NIGERIAN MUSLIM SHURA ASSEMBLY (NIMSA) MECE CE NIMSA?

Danna nan domin shiga group na karatu Online

NIMSA wa ni hadin kai ne da ake
kokarin samun shi a tsakanin
dukkanin musulmai na Najeriya ta
hanyar tattaunanwa tsakaninsu da
kuma shawartar juna. Kalmar
SHURA ta fito a cikin Alkur’ani mai
Girma in da Allah Ya ke bayani
game da muminai a matsayin
“kuma al’amarinsu shãwara ne a
tsakãninsu, kuma daga abin da
Muka azurta su sunã ciyarwa”
Q42/38.
Al’ummar Musulmi su na fuskantar
matsaloli ta fuskoki da dama, da
kuma gazawa ta fannoni da dama
a cikin wannan kasar.
Warwarewar irin wadannan
matsaloli ba zai yiwu ba sai da
hadin kai da kuma shawartar juna
ta hanyar zabar wadanda za su
wakilci dukkanin musulmai da
kuma ba da gudunmuwa a kan
wannan tafiya.
Tun da masallaci shi ne babban
wurin da ya ke hada musulmai
domin gabatar da ibadun su, shi
ne mu ke son mu yi amfani da
Masallaci a matsayin wurin da za
a yi amfani da shi domin hada
al’ummar wannan yanki. Dukkanin
musulmin da ya kasance a gari
dole ya na da masallacin juma’ar
da ya ke yin Salla, ta hanyar
wannan masallacin juma’ar ne za
su taru (wadanda suke wannan
masallaci) su zabi mutanen da za
su yi magana da yawun su
(matsaloli da matakan ci gaba).
Karkashin wadannan masallatai
kuma (su wadancan wakilai) za su
hadu su ma domin fitar da wakili
guda domin karamar hukumar su.
Kamar misali Kaduna ta na da
kamarar hukuma 23 kowane
masallacin jumu’a da ya ke cikin
kowane karamar hukuma zai
bayar da wakili, su kuma
wadannan wakilai na masallatai
za su fitar da wakili da za su rika
fada masa matsalilin al’ummar su.
Wannan wakili shi ne shugaba a
wannan karamar hukumar. Su
kuma shuwagabannin kananan
hukumomi su ne za su hadu
domin su fitar da shugaba a jiha
(ko wace jiha a Nijeriya).
Karkashin wadannan shugabbani
na jihohi su kuma za su fitar da
shugaba guda wanda zai rika yin
magana da kuma zartar da
abubuwa da yawun musulmai
Najeriya.
Shi kuwa wannan zabe da za a
gabatar al’umma su ne wadanda
za su gabatar a karkashin
masallatansu na juma’a ta hanyar
amfani da waya da kuma internet
wanda idan Allah Ya so, duk
wanda mutane su ka zaba shi ne
zabinsu ko shi ne wanda za su yi
mishi biyayya tun da su su ka
amince.
Idan har Allah Ya kaddara wannan
burin na mu ya cika, zai zamanto
al’ummar musulmi za su rika yin
magana da murya guda, kuma
magana mai ta siri.
YADDA A KE YIN RIGISTA:
1) Za ka shiga www.shurah.org
(wanda zai fara aiki nan gaba)
2) Ko kuma ka aika da sakon SMS
zuwa ga 08168361885 ka rubuta
sunanka, jiharka, karamar
hukumarka, unguwarka,
masallacin jumu’arka, (don Allah a
rubuta shi daidai da yadda misalin
yake a kasa)
MISALI: SALISU HASSAN,
KADUNA, KADUNA SOUTH,
UNGUWAR SANUSI,
MASALLACIN DANFODIO
NASARORIN DA AKA SAMU A
HALIN YANZU
Duk da ba a sanar da wannan
tafiyar ba a gidajen yada labarai
da jaridu da masallatai wanda za
ayi hakan da yar dar Allah da
zarar babban shafin mu na intanet
ya zama daidai. Amma kusan
yanzu cikin kwanaki 23 daga
shida ga watan Oktoba 2012 an
sami sakwon SMS sama da 3500
daga bangoriri daban-daban na
wannan kasa. Bayan kuma
babban shafin mu ya zama daidai
duk wanda ya aiko da sakon shi
zai sami damar shiga shafin domin
ci gaba da tafiyar da al’amura
kamar yadda ya kamata.
Muna rokon Allah ya bamu nasara
a cikin wannan tafiya.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

3 responses to “NIGERIAN MUSLIM SHURA ASSEMBLY (NIMSA) MECE CE NIMSA?”
  1. Muhammad Muhammad Avatar
    Muhammad Muhammad

    Salamun Alaikum,
    Ina kira da a hada dukkanin bangarorin musulmai a wannan kungiya ta NIMSA musamman ma Shi’a domin muna bukatan hadin kansu fiye da yadda ake tsammani, kuma suma suna bukatan hadin kanmu, wannan yunkuri ne mai kyau.
    Mu muna da fahintar juna da su, kuma zamu iya shawo kansu wajen amsa wannan gayyata.

  2. Muhammad Muhammad Avatar
    Muhammad Muhammad

    Salamun Alaikum,
    Ina kira da a hada dukkanin bangarorin musulmai a wannan kungiya ta NIMSA musamman ma Shi’a domin muna bukatan hadin kansu fiye da yadda ake tsammani, kuma suma suna bukatan hadin kanmu, wannan yunkuri ne mai kyau.
    Mu muna da fahintar juna da su, kuma zamu iya shawo kansu wajen amsa wannan gayyata.
    Wassalam: Muhammad

  3. AHMAD BELLO KUMO Avatar
    AHMAD BELLO KUMO

    Salaam.
    In our present day Nigeria the Muslims, Sunni or dariqa, lack a unifying leader who will call all & we all respond. This shura therefore is the only way open to us to elect leaders we respect and obey.
    I commend the initiator(s) for this unique and timely effort. May Allah make it come to light & may He protect it from jealousies of other malams and the hypocrites.

Leave a Reply to AHMAD BELLO KUMOCancel reply

Latest updates
Categories