WASU DAGA CIKIN HAKKOKINMIJI AKAN MATARSA(Sheikh kabiru Haruna Gombe)

·

·

WASU DAGA CIKIN HAKKOKIN
MIJI AKAN MATARSA.
1-Soyayya ta gaskiya.
2-Tsare Amana Miji.
3-Tausasawa miji da wasa da
dariya dashi.
4-Tsare sirrin miji.
5-Kada ta fita daga gidansa sai da
izininsa.
6-Baza tayi azumin nafila ba sai da
izininsa.
7-Ta yarda ya sadu da ita duk
lokacin da yake bukata, dan
Annabi Mai tsira aminci yace duk
matar da taki mijinta ya sadu da ita
a duk lokacin da yake so, to
Mala’iku zasuyi ta la’antar ta
bazasu su daina ba har sai lokacin
da ta yarda da shi. (BUKHARI/
MUSLIM).
8-Ta saurari mijinta kuma tayi
masa biyayya matukar ba aikin laifi
ya umurceta dayi ba.
9-Mace ta nisanci raina abin da
mijinta ya bata, domin Annabi
muhammad mai tsira aminci yace
“Mata zasu shiga wuta ne saboda
kafurce wa mazajensu, wato raina
alherin miji” (BUKHARI/MUSLIM)
10-Kada mace ta cutar da mijinta
da magana ko da aiki.
11-Mace tayi ado da kwalliya wa
mijinta, saboda Annabi mai tsira da
aminci yace “Allah kyakkyawa ne,
kuma yana son kyakkyawan
abubuwa, (IMAM MUSLIM YA
RUWAITO)
12-Mace ta tsare dukiyar mijinta
dana ‘ya’yansa harma dana
gidansa, dan Annabi mai tsira da
aminci yace “Mace mai kiwo ce a
gidanta, za’a tambayeta abin da ta
kiwata.
13-Mace tayi gaggawan baiwa
mijinta hakuri a duk lokacin da
taga yayi fushi, Tace masa, dan
Allah kayi hakuri, bansan abin da
nayi zai bata maka rai ba, ka yafe
mini dan girman Allah.
14-Mace tayiwa mijinta dukkan irin
aikin da ake bukata ayishi a gida.
15-Mace ta kyautata halayenta ga
iyalan mijinta.
16-Mace kada tayi abokantaka da
mugayen kawaye, sai su hallakar
dake baki sani ba.
17-Mace ta zama mai tausayawa
mijinta, kamar yadda uwa take
tausayin ‘Danta.
18-Mace ta zama mai Biyayya ga
mijinta.
19-Mace ta zama Abokiyar rayuwa
ga mijinta.
20-Mace ta kusanci dukkan abin
da mijinta yake so.
21-Mace ta nisanci dukkan abin da
mijinta yake ki
22-Kiyi murmushi a duk sanda
mijinki ya kalleki.
23-Kiyi masa addu’a a duk lokacin
da zai fita, kice adawo lafiya Allah
ya bada sa’a.
24-Kiyi masa addu’a kuma a duk
lokacin da bakya ganinsa bayan
bayanan.
25-Idan mijinki ya dawo ki karbi
abin hannunsa, tare da yi masa
sannu da zuwa, dan girmama shi.
26- A duk samda zakiyi magana da
mijinki ki gaya masa magana mai
dadi, mai tabshi, kada ki daga
muryanki akan nasa, kuma kada ki
masa tsawa har ki harare shi.
27-Ki zama cikin tsabta da kamshi
mai dadi duk lokacin da kuke tare.
28-Ki sanya hijabi a duk lokacin da
kuke tare da wadanda ba
muharramanki ba.
29-Kisa lokaci idonki, ki kuma
shafa jan baki, kuma ki shafa
turare, amma sai kuna tare dashi a
gida dan mace bata shafa turare
ko janbaki ta fita anguwa dashi.
30-Ki kaskantar da kai dan biyayya
a gare shi.
31-Ki san lokacin da yake dawowa
dan kada ya sameki a cikin
kazanta, ki kuma san lokacin cin
abincin sa dan ki tanada ba sai
yazo yana nema ba.
32-Bayan kin gama masa komi ki
tambaye shi ko yana da wata
bukata a gareki, dan mi biya masa
ita.
33-Kar ki nuna murnan ki idan
wata hasara ta same shi, ki nuna
masa kamar kece kika yi hasarsar.
34-hakanan kiyi murna da duk
wani alherin daya samu.
35-Ki zama kamar matan
sahabbai, yadda sukewa
mazajensu. Idan miji zai fita sai
suce a dawo lafiya, kar ka kawo
mana haram zamu iya hakuri da
yunwar duniya, amma baza mu iya
hakuri da azaba ba gobe lahira. In
ya dawo kuma su karbeshi, suyi
Masa sannu da zuwa suce masa
yau wace aya ne ta sauka kuma
wane hadithi manzon Allah mai
tsira da aminci ya fada.
In dare yayi kuma sai tayi wanka,
ta zabi tufan da yafi kyau ta
rangada ado, ta fuskanci mijinta
tana tana fara’a tana murmushi,
tana ce masa kana da wata
bukatane gareni? In kana da
bukata ka biya.
To ya ke ‘yar uwa musulma, idan
kina son tsira duniya da lahira ki
kiyaye harkokin kuma kiyi aiki
dasuidan ba haka kuma ki tuna
ranar mutuwa da za’a saki cikin
kabari ba taburma, ba katifa, ba
gado, ba window, ba kofa, bama
wata iska da zata sameki, daga ke
sai halinki. A cikin kabari a doka
miki tukwane a kanki a saka
itatuwa a tattare, asa ganye a
doddara, a kwaba kasa a lillike
sannan a kawo sauran kasan data
rage a rufe kabarin da kike ciki
Innalillahi wa inna ilaihi ra’jiun.
Idan kuma kina son Allah Ta’ala ya
yalwata, kuma ya haskaka, kuma
kabarinki ya zama dausayin
Aljannah to ki kiyaye wadannan
harkokin mijinki a kanki domin
Annabi mai tsira da aminci yace da
wata mace, “Mijinki Aljannarki ko
wutarki, ki duba kiga yaya
matsayinki a wurin mijinki, kin tsare
hakkokin sa ko baki tsare ba, idan
kin tsare to ya zama aljannar ki
kenan, (IMAM AHMAD YA
RUWAITO KUMA ADAWI NE YA
INGANTA HADITH DIN).
Allah ya bamu ikon yin daidai a
dukkan al’amurran mu.

38 responses to “WASU DAGA CIKIN HAKKOKINMIJI AKAN MATARSA(Sheikh kabiru Haruna Gombe)”
 1. Lawal Bala Anchau Avatar
  Lawal Bala Anchau

  Allah Ya biya da Al-jannar Firdausi.

 2. qatada Avatar
  qatada

  Allah biyaa

 3. Muhammad chigari kumo Avatar
  Muhammad chigari kumo

  Sunnah sak
  bidi’a sam
  tauheet sak
  shirka sam
  allah taimaki duk wani ahlun sunnah
  da duk wani malaminmu
  08184863611

 4. Hamisu salisu tofa Avatar
  Hamisu salisu tofa

  Assalamu alaikum.Allah ya saka da alheri saboda da fadakar da yan uwa ahlul sunnah da sauran musulmi.

 5. Usman hamza ahmad Avatar

  Assalamu alaikum malam ga tambaya:don allah menene hukuncin cin abincin kirisimeti.kuma ya halarta mutum ya yankamusu.bissalam.

 6. abdullahi yusuf jalam Avatar
  abdullahi yusuf jalam

  mallam allah ya saka da mafificin alherinsa jannatul firdausi ya kareka daga mahassada da marasa son gaskiya har karshen rayuwarka

 7. abdoullahi aboubakar Avatar
  abdoullahi aboubakar

  assalamu alekum ahlul suna tan bayata itace ahlul suma dabam musulmi dabam ina so ababbacemin

  1. HabibuLLAH Avatar
   HabibuLLAH

   Assalamu alaikum, nidai gyara zanyi maka: Ahlus-Sunnah take ba suna ba ko suma kamar yadda kace. Allah yasa mu gyara

 8. MAIMUNA UNGUWAR RIMI Avatar
  MAIMUNA UNGUWAR RIMI

  Assalamu alaiku,malam kabir naga abunda kuka taru kukayi na sunna tv, Allah yasa mu haka a nan gaba kuma dukkan mu ya zame mana (faradun farillah ne)mu dunga kalloh.Allah yasa kani na kabiru ya gado irin sunan da sauran ayyukan alkhairi.amee

 9. Aisha Avatar
  Aisha

  Assalamu alaykum,tambayata,mijin da ake kyautata mashi amma baya godewa fa?a kullun neman laifin matar shi yake. Dan Allah ayi mani bayani,Allah Ya saka da khairan

  1. Abubakar Auwal Gagi Avatar
   Abubakar Auwal Gagi

   Yar’uwa kada kigaji, kichi gaba da kyautata masa, kada kikasa. Allah zaibaki lada.
   Allah yataimakeki da dukkanin sauran mata, ameen!

 10. Marwan B. Kabir Avatar

  Allah Ya biya Sunnah Sak

 11. Saidu bawa gwani Avatar
  Saidu bawa gwani

  Allah ya bamu ikon bin umarnin Allah da manzon sa (s.a.w) ameen

  1. Nuramohdnabala Avatar

   4m

 12. Khadija aliyu Avatar
  Khadija aliyu

  Allah ya bada lada

 13. El-abdul Avatar

  May protect ustaz amen

 14. Abdullahi Ali Avatar
  Abdullahi Ali

  Assalamu alaikum, more grease to ur elbow.contnue with ur da’awa insha Allah, Allah is with those dat ‘re with him,no jinn,no human o evil dat ‘ll mk u 2 b afraid death.

 15. safiya umaru Avatar
  safiya umaru

  ALLAH YA SAKA DA ALKHAIRI.

 16. Ya Ubangiji ka bamu daman kare hakkokin junanmu amim

 17. Muhammad Aminu Bunza Avatar
  Muhammad Aminu Bunza

  As-Sheikh Malam Muhammad Kabiru Haruna Gombe, Allah Ya saka maka da Aljannar Firdausi, Amiin.
  Mu kuma da mu da matan mu, Allah Ya ganar da mu hakkokin junan mu, kuma Ya bamu ikon bayar da su yadda ya dace, Amiin.
  Mun gode.

 18. adamu dalhat Avatar
  adamu dalhat

  karanta lalle akwai karin ilimi!
  Allah ya saka alkhairi mallam.

 19. Abubakar Auwal Gagi Avatar
  Abubakar Auwal Gagi

  Allah yataimaki Mallam, da dukkani masu da’awar sunnah, amin!

 20. Anas ibn ibrahim Avatar

  Assalamu,alaikum malam don allah inada tambaya menene hukuncin wanda akasamusu ranada budurwa sannan bayan ansamusurana dagabaya saiyafara zinada ita yawannan auren xaikasance malam akwai aure atsakaninsu ko babu?

 21. Musa Ibrahim K. Avatar

  Allahu Akbar. Allah ya saka maka da Aljannat Firdausi amin. Sunnah sakkh,bid’a sam.

 22. Musa Avatar

  Allah yakaremu daga sharin munkirai

 23. Rabi'u Abdullahi Bawada Avatar
  Rabi’u Abdullahi Bawada

  JazakAllahu bi khair

 24. Assalamualaykum

 25. Nuramohdnabala Avatar

  Hhm

 26. Abdullahi ahmad Avatar
  Abdullahi ahmad

  Assalamu alaikum, dafatan Allah yasamaka masu yada addini acikin wan an shafi kuma Allah sakawa malamsammu da alheri

 27. ibrahim salisu Avatar

  fatan alheri agate ka malam

 28. ibrahim salisu Avatar

  aslm

 29. asmau rabiu Avatar
  asmau rabiu

  Slm Allah ya saka sa alheri malam.Don Allah malam inason insan hakkokin Ma ce kan miji sannan minene adalci kuma ya akwyinsa tsakanin mata biyu Ko fiye da haka?shin rashin adalci na shafar iyalii idan miji baiyi?

 30. aisha yusuf Avatar
  aisha yusuf

  may almighty god protect our leader

 31. hauwa saleh Avatar
  hauwa saleh

  may d almighty Allah protect n guide us in a right path

 32. Muhammad Abdullah (M. juli) Avatar
  Muhammad Abdullah (M. juli)

  Assalamu alaikum, sunna suna ta tara, sannan bid’a ma suna ta tara (wata bidi’ar dole ayita, ga karamin misali posting din malamai zuwa garuruwa yin tafsir, yana da kyau, amma annabi yayi ??? bidi’a kenan mai kyau) ina jan kunnen yan izala da amfani da kalmar bid’a sam, domin ko sau nawa ka furtata yaudarar kanka kakeyi, akwai mai kyau sannan mara kyau, sunna kuma dole abi indai an tabbatar da sunnar gaskiya ba sunna naira ba. wassalam.

 33. muh'd Avatar

  Allah amfa nadai

 34. sani gimba Avatar
  sani gimba

  allah ya tabbatar da diga diganmu akan bin sunnan manzon allah s.a.w

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: