Bismillahirrahmanirraheem.
Shin wai masu ikrarin sufanci a zamaninmu na yanzu shin sufayen ne da gaske ko kuma ‘yan cuwa cuwa ne? Ya dace ‘yan uwa mu fahimci abinda mukeyi kada mudinga ruduwa da shirme mu daukeshi a matsayin addini. Addini na littafin Allah addini na hadisan manzon Allah(s.a.w). Zan hakaito mana wasu daga cikin kalamai na sufaye na farko domin mu gwada wannan kalamai da kuma halin da wasu masu karyar sufanci suke ciki.
Shin da farko a takaice meye sufanci da ginu akai? Ta ginu ne kan gudun duniya, da bautar Allah. sufi yakan kaurace wa jama’a ya koma kan dutse yayi zamansa yayi ta bautar Allah. Haka abin ya fara yana tafiya. Kafin tafiyar tazo ta samu matsalar da ‘yan bid’ah suka ruda ta. Duk da dai ita sufancin bata da asali a addini, kuma malamai sunyi bayani akai. Amma zan rubuto kalaman ne saboda mabiya sugane ainihin sufanci na da din.
Da Farko ga bayanin Da junaid yayi, wanda in ana magananan sufanci ne dole a sanya su aciki. Domin su kusoshi ne.
قال جنيد رحمه الله: طريقتنا هاذا مقيد بالكتاب والسنة. من لم يحفظ الكتاب ولم يحفظ الحديث فلا يقربن طريقتنا.
Junaid Allah ya gafarta masa yace: WANNAN DARIKA TAMU AN KAYYADE TANE AKAN LITTAFIN ALLAH DA KUMA HADISIN MANZON ALLAH, DUK WANDA BAI KIYAYE LITTAFIN ALLAH BA, KUMA BAI KIYAYE HADISAN MANZON ALLAH BA TOH KADA YA KUSANCI DARIKARMU….
Sannan Ga kuma abinda Sahl al tustari yake cewa:
أصول طريقتنا خمسة.
1.التزام بالكتاب والسنة.
2.الإقتداء بنبي الأمة.
3.أكل الحلال.
4.العفو عن من ظلمك.
5.لزوم التوبة.
Yace: asalin hanyar mu Guda biyar ne:
1.ka lazumci littafin Allah da sunnar annabi(s.a.w).
Toh dun Allah yanzu ina masu kiran kansu sufaye ina sunnar annabi? Sai dai abaki. Abinda ake nufi da lazumta shine: ya zama koda yaushe kana mai aikatashi, da zarar kaji ance annabi yace kaza, ko yayi kaza, kaima ka aikata shi. Ance annabi na son aswaki, kaima kaso aswaki, ance annabi na barin gemu, kaima bar gemu, ance annabi na sallan dare, kaima tashi kayi, ance annabi na azumin litini da alhamis,kaima daure kayi. Ance annabi baya barin tufafinsa yaja kasa, kaima dage naka, irin wa’innan su ake kira sunnah, da zarar ankawo maka hadisi inagatacce, ta dace da son zuciyarka bata dace ba karbeta. Amma
rawa, kida da fada a baki, ba ita ke nuna bin sunnar annabi ba. Wani malami yake cewa:
ومن محبته صلى الله عليه وسلم. انتصار سنته.
Yace yana daga cikin son manzon Allah(s.a.w) taimakon sunnarsa… Ina masu kururuwan son annabi? Ba yiwa annabi waka da rawa shi ke nuna son annabi ba. A’a, ka taimaki sunnarsa, ka yada addinin da yazo dashi. Ka bi duk abinda yace ka kaurace wa abinda yayi hani akai….wannan itace hakikanin son annabi, amma bawai fada da baki ba.
2.na biyu yace, yin koyi da Annabi(s.a.w)..
Ya zamto duk abinda zakayi kana koyi da annabi ne. Kafin ka zama sufi na gaskiya sai ya zamto duk abinda zakayi kana koyi ne da annabi(s.a.w) ba zaka kirkiri wata kalar ibadah dabam ba irin ta annabi ba, ba zakayi sallah ba irin ta annabi ba. Ba zakayi zikiri ba irin ta annabi ba.
3.na uku yace: cin halal. Duk wani sufi na gaskiya zakaga ya toge kan cin halal. Babu ruwanshi da haram..
4.asali na hudu yace, yafiya ga wanda ya zalunce ka.. Duk sufi na gaske babu ruwanshi da hayaniya, duk abinda aka mishi yafewa yakeyi. Ba zai zalunceka ba, kuma inka zalunce shi sai ya yafe.
5. Sai na biyar yace: lazumtar tuba.. Duk sufi zaka sameshi a kullum mai lazumtar tuba ne… Mai kankan da kai zuwa ga Allah…
Wa’innan sune kalaman sahl al tusturi. Dun Allah ‘yan’uwa ku kula da irin wannan zantuka na hamshakan malaman sufanci na gaske… Idan aka dauki wa’innan ka’idoji aka sanya akan masu ikrarin sufanci na yanzu za’a samu sufi ko guda daya? Ko daya babu. Sannan meyasa basu fitar da irin wannan kalaman suna tallata wa mabiyansu? Dun Allah ga aiki na baiwa duk wani dan’uwa mabiyin darikah..
1. Ya dauki wannan ka’idojin wanda kusoshin sufanci suka fada, ya daurashi kan shehinsa, ko malaminsa, yaga inba shehinsa ko malaminsa na kan ramin halaka ba, yanzu dun Allah suwaye masu fada da kitaab wa sunnah? ‘yan dariku, gashi kuma sahl ya fara kawo cewa darikarsu tana rataye ne da kitaab wa sunnah.
2. Na biyu.. Meyasa ba’a bude majalisi na littafai wanda sufayen zamani suka rubuta? Irin littafin jawaahiru ma’ani, Meyasa? Shin sun qunshi gaskiya kuwa? Su duba duk wani malamin sunnah in ya buga littafi ana bude majalisi a karanta abinda ya rubuta.. Amma ku tambayi kanku meyasa ba’a karanta naku?….
Daga karshe duk maison gane hakikanin tasawwufanci, to ya binciki wallafe wallafen wa’innan bayin Allah. Irinsu sahl al tusturi, ibrahim ibn adham, irinsu junaid. Da abdulkadir jailani. Domin shima abdulkadir jailani ahlussunnah ne. Duk masu maqalewa dashi a tafarkin darika karya sukeyi… ‘yan’uwa matasa mabiya darikah. Wallahi inkunason gaskiya ku binciki littafan wa’innan maluman da kuma tarihinsu, wa’inda sune jagorori a harkar sufanci,kusha mamaki. Wallahi sai kun gudu kunbar wannan shirme da kukeyi da sunan addini… Zaku tabbatar an rudeku.. Mu mun karanci sufancin zamani da aqeedunsu, sai muka gujesu. Kaima dan’uwa ka karanci aqeedar ahlussunnah mana a rubuce muga ko. zaka kisu? Kadaina amfani da malam wane yace, ko wane ya aikata kaza. A’a karanta a rubuce ka fahimta, wannan itace hakikanin gaskiya.ina aka samu wai malami ya zauna a gida bayi da aikin komai wai sai roka wa mutane Allah. Shin wannan abu na da asali a addini? Malam baka fita jihadi, baka fita wa’azi, kai kenan kullum ka tsubbace kanka wuri daya? Shin haka annabi ya rayu ta wannan hanya? Ina aka samu raba wa mutane darika? Shin akwai wani nassi da ya tabbatar da haka? Ina aka samu kirkirar bid’ah da sunan mai kyau? Yaa dace jama’ah ayi lura, yanzu lokaci ya wuce da za’ayi ta mana nuku nuku. Komai ya fito fili mun gane. Maison gaskiya yaci gaba da bincike Allah zai nuna masa.. Jama’a ayi hakuri in na tsawaita…. Allah yasa mugane, Allah ka shiryar damu Hanya madaidaiciya. Wanda kuma ranshi ya baci da zantuka na, yayi hakuri. Ni inayi ne saboda kauna da nakeyi wa ‘yan’uwa wanda suka kauce wa hanya. Wassalaamu alaikum wa rahmatullah.
Leave a Reply