Da’awar Musulunci Ta Fara Fitowa
Fili
Shekaru uku kenan cif aka yi ana
sirranta da’awar musulunci tare da
kiran daidaiku wadanda ake ganin
dacewar su da shiga musulunci a irin
wannan lokaci mai tsanani. Kuma
sama da mutane 40 ne suka samu
horarwa ta musamman daga manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam
wadanda suka hada da iyalansa da
mafi kusancin mutane zuwa gare shi.
Sai kuma wadanda Allah ya zabe su
don shiga cikin wannan ayari mai
albarka daga cikin wadanda su
wadannan bayin Allan makusantan
manzon Allah suka janyo. Sun
kasance cikin wani yanayi na bakunta
a cikin mutanensu, kasancewar su a
kan wani addini da wata akida da
take bakuwa a cikin al’ummarsu.
Amma kuma sun yi riko qam-qam da
addininsu, suna ji da shi matuka,
kuma a dare da rana tunaninsu shi
ne ta wace hanya ne za su nusar da
mutanensu a kan gaskiya? Al-Guraba’
Al-Awwalun, na Salman Al-Auda,
shafi na 133.
Wadannan bayin Allah da suka samu
horaswa a wannan lokaci sun
kasance daga gidaje daban daban,
mafi yawansu kuma manyan mutane
ne da matasa ‘yan gata da ‘ya’yan
masu iko. Akwai kuma wasu masu
rauni wadanda ke cikin kangin bauta
ko kuma cikin halin kuruciya kamar
su 13. Su ne kuma suka zama tubalin
musulunci na farko wanda aka gina
fadarsa a kan su. Su ne masu zurfin
ilmi a cikin sahabbai, masu bayar da
fatawa, masu yanke hukunci. Kuma
duk wata arangama da dauki-ba-dadi
da aka yi a bayan haka su ne suka
zamo a sahun gaba. Rasulullahi Fi
Makka, na Al-Yahya, shafi na
111-112 da kuma As-Sirah An-
Nabawiyyah na Sallabi, shafi na
102-103.
Bayan wannan tsawon lokacin ne
Allah ya sauko da umurninsa zuwa
manzonsa Sallallahu Alaihi Wasallam
yana cewa: “Ka yi gargadi ga
danginta mafiya kusanci” yana nufin
kabilun Quraishawa da suke Makka.
Suratus Shu’ara’: 214. Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam take ya
yanke shawarar matakin da zai
dauka. Ya nemi kafar sadarwa mafi
karfi ta wancan zamani da salo mafi
kaifi wajen isar da sako zuwa ga
mutane. Sai ya hau kan dutsen Safa
yana cewa, “Ya Sabahah! Ya
Sabahah!!” Irin kiran da masu shelar
yaki suke yi don yekuwa da gargadi.
Kafin ka ce me ye wannan, duk cikar
Makka da batsewarta ta hadu a
gabansa don jin abin da yake yekuwa
a kan sa. Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam sai ya yi shimfida
mai karfi wadda ta zarge su, ta
hujjace su. “Idan na ce maku a nan
saman dutsen nan ina hangen kurar
wata runduna da za ta kawo hari
zaku gaskata ni?” Suka ce, kwarai
kuwa. Ai kai ba makaryaci ba ne. Ba
mu taba sanin an zarge ka da karya
ba. Sai ya ce: “To, ni mai gargadi ne
daga Allah don ku bi shiriyarsa, ku
kama godaben gaskiya kafin wata
azaba mai tsanani – in kun kiya – ta
cim maku”. A nan ne fa suka yi
cirko-cirko, suna kallon juna. Ba
wanda ya iya buda baki ya ce uffan,
sai mafi karancin arzikin wannan
al’umma shi ne Abu Lahabi. Shi ne
ya furta mummunar magana ga
ma’aiki, yana mai cewa, “Tir da
halinka ya Muhammad! Yanzu a kan
wannan ne kake kiran mu?!” Daga
nan kuma taro ya watse. Wannan
haduwa ta zamo ita ce ajandar
tattaunawar jama’a na cikin gida da
kasashen waje a tsawon wannan
shekarar. Kuma a kan abinda ya faru
a wannan wurin ne madaukakin sarki
ya saukar da Suratul Masad wadda ya
fallasa Abu Lahabi a cikin ta gami da
mugunyar matarsa. Kuma Allah ya
kama sunansa baro-baro a cikin
wannan sura domin ya tozarta shi
kamar yadda ya tozarta fiyayyen
halitta. Sahih Al-Bukhari, hadisi na
4971 da Sahih Muslim, hadisi na
208.
Abu Lahabi dai mutum ne da Allah ya
tara ma sa ni’imomi da dama. Domin
kuwa kamilin mutum ne, kyakkyawa,
mai girman matsayi da wadatar
arziki. Ga shi kuma baffan ma’aikin
Allah. Amma kash! Duk wadannan
abubuwan ba su amfane shi ba, shi
da muguwar matarsa Ummu Jamil.
Maganar Allah ta tabbata a kan su
suka mutu tozartacci, suna
makamashin Jahannama. A cikin
‘ya’yansu hudu Utbah da Mut’ib da
Durratu duk Allah ya yi masu arzikin
musulunta. Sai Utaiba ne ya mutu
kafiri. Dalili kuwa, lokacin da
mahaifin nasu ya umurce su da sakin
auren ‘ya’yan manzon Allah mata da
aka daura ma su sai Utba ya saki
Rukayya a mutunce. Shi kuma
wannan shakiyyin sai da ya zo ya
tozarta manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam sannan ya zartar da
muradin mahaifinsa ya shelanta sakin
Ummu-Kulthum. Ashe daman Allah
ya yi ma su zabin wani nagartaccen
bawa nasa shi ne Usmanu Dan Affan
wanda manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ya daura ma sa auren su
daya bayan daya. Sannan Allah ya yi
ma Utbah tukuicin cikawa da imani
shi da kannensa biyu; Mut’ib da
Durratu. Utaiba kuma Allah ya tozarta
shi ya yi mutuwar kaskanci a kan
kafirci.
Ya Allah muna rokon ka ka yi mana
arzikin gamawa lafiya da mutuwa
cikin masoyan manzonka masu kariya
ga addininsa da tafarkin shiriyarsa.
Leave a Reply