‘YAN MATAN FACEBOOK(Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe)

‘YAN MATAN FACEBOOK
Hausawa suna cewa ‘Yammata
adon gari, In ba ku ba gida, In kun
yi yawa….. .Annabi (S.A.W) ya na
cewa: “ Mata warin takalmin ‘ya’ya
Maza ne” Alqur’ani mai girma
kuma yace: “Su sutura ne gareku
(maza) kuma sutura ne gare su
(mata)”
Lalle Allah ya halitta Mata cikin son
kawa da kwalliya, kamar yadda
hakan ba haramun ba ne, matukar
ana cancada adon ne cikin iyakar
Musulunci.
Daga cikin abubuwan da suke ba
ni mamaki a wannan dandali akwai
yadda na ke ganin ‘yan mata ke
saka hotunansu tsirara don Mutane
su kalla suji dadi ba tare da sun
biya sadaki ba, abin ban mamakin
ma har da wasuu daga cikin matan
aure. Amma abin tambaya anan
shine: wai me ke jawo wannan hali
na rashin kunya da yakamata ne?.
Tsammani na, abubuwan da ke
jawo hakan:
• Wassu ba su san cewa hakan
Harmun ba ne.
• Wassu kuma tallen kai ne.
• Wassu kuma fitsara ce zalla!!
• Wassu kuma gaurin gwauranta
ne.
• Wassu kuma wasa da Nishadi ne.
• Wassu kuma ban sani ba!!
Allah madaukakin sarki a cikin
Littafinsa ya umarci Mata su rufe
jikkunansu da tufafi, ka da su
baiyyana adonsu sai ga
Mazajensu ko Muharramansu.
Kamar yadda Allah ya kira irin
wadannan shiga da sunnan fita irin
ta Jahilyyar farko. Me wannan hali
inji Allah Jahila ce!!!
In ka tambayi Maza, ko za ku iya
aurar irin wadannan matan? Sai ka
ji sun ce maka: Allah sauwaka!!
Dalilinsu wai bayan kowa ya san
komai nata!!!
Manzon Allah yace: “ Wanda ba ya
damuwa da wa zai shiga kan
Matarsa, ba zai shiga Aljanna ba”
Tirkashi!! Ina ga wadda ta ke tallata
kanta wa duniya baki daya???
Wadanda su ke ganin saboda kirar
da Allah yai musu, ba wanda zai
gani bai hadiyi yawu ba, sai muce:
Manzon Allah yace: “ Akwai wassu
‘yan Wutan da babu su a
zamanina, cikinsu akwai: “Mata ma
su shigar tsirara, ko sun sa tufafi
jikinsu a baiyyane ya ke, sun
karkace suna kokarin karkatar da
mutane, Ba za su shiga Aljanna
ba, kamshin ta ma, ba za su ji ba”
Allah ka raba mu da wannan
rashin rabo!! Ameen
Rashin Aure ya ke sa Wassu shiga
wannan sana’a, don ragewa kai
gauri da gaunin Tuzurunta ka,
Maganin wannan karbar Sunnar
Manzo ta hanyar Aure. Wanda ya
sanki ‘ya mace ba zai aure ki ba, in
kuma ya aura. Ba za ki yi kima a
idanunsa ba,har Abada. Tsalle
daya shi ke jefa mutum Rijiya.
Ya ‘Yar uwata ki rasa abin wasa da
shi, sai Mutuncinki da na ‘yayanki,
Allah ya halasta wassu wasanni,
ya kuma sanya cikekkiyar nutsuwa
cikin karatun Alqur’ani. Balle uwa
Uba wasan miji da mata, Ki
sumbace shi, a baki lada, ki fada
masa magana mai dadi ki samu
lada, Dukkan abin da zakiyiwa
mijinki na kyautatawa lada, Balle
uwa uba…
Cikin Mata akwai kamammu ko
nan cikin Facebook, adadinsu
kuma kara yawa ya ke, Wannan
yasa na rubuta wannan makala
don ‘Yar uwa kada jirgin Annabi
nuhu ya ta shi ban da ke ciki.
Annabi Mai tsira da aminci yace:
‘’WANDA YA TUBA DAGA LAIFI
KAMAR WANDA BAI TABA YIN
LEFIN NE BA”
‘Ya Allah ka tsare mana Kannanmu
da Yayan Musulmai.
AMEEEEEEEEEEEEE
EEEEEEEEEEEEEEN

Click Here to Support our work

102 Comments

 1. Gaskiya wannan abu buwa da aka zayyana duk suna faruwa awannan zamani damuke ciki ,sai dai dami mukoma ga ubangiji da addu’a ya yaye mana wannan masifa , ya kuma tsare mamu imanin mu a wanna yanayi da muke ciki, shi kuma marubuci Allah ya saka mashi da alhairi ameen summa ameen

 2. Allah ya tabbatar maka da alkhairin duniya dana lahira,Allah ya bamu ikon gyara halayenmu,ya Allah ka shiryemu baki daya.

 3. Jazzakallahu khairan Allah ya kara maka basira da fasaha da hakuri da jumriya kuma da tsayuwa akan gaskiya bi ma’ana tsayuwa akan Al-quran da kuma sunnah Annabi Muhammad [s.a.w] mu kuma Allah yaba mu ikon aiki da abinda ka ilmantar da mu Ameeeeeeeeeeeeeeeeeen.

 4. Allah yasaka da alheri malam kuma ya kareka daga makiya kuma malam atayamu du’ai game da halin rayuwa na yau.

 5. A gaskiya ‘yan matan fb suna abinda bai dace ba,kamar yadda suke saka hotunansu a profile don su bayyanadda kyakkyawar surarsu ga mazajen da ba nasu ba,haka kuma suke ta rubuto kalamai masu dadin ji ga samari,kai ta’asar su ta wuce a fada dan sai kace karya ce,Allah ya shiryamu amin.

 6. Alhamdu lillahi! Alhamdu lillahi!! Alhamdu lillahi!!! Madallah da irinku. Allah ya biyaka/ki da kyakkyawar rahama da albarka.

 7. Allah bada lada,may allah (s.a.w) cont 2 protect our malam.ameen.dafa tan za’a gyara.

 8. Mallam wlh bamuda abinda xamu iya sakamaka dashi ba saidai fatan alkhairi allah ya bamu ikon gyarawa amin kuma ya dada kareka daga sharrin makiya

 9. Assalamu alykum mal. Allah ya saka maka da alkhairi yasa kuma mufi karfin zukatan mu ameeeen.

 10. Slm,mlm aganina wannan badala rashin mallakar hankaline,tsoron Allah,rashin tunawa yaushe azarailu zaizomaka,dakuma ranar Alkiyama.Allah ya karemu da ‘ya’yanmu yakuma shiryi masu yin haka.Ameeeeeeen.daga maman Walid,brigade,layin maizara bayan kasuwa

 11. Slm ai kabiru gombe zunubin da kake da karyar da kake da sharrin da kake wa sufaye ya fi laifi akan abinda yan matan suke tunda kai qazafi kake saboda yan kudi kadan da kake samu daga gurin qungiya Allah ya tsare musulmi daga sharrin rubabbun musulmai irin ka

 12. Wannan bayani ko kuma ince matashiya da mallam yayi tana da matukar amfani ga al’ummar musulmi baki daya, musamman wadanda akayi matashiyar domin su” wato mata. Allah ya saka wa mallam da alhairi mu kuma allah ya bamu ikon gyarawa.

 13. Mallam Allah yasaka da alkhairi. Allah ya kara basira Allah taimake ka da muslumai gabaki daya AMEEN.

 14. Hakika lallai ne maza bazusu lalace ba, batareda mata sun bada kansuba dun haka mata kuyi gyara akan wannan hali da kukeyi Allah, S. W. A ya shiryeku damu baki daya Ameen.

 15. Mal Allah yasaka da alkhairi,yarubanya hasanarka,yakankare sayyi’a dinka,ya albarkaci iliminka amin.

 16. Allha saka da Alkayree ya nunamana gaskia gaskia ce yabamu ikon binta ya kuma karemu daga sharrin shedan da rudin dunia.yabamu ikon bin Qurani da sunnar manzo Allah saw

 17. Allah ya karawa malam lapia.Yakareshi daga sharrin masu sharri yasaka maka da gidan anjanna FIRDAUSI ameeen

 18. ALLAH
  ya sakawa malam da alkhairi kuma ya bamu ikon yin aiki da abinda ake fadakardamu a koda yaushe

Leave a Reply

%d bloggers like this: