Rarrabuwar Musulmai

·

·

Assalaamu Alaikum warahmatullahi wabarkatuhu,
Wai shin meyasa hadisinmu daya,qur’aninmu daya, manzonmu daya, kalmar shiga addininmu daya. Amma duk da haka muka rarrabu? Shin ayoyin Qur’ani wata tana warware wata ne? Shin nassin hadisan manzon Allah wata tana warware wata ne? Toh meye matsalar da muka rarraba? Da farko, rarrabuwarmu tana tabbatar da manzoncin manzon Allah ne, domin shi ya bada bayanin hakan zai faru. Daga cikin rarrabuwa da al’ummar musulmai sukayi akwai wanda su sun riga sun fice daga addinin musulunci. Akwai wanda kuma sunanan a fake. Basunan basu can, daga cikin wa’inda suka fice daga addinin musulunci misali akwai mu’utazila, kadariyyah, ahmadiyyah, qur’aniyyun, khawaarij. Wa’innan duk malamai sun riga sun tabbatar da cewa sun fice daga da’irar musulunci. Saboda aqeedunsu sun tsabawa wa ainihin ta musulunci. har iyau daga cikinsu akwai rafidawa ‘yan shi’ah musamman ‘yan ithna ashariyyah. Daga cikin aqeedunsu akwai zagin sahabban manzon Allah(s.a.w) wanda wannan yaci karo da koyarwar addinin musulunci.kuma wannan kawai y isa ya fitar da mutum daga musulunci. Sannan kuma suna halatta zina ta hanyar halatta auren mutu’ah. Su gefen wa’inda su basunan basu can, akwai mabiya tafarkin sufaye. Wanda sun kasu kashi wurin 333. Banda wa’inda suka flito baya bayannan. Toh su duka wa’innan mabiya darikun sufayen zaka samu masu darikun ma’ana wa’inda suka kago darikun suna ikrarin su jikokin annabi ne. Kuma suna itikadin zasu ceci mabiyansu ranan tashin qiyaama. Toh abinda yasa mabiya tafarkin sufanci ake musu uzuri saboda da yawa daga cikinsu sun amince da hadisan annabi. Toh meyasa ake samun tsabani tsakanin mabiya sufanci da ahlissunnah? Domin su mabiya sufanci suna daga cikin ‘yan bid’ah. Wanda suke amincewa da cewa akwai bid’ah kyakkyawa. Sannan kuma matsala ta biyu basu bibiyar hadisan manzon Allah(s.a.w) domin gano ingancinsu. Sannan kuma basu bata fassarar da magabata suka bata. Haka kuma ayar al’qur’ani zasu fassarata amma inka tambayesu shin waya gabaceku wurin irin wa’innan fassara da kukayi wa wannan ayah? Bazasu iya kawowa ba. Su kuma mabiya tafarkin sunnah abinada ya bambantasu da duk mabiya wata tafarki ba sunnah ba shine, su bazasu fassara wata ayah ba har sai suna da magabaci cikin magabata na kwarai wanda shima ya baiwa ayar irin wannan fassara, haka kuma hadisi bazasu fara amfani da’ita ba har sai sun tabbatar da ingancinsa, sannan kuma bazasu bata wata ma’ana ba da ta tsabawa fassarar magabata ba. Toh gashi musulmai sun rarrabu kaman yanda annabi ya bada labari zasu rabu, kuma kowa yana ikrarin cewa shine ke kan daidai. Toh shin hanyar zuwa wurin Allah guda nawa ne? Hanya dyace tak. Wacce? Tafarkin annabi. Allah kuma yayi umarni da muyi riko da igiyarsa. Shin meyasa bazamuyi ba? Wasu daga cikin musulmai zakaji suna kafa hujjah da mafarki, wani kawai in yace yayi mafarki yaga annabi yace masa kazaa, toh shikenan wannan ta zama hujjah awurinsu. Kaman sufaye. Wasu kuma zakaji suna kafa hujjah ne da maganar imami, imami wane yace. Kaman mabiya addinin shi’ah. Sannan wasu kuma zakaji suna kafa hujjah da fadin imamai masu mazhabobi, ko kuma fadin wani malami. Wannan har a ko’ina ana samunsu, harma acikin ahlussunnah. Wasu zakaga suna kafa hujjah ne da Qur’ani da hadisi,duk kuma wata hukunci suna nema mata mafaka ne a karkashin wannan iniwowi guda biyu. Wa’innan sune tatattun ahlussunnah. Kuma zaka samu duk abinda sukeyi suna da hujjan yinsa. Basu kirkiran wani abu su saka a addini su kirata bid’ah mai kyau. Sannan basu makalkale wa bayaanan fukaha’u inhar sun samu hadisi da ya rushe wannan magana. Toh meyasa dan’uwa bazaka zama daga cikin wai’nnan tawaga ba? Ma’ana mabiya sunnar annabi? Shin shi shehi da kake bi. Waya tabbatar maka shi ya tsira? Kuma shin wa ya tabbatar maka cewa zaiyi ceto? Sannan waya tabbatar maka cewa inzaiyi ceto zai ceceka? wannan abubuwane da ya kamata ‘yan’uwa su lura dashi sosai. Kada kawai wani ya rudaku. Addinin musulunci abace mai sauki, kuma a bayyane take, babu wani boye boye cikinta. saboda haka ‘yan’uwa ku zama wayayyu acikin addini kada ku zama gidadawa. Allah yasa mudace, Allah ka nuna mana gakiya ka bamu daman binta ka nuna mana karya ka bamu daman kaurace mata. Allah ka ruguje kafurci da kafurai, ka daukaka musulunci da musulmai. Wa’innan wa’inda sukayi fim don batanci wa annabinmu Allah ka nuna musu ayah.
Visit www.facebook.com/groups/ahbaabrasulullah

Posted By Nibras Muhammad

2 responses to “Rarrabuwar Musulmai”
  1. guziri Avatar

    Reblogged this on guziri.

  2. […] Rarrabuwar Musulmai. […]

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: