Wahayi Ya Tsinke, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ya Shiga Damuwa
Tun daga wancan lokacin da muka fada a baya Jibrilu (AS) sai ya daga kafa bai sake ziyartar manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ba. Har sai da manzo ya shiga cikin shaukin dawowar wannan bakon arziki. Sai bayan da watan Ramadhan ya shude ne sannan Jibril (AS) ya sake zuwa da suratul muddasir wadda a cikin ta Allah yake umurnin manzonsa da ya tashi ya fara wa’azi. Zama ya kare kenan, babu sauran hutawa. Domin za a shiga gwagwarmayar kira zuwa ga gaskiya da tabbatar da ita, aikin da ba zai kare ba sai ran da rayuwa ta kare. Manzon Allah kuwa bai yi kasa a guiwa ba, ya tashi tsaye haikan wajen kira zuwa ga musulunci. Amma sai ya natsu ya karanci mutanensa. Domin akwai masu saukin kai da saurin fahimta da jawuwa zuwa ga gaskiya, akwai matsakaita. Sannan akwai masu taurin kai kamar daga kashi aka halicci zukatansu. Don haka, sai ya shirya tsarinsa na kira a sirrance da bin daidaikun mutane wadanda ya tabbatar za su iya hada sahun farko na masu imani.
Leave a Reply