Nasiha Zuwa Ga 'Yan'uwa Musulmai 'yan Izalah

·

·

Nasiha Zuwa Ga ‘yan’uwa Musulmai ‘yan Izala…….
Bismillahirrahmaanirraheem!!!
A hakikanin Gaskiya Sake Hadewar kungiyar ‘jama’atu izalatil bid’ah wa’ikamatussunnah’ wuri daya abin farin ciki ne ga duk al’ummar musulmai na duniya, ba ahlussunnah kawai ba. A’a har da ma wanda basu ba. Domin Duk wanda kaji yana bakin ciki ko yana kushe hadewar to munafuki ne, ko ya sani ko bai sani ba. Hakikah Qungiyar ‘izala’ tayi da’awa a kasannan, wanda kuma da taimakon Allah ta cimma wurare da yawa. a daa kasannan tana cikin duhun jahilci na bid’oi da aka kirkira aka cusa cikin addini, da shirka da ta mamaye kasaa. Allah ya taimakemu da wannan Qungiya mai albarka wanda ‘yan’uwa musulmai Ahlussunnah suka kafa domin amsa kiran Allah da yayi acikin suratu Al’emran ayah ta 104 inda Allah yake cewa:
ﻭﻟﺘﻜﻦ ﻣﻨﻜﻢ ﺃﻣﺔ ﻳﺪﻋﻮﻥ ﺇﻟﻰ ﭐﻟﺨﻴﺮ ﻭﻳﺄﻣﺮﻭﻥ
ﺑﭑﻟﻤﻌﺮﻭﻑ ﻭﻳﻨﻬﻮﻥ ﻋﻦ ﭐﻟﻤﻨﻜﺮ ﻭﺃﻭﻟﺌﻚ ﻫﻢ
ﭐﻟﻤﻔﻠﺤﻮﻥ.
‘A samu wasu al’ummah cikinku, suna kira zuwa ga alkhairi, suna umarni da kyakkyawan aiki, suna hani da mummuna, wa’innan sune masu rabauta…
A hakikanin Gaskiya ina kira ne ga jagorori da kuma mabiya su gane, wannan hadewa da kungiyar izala tayi abu ne mai matukar mahimmanci a garemu baki daya. Domin Allah yake cewa cikin suratu al’emran ayah ta 103:
ﻭﭐﻋﺘﺼﻤﻮﺍ ﺑﺤﺒﻞ ﭐﻟﻠﻪ ﺟﻤﻴﻌﺎ ﻭﻟﺎ ﺗﻔﺮﻗﻮﺍ
ﻭﭐﺫﻛﺮﻭﺍ ﻧﻌﻤﺖ ﭐﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﺇﺫ ﻛﻨﺘﻢ ﺃﻋﺪﺍﺀ ﻓﺄﻟﻒ
ﺑﻴﻦ ﻗﻠﻮﺑﻜﻢ ﻓﺄﺻﺒﺤﺘﻢ ﺑﻨﻌﻤﺘﻪۦ ﺇﺧﻮﻧﺎ ﻭﻛﻨﺘﻢ ﻋﻠﻰ
ﺷﻔﺎ ﺣﻔﺮﺓ ﻣﻦ ﭐﻟﻨﺎﺭ ﻓﺄﻧﻘﺬﻛﻢ ﻣﻨﻬﺎ ﻛﺬﻟﻚ ﻳﺒﻴﻦ ﭐﻟﻠﻪ
ﻟﻜﻢ ﺀﺍﻳﺘﻪۦ ﻟﻌﻠﻜﻢ ﺗﻬﺘﺪﻭﻥ.
‘Kuyi riko da igiyar Allah baki daya kada ku rarraba, ku tuna ni’imar Allah a kanku lokacin da kuke abokan gaba, sai ya hade zukatanku, kuka wayi gari da ni’imar Allah kuna ‘yan’uwa. Wanda ada kuna kan gaba ta wuta sai ya tsamar daku daga cikinta, da haka ne Allah yake bayyana muku ayoyinsa domin ku shiryu’ wannan yana daga cikin mu’ujiza ta qur’ani. Dubi Ayar kaman an saukar da’ita kan ‘yan izala.
Toh ni abinda na lura shine acikin wannan Qungiya ta izala akwai wanda suke da tsarkakakkar zuciya wanda su burinsu a hadu ayiwa addinin Allah aiki, kuma akwai wasu wanda su kawai neman sunaa suke, akwai wasu kuma wanda abin duniya ce kawai ta damesu…
Wannan tsarin haka take gudana tsakaanin ko wata al’ummah dama. A hakikanin gaskiya al’ummah bata haduwa ta gaskiya, har sai ansamu hadewa cikin aqeedah, da sauran usulai na ibadah, saboda haka nake ganin wani irin tsari da naga wasu suke kira da azo a tafi akai ba tsari bace wanda zata daure, cewa: ‘a hadu amma kowa ya cigaba da tsarin da yake bi’ wannan a hakikanin gaskiya ba tsari bace wanda zata daure, aima zai zama abin kunya da zargi inhar wanda ke tuhumar wani don yayi kabdu, ko sadlu. Ko kuma wanda ke zargin wani dun yayi ruqiyyah da cewar yayi aikin bori. Ko kuma wanda ke tuhumar wani dun yayi sallama daya a sallah, a ganshi kuma yanzu yazo yana cewa babu laifi ayi duka. Kaga dole a zargeshi kuma a tuhumeshi da ya kawo hujjah. Dama tuncan meyasa ka tuhumi maiyi? Son zuciyace ko rashin gaskiya?kaga dole yayi bayaani. dacewa yayi tunda sunnah akebi ayi adalci wa juna, wannan addini mukeyi ba jam’iyyar siyasa ba. komai ya dace mubishi kan tsari. Malamai kowa ya kawo fatawarsa da ya dogara da’ita sai a hade a fitar da wanda yafi tafiya kan tsari… Amma misali cewa. Mai kabdu ko sadlu a sallah kowa yaci gaba da tashi, ko mai yin ruqiyyah da wanda yace hakan bori ne kowa yacigaba da tashi, wannan ba tsari bace wanda zata kaimu ga gaci. Zahiri maslan wanda yayi kabdu ko sadlu a sallah sallarsa tayi, toh amma wanne yafi acikin shi sadlu da kabdun? Akwai wanda yafi acikinsu, kaga sai malamai su hadu sufitar da wanda yafi suyi bayaani mai gamsarwa wanda mabiya zasu gamsu dashi. Sannan irin mas’aloli na ladanci, da sallama daya da biyu duk ya dace malamai su zauna su fitar da tsari daya wanda yafi hujjah sai mutafi akai. Wannan itace hakikanin gaskiya, a cire son zuciya da son mulki ayi wa addinin Allah aiki, da haka zamu samu tsira. Na sani da wuya in ba Allah ya sanya ka cikin mai rabo ba, ka gina jama’arka kan wata fatawa sannan daga baya kazo ka rusheta saboda ka gano hakikanin gaskiya wannan fatawar akwai kure ciki, wannan ita ta kashe malaman bid’ah. amma a hakikanin gaskiya inkayi hakuri ka daure ka fita kayi bayaani, sai kaga Allah yaa dada daukaka ka, kaaga kuma ka tsira. Domin ka gwammaci kunyar duniya data qiyaama. Sannan akwai wasu malamai da ‘yan’uwa dalibai da mabiya wanda suna da kyakkyawar nufi ga wannan kungiyar, amma da yawa daga cikin wasu mabiya ko dalibai, ko malamai. suna kushesu domin suna ganin su basuson hadewanne. Bazan baku misali ku fahimta, duk wani malami da kuka ga ya jajirce wurin yin bayaani na tsabaanin aqeedah da fatwa dake tsakanin ‘yan kungiyar izala, toh a hakikanin gaskiya yana son ‘yan izala da alheri ne, amma duk wanda zaice a tafi kawai kowa ya rike tashi fahimtar,toh a hakikanin gaskiya bai fahimci addini ba, ko kuma dama yana da wata buri tashi ta karan kansa. Tambaya anan in aka bincika acikin wa’azuzzuka wanda akayi bayan rabuwar wannan kungiya, zaka samu akwai wanda wannan bangaren tana tuhumar dayan, saboda wasu mas’aloli kaman wanda na zayyana a baya.irinsu yin ruqiyyah, sallama daya da biyu, fifita mazhaba kan nassi inghatacce, kabdu da sadlu, da dai sauran mas’aloli masu yawa. Toh yanzu a tunaninku bazaku zama abin zargi ba inkuka amince da cewa kowa ya rike tashi a tafi? Shin daa zargin da kuke wa juna ta son zuciya ce? Kaga dole a amsa wannan tambayar. Toh meyasa muka raba kafa da ‘yan bida’ah? Inhar kowa ya rike fahimtarsa ne ai sai mu sake hadewa da ‘yan bid’ah suma su rike tasu fahimta muma mu rike tamu… Saboda haka ‘yan’uwa kan al’ummah bata haduwa dole sai an hadu karkashin littafi daya, karkashin Shugabanci daya. Da hakane ake samun kan al’ummah ya hadu.. Sannan kuma ba haka ne ke nuna. Baza’a samu tsabani a tsakani ba. A’a za’a iya samu toh amma Allah ya bamu hanyar da zamu warware tsabani dake tsakaaninmu inada yake cewa cikin suratu nisa’I ayah ta 59
ﻓﺈﻥ ﺗﻨﺰﻋﺘﻢ ﻓﻰ ﺷﻰﺀ ﻓﺮﺩﻭﻩ
ﺇﻟﻰ ﭐﻟﻠﻪ ﻭﭐﻟﺮﺳﻮﻝ ﺇﻥ ﻛﻨﺘﻢ ﺗﺆﻣﻨﻮﻥ ﺑﭑﻟﻠﻪ ﻭﭐﻟﻴﻮﻡ
ﭐﻝﺀﺍﺧﺮ ﺫﻟﻚ ﺧﻴﺮ ﻭﺃﺣﺴﻦ ﺗﺄﻭﻳﻠﺎ.
‘In kuka samu tsabaani tsakaninku toh kumaidashi zuwa ga Allah da manzonsa, in kun Kasance masu imani da Allah da ranan tashin qiyaama ‘ ma’ana ku maidashi zuwa ga Allah (qur’ani) manzon Allah (hadisi). Toh kaga wannan ka’idar ya kamata mubi in mun kasance munyi imani da Allah. Ba wai ace kowa ya riqe nashi ba. A’a me Allah da annabi sukace? Wannan itace ka’idah ta ahlussunnah wal jama’a… Babu biyayyah ga wanda bai bin umarnin Allah. Ya kamata muzama wayayyu musamman matasa, babu wani malami da zai kare ka a gaban Allah. Saboda haka bai dace ba wani malami ya bada fatwa da ta tsaba wa shari’ah ka karba kayi amfani dashi. Inkayi haka yazama ka zama mushriki. Ya zama kana bautan daagut. Mu zama masu amfani da kwakwalwarmu, duk wata fatwa da za’a kawo muzamto cewa muna da masaniyar cewa bata tsabawa shari’ah ba kafin mu bita. Wannan itace zata kaimu ga gaci. Allah yasa mudaace. Allah ka dada daukaka addinin musulunci da musulmai, ka ruguza kafirci da kafirai wassalaam.

9 responses to “Nasiha Zuwa Ga 'Yan'uwa Musulmai 'yan Izalah”
 1. Yakubu Dan'asabe Avatar

  Allah ya tabbatar damu akan sunnar manzo(saw)

 2. Auwal Abu Aisha Avatar
  Auwal Abu Aisha

  Malam Nibras Allah ya saka da alheri.Muna saurarenka

 3. Yakub m sani Avatar

  Allah ya saka da alkairi idan za,asamu mutane irinka wallahi da duk baza,a samu kace nace ba.

 4. USMAN SALEH Avatar
  USMAN SALEH

  ALLAH YA SAKA DA ALHERI, DUK MASU KOKARIN SUGA SUN KASSARA TAFIYAR HADIN KAN NAN ALLAH YA MANA MAGANINSU. ALLAH KARA HAD

 5. shehu m kunu Avatar
  shehu m kunu

  Annabi kabalu yayi ko sadalu

 6. Abdullahi usman kuta {ABDUL SUNNIH} Avatar
  Abdullahi usman kuta {ABDUL SUNNIH}

  Allah ya saka da alhairi. Allah kara hadin kan ahlu sunnah a nigeria. Wanda ke fatan rabuwar kungiyar Allah yi maganinsa

 7. usman saleh Avatar
  usman saleh

  Malaman sunnah ku dunkule wuri guda, Allah yai jagora…

 8. Abubakartilde Avatar
  Abubakartilde

  Allah yasa mu dace

 9. Ibrahim Abuga Avatar
  Ibrahim Abuga

  Malam Nibras ka yi kokari, kuma akwai alamar kana son bin inda gaskiya take, amma yana da kyau mu san cewa mas’aloli na furu’a mas’aloli ne wanda ba a taba zama a saman fahimta guda, ko kana iya kawo mini mutum guda wanda fahimtar sa take dai-dai da kowa a kan mas’alar furu’a tun zamanin Sahabbai har izuwa wannan lokaci na mu? na san ba kai dai ba babu mai iya kawo wannan,to, kaga ko ya saba ma hankali ace dukkanin su cikin bata suke don rashin kasancewar su akan abu guda.kuma yana da kyau mu sani cewa ko da Hadisi ya inganta ba shi ke nuna yin aiki da shi ba kai tsaye sai an gitta shi a saman ka’idodin da malumman sunnah suka kafa watau usulul fiqhi sannan za’a gane ma’anar Hadisin da kuma yin aiki da shi ko akasin haka, ga misalai; ana iya samun hadisi ingantacce amma kuma wani hadisi ya shafe shi, ana iya samun illar da ya sa Annabi ya aikata abu, to, kaga idan babu wannan illar ai kaga ba za’a yi aiki da wannan Hadisi ba, yana yiwuwa a samu Hadisi wanda isnadinsa ingantacce ne amma matanin ba ingantacce ba, ko dai saboda maganar an juya ta abinda malammai ke kira ‘Qalbi’ ko kuma yadda aka gina larabcin babu fasaha acikin sa, to kaga ko ba ya yiwuwa a ce Annabi ya fadi magana mara fasaha, ko abinda ya ke ya yi kama da wadannan.Haka kuma ana iya samun ingantaccen ‘Nassi Aahad’ ya saba ma Nassi Mutawaturi ko wata Aya ta Alqur’ani, kaga ko ba ya yiwuwa ayi anfani da wancan Nassi duk da ingancin sh a bar wadannan Nassosa Mutawaturai, wani lokaci ana iya samun Nassi ingantacce amma sahabin da ya ruwaito Hadisin karshen Hadisin ne ya ji bai ji farko ba wanda farko shi ke nuna ba yadda karshen ke nufi ake nufi ba. da dai sauran su. To, kaga duk wadannan su ke sa wanda ba shi da cikakken sani ya ke ganin cewa maluma suna saba ma ingantaccen Hadisi to, kaga ba haka abun ya ke ba. don haka yana da kyau mu duqufa wajen neman ilmi zamu ganu duk wadannan abubuwa. Allah Ya Y muna jagora.

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: