da zai wahalce su. Da ya zo
ya zauna a inda suke sai suka ce
da shi: Ya Muhammad! Lalle, mun
aika Maka ne domin mu yanke
uzurinmu gare ka, wallahi mu ba
mu taba ganin wani mutum daga
cikin Larabawa da ya kawo musiba
cikin jama’arsa ba kamar yadda ka
kawo musiba cikin jama’arka ba.
Hakika ka zagi iyayenmu, kuma ka
aibanta addininmu, sannan ka
maida masu hankalinmu wawaye,
ka kuma zagi allolinmu, ka raba
kawunan jama’armu. Babu dai
wani mummunan da ya rage
wanda ba ka sanya shi tsakaninmu
ba..)). Intaha.
Ku dubi wadannan mujrumai! Wai
daga cikin laifukan da suke zargin
Manzon Allah mai tsira da amincin
Allah na yi shi ne: raba kawunan
jama’a! saboda kawai ya ce: A bi
Addinin gaskiya, kada a karbi
umurnin kowa matukar ya saba wa
umurnin Allah Madaukakin Sarki,
da ManzonSa mai tsira da aminci.
Wannan ita ce al’adar karkatattu,
sawa’un mushrukai ne su masu
bautan gumaka, ko kuwa kafurai
ne ma’abuta littafin, ko kuwa fasikai
ne da ‘yan bidi’ah cikin Al’ummar
Musulmi. Wannan shi ya sa a
shekarun farko na kafuwar
Kungiyar Izala babban abin da ‘yan
bidi’ah da ma’abuta maslahar kai
suke tuhumar masu wa’azi a
cikinta da shi, shi ne: Su masu
raba kawunan al’umma ne, masu
bata tafiyar Al’ummar Musulmi ne,
ba sa yin magana a kan abin da
aka yi ittifaki a kan sa sun koma
suna magana a kan sabanin
fahimta, maimakon su shiga daji su
musuluntar da maguzawa sai ga
shi sun koma suna cewa wai
Darikah ba ta da kyau, wai Shi’ah
ba Musulunci ba be, wani abin
dariya ma wai taron suna bidi’a ce!
wai addu’a bayan salla cikin jam’i
bidi’a ce, kai lalle wadannan
mutane sun cika fitina tir da
halayensu, kuma dole ne a hadu a
yake su domin Musulmi su huta da
musibarsu.
‘yan’uwa masu kaunar Sunnah!
Wannan shi ne abin da yake
faruwa har kullum tsakanin masu
neman a kudurta gaskiya, a kuma
fadi gaskiya, sannan a yi aiki da
gaskiya cikin dukkan kome. Ina
fata ba ku manta da jigon
makaalarmu ba, watau ta’ammulin
maganar babban Malami Alhafiz
Ibnu Rajab ba, da kuma babban
Malami Uthmanu Dan Fodiyo ba.
Allah Ka ba mu karfin aiki da
gaskiya komin dacinta. Ameen.

8 responses to “Nasiha Ga Masu Wa'azi(Dr Ibrahim Jalo Jalingo)”
 1. Ibrahim Musa Faskari Avatar
  Ibrahim Musa Faskari

  Juziyta khairan

 2. Adam abualamin Avatar
  Adam abualamin

  Allah yasaka da alheri allah yasa malaman sunji.

 3. Hafiz maiakwai Avatar

  To malam Allah ya biyaka ya saka da alheri.Kuma Allah ya sa mu kara samun maluma kamar ka da zasu rika sanar da mutane da karantar da su.

 4. sulaiman yusuf Avatar

  Dr. Allah S.W.T. yasaka da alheri, kuma ya hada kayukan ahlus sunna akan gaskiya amin.

 5. Amin malam, Allah saka da alkhairi. Ya kuma ganar da wanda basu son gaskiya amin.

 6. Sakinat Avatar

  Slm Malam Allah yasakada alkhairi,mukam da irinku a’alumma munjidadi. Allah kabamu ikon bin gaskiya ameeen.

 7. Abbas kawuba Kwairanga Avatar
  Abbas kawuba Kwairanga

  Allah Humma Ameen< Ya Ash-Sheik May Allah bless you and family…

 8. MUSA JIBRIN Avatar
  MUSA JIBRIN

  Malamin sunnah daban da malamin bid’ah, malam jalo ALLAH yasaka da alheri

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: