Mushrikai Sun Bullo Da Sabon Salo
Ganin duk irin matakin kuntatarwa,
takurarwa da azabtarwa ba su hana
musulmi riko kan-kam ga addininsu
ba, sai mushrikai suka sake dabara.
A yanzu sun yarda su hau teburin
sulhu da manzon Allah kuma suna
ganin da haka zasu yi galaba a kan
sa. Kwamitin dattawa ya shawarta
wanda ya kamata a tura ma sa, sai
aka yi matsaya a kan Utbatu dan
Rabi’ata ganin irin zalakar baki da
yake da ita. Ga kuma kwarjini da cika
fuska. Da Utbatu ya zo wurin manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam sai
ya fara da tambayar sa, shin
Muhammadu kai da uwayenka wane
ne ya fi? Domin mun san wadannan
ababen bautar namu su ma su suke
bauta ma. Ka fada mana kai ka fi
uwaye da kakanninka ne? Tsakanin
kai da Abdullahi wa ya fi wani? Ka fi
Abdulmuttalib ko ka fi Hashim?
Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ya yi shiru bai ce ma sa
kome ba. Sai ya ci gaba:
“Muhammadu, wallahi a tarihin kasar
nan ba mu taba ganin mutum
shu’umi irinka ba. Ka tarwatsa
haduwarmu, ka zagi addininmu, ka
tozarta mu a idon duniya. A yau ko
ina maganar ka ake yi; ana fadin
wani boka ya bayyana cikin Quraish,
wani dan dabo ya bullo a garin
Makka. A yanzu abu kadan ya rage ka
sa mu dauki takubba mu karkashe
kawunanmu”.
Duk abin nan da yake fadi manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yana
shiru bai ce yana sauraren sa.
Sannan sai ya ci gaba:
“Ya Muhammad! Ka fada mana idan
kana da bukatar kudi mu tara maka
abin da kowa bai da irin sa. Ko kana
sha’awar mata ne? Za mu sa ‘yan
matan gari su yi fareti ka zabi goma
da kake so mu aura maka su a huta.
Idan kuma ka san cewa, aljannu ne
suke damun ka sai ka fadi mu tashi
tsaye wajen nema maka magani”.
Sai da Utbatu ya dasa aya ya nunfasa
sannan sai manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam ya ce ma sa, Baban
Walidu ka kare? Ya ce ma sa eh,
bismillah, in ji daga gare ka.
Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam sai ya yi isti’aza ya fara
karanta ma sa Alkur’ani. Sai da ya
karanta ma sa ayoyi 13 na farkon
Suratu Fussilat har ya kawo in da
Allah yake cewa: “Idan sun kau da
kai to, ka ce na gargade ku a kan
wata babbar tsawa irin wadda ta ci
Adawa da Samudawa”. Suratu
Fussilat, aya ta 13. Sai Utbatu ya
zabura ya rufe bakin manzon Allah,
ya ce, tsaya! Haka ya isa. Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya
ce, to ka je kayi nazarin abin da ka ji.
Ai kuwa fitar sa ke da wuya ya nufaci
Quraishawa suka rantse da Allah
Utbatu ya canza, bai dawo da irin
fuskar da ya tafi ba. “Me ake ciki?”
Suka tambaye shi. Ya ce, ba komai.
Na je na same shi. “To, ya kuka yi?”.
Ya ce, wallahi na ji maganar da ban
taba jin irin ta ba. Ba waka ba ce, ba
sihiri ba, ba kuma bokanci ba.
Wallahi kul-ba-dade wannan
maganar tasa sai ta samu karbuwa.
Idan kuna bin shawarata ku fita batun
sa ga abin da ya sa gaba. Idan
duniya ta karbi sakonsa har ya
daukaka daukakar taku ce. In kuma
wani abu ya faru da shi shikenan,
Allah ya raka taki gona! Suka ce,
haba! Wallahi tun daga nesa mu mun
san ya sihirce ka. Utbatu ya ce ba
ruwana. Ku je ku yi yadda kuka ga
dama. As-Sirah An-Nabawiyyah, na
Ibn Hisham (1/294) da Al-Bidayah
Wan-Nihaya na Ibn Kathir (3/68-69).
Allah sarkin sarauta. Da Allah ya nufi
wannan taliki da shiriya wannan ita
ce babbar damar sa. Amma ita
shiriya rabo ce min-indillahi.
A cikin wannan labarin za mu ga irin
hakuri da juriyar manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam. Domin
duk abin da Utbah ya fadi na cin
zarafi da zargi, har da tuhumar sa da
ciwon aljanu bai fusata shi ba. A
cikin mutuntawa ya ce ma sa, “Baban
Walidu ka kare?”
Game da tambayar da ya yi kan
iyayensa kuma sai manzonmu ya
lizimci kawaici bai ce ma sa kome
ba. To, wane ne kuwa zai buda baki
ya ce ya fi iyayensa?! A maimakon
haka sai ya mayar da hankali ga isar
da sakonsa, in ya so shi ya yanke
hukunci da kansa idan wannan sako
ya ci karfin addinin iyaye ko ba haka
ba.
Game da ababen kwadaitarwa da ya
gitta ma manzon Allah kuwa, ba fa da
wasa yake yi ba. Iyakar gaskiyarsa
shi da sauran masu fada a ji a garin
Makka kenan. Da bukatarsa ta duniya
ce, zasu taru su biya ma sa ita.
Amma ina dan aiken Allah ina
waiwayar abin duniya! Sau da yawa
magadan annabawa – tun da su ba
ma’asumai ne ba – sukan fada a irin
wannan tarko na su Utbah. Da zaran
aka bai wa malami mukami, ko aka
bude ma sa hanyar samun kudi, sai
ya shiga sharholiyar jin dadi da aure-
aure da hawan manyan ababen hawa
da gina gidaje. Ta cikin wannan
kuma sai ya manta da fadin gaskiya,
da yakar zalunci, da isar da sakon
Allah. Idan aka yi barna sai ka gan
shi yana kame-kame da kanikanci
don ya gyara duniyar mabarnata. Idan
kuwa aka ce ma sa fadi gaskiya, da
ka kalli idonsa zaka ce, in baki ya ci
dole ne ido su ji kunya. A wasu
kasashen ma akan yi amfani da wasu
ayyuka na musulunci a zahiri a
shigar da malami a cikin su don
dauke hankalinsa daga tafarkin da ya
dauko na isar da sakon gaskiya.
Dole ne malamai magadan annabawa
su ci gaba da daukar izna a cikin
tarihin fiyayyen halitta. Ba kawai
karantawa da fatar baki ba, a’a. Dole
ne su sanya shi a gaba a matsayin
abin koyi. Su kuma tuna zancen
annabi Yusuf (A.S) da ya ce: “Ya
ubangijina! Hakika, zama gidan
kurkuku ya fi soyuwa a gare ni a kan
abin da suke kira na zuwa gare shi
(na alfasha). Allah muke roko ya
datar da mu. Fiqh As-Sirah An-
Nabawiyyah, na Munir Gadhban, shafi
na 169.
Har wayau a cikin tarihin da muka
gabatar mun ga tasirin Alkur’ani ga
zukata, da irin yadda gaskiya idan
aka shimfida ta take rufe karya. Irin
su Utbah su ne suka ga gaskiya
amma suka fandare ga barin ta.
Kuma suka yi tsayin daka ba za a isar
da ita a fili zuwa ga jama’a ba. Shi ya
sa a ranar Badar madaukakin sarki
duk ya share su, masu rabon shiriya
kuma sai ya bari suka ji sakon kuma
suka karbe shi.
Yanzu kam tun da na dawo daga
tafiya wannan darasi – in sha Allahu
– zai ci gaba.
Ya Allah! Ka yi mana rabon shiga
cikin masu imani, masu rikon
gaskiya.
Leave a Reply