ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam Majalisi Na 68(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

Jarrabawa Ta Kai Makura
A daidai lokacin da manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam da sahabbai suka fita daga waccan jarabawa ta daurin ta-la-la da muka fada sai kuma wata sabuwar jarabawa ta sabka a gare su. Wannan jarabawa ita ce rasuwar manya-manyan mutane biyu da suka zamo jigogi ga addinin musulunci; Abu Talib da Nana Khadijah. Sun rasu a cikin mako daya, a karshen shekara ta 10 daga farkon annabta. Duba Fathul Bari na Ibn Hajar, (7/194). Shi dai Abu Talib kamar yadda aka sani ya kasance mai cikakken goyon baya da ba da gudunmawa da kariya ga manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam. Kuma duk wata barazana da take fuskanto manzon Allah to, yakan tare ta ne bil-hakki har sai in da karfinsa ya kare. Ita kuma Nana Khadija ita ce uwargida mai kwantar da hankali da samar da natsuwa gare shi ta hanyar so da kauna da take yi masa da kyawawan shawarwari managarta da take ba shi, ga kuma amfani da kudinta wajen ci gaban addini. Babu shakka mutuwarsu ta samar da wani gibi mai yawa a cikin zuciyar ma’aiki. In da ma ace dukan su sun cika a kan imani, to da lamarin mai sauki ne. Domin makomarsu abin farin ciki ce. Ita dai Khadija daman tun da farko ta musulunta, kuma ta ci gaba da yin sallah da sauran al’amurran neman kusanci da Allah har ma Allah ya aiko Jibrilu Alaihis Salam da sako zuwa gare ta ta hannun mijinta cewa, Allah ya yi ma ta tanadin gida a mafi kololuwar aljanna. Amma shi Abu Talib har zuwa lokacin mutuwarsa ya kasance mai imani da gaskiyar manzon Allah a zuciyarsa, kuma yana furta haka sau da yawa a gaban jama’a. Amma kuma bai cika sauran sharadin musulunta ba, shi ne; mika wuya ga manzon Allah da janyuwa zuwa ga umurninsa. A lokacin da ya zo cikawa sai mafi kusancin mutane daga cikin kafiran abokansa suka zo duba shi a daidai lokacin da manzon Allah yake rungume da shi yana rarrashinsa ya shiga musulunci. Su kuma sai suka rinka nuna masa cewa, idan ya yi haka zai yi abin kunya ne, don kuwa da tsufansa don ya ga mutuwa ya saki addinin mahaifinsa Abdulmuttalib. Daga karshe ya yi wata waka mai ban tausayi wadda a cikin ta yake nuna cewa, kawai abin da zai hana shi ya faranta ran manzon Allah ta hanyar furta kalmar shahada shi ne gudun a dauka cewa, ya yi raki ne. Allahu akbar! Babu shakka musulunci rabo ne. Miyagun abokai kuma hatsari ne. Sannan Allah ba ya son musuluncin da za a yi shi don dadada ran waninsa, ko da kuwa wanin nan fiyayyen halitta ne Sallallahu Alaihi Wasallam. Allah Tabaraka Wa Ta’ala yana cewa:
((وما أمروا إلا ليعبدوا الله مخلصين له الدين حنفاء..))
Ma’ana:
“Ba a umurce su ba sai don su bauta ma Allah suna masu tsarkake masa addini, masu kauce ma shirka..”.
Don haka, duk wanda zai yi addini ba don Allah ba ya yi a banza, kuma Allah ba zai karba ma sa ba.
Wani abin lura a nan shi ne yadda Allah yake jujjuya musulmi daga wata musiba zuwa wata. Kada kayi tsammanin wai masoyan Allah ba su gamuwa da jarabawa. Bil-hasili ma ta fi kama masoyan Allah don abin da ke tattare da ita na girma da matsayi da yawan lada bayan shudewar ta.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates