Hudubar da muka gabatar a yau a masallacin Inwa Dutse Housing Estate Jigawa "Sharhin Hadisin Kada Ka Yi Fushi( Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺍﻟﻌﻠﻲ ﺍﻷﻋﻠﻰ ، ﺧﻠﻖ ﻓﺴﻮﻯ ، ﻭﻗﺪﺭ
ﻓﻬﺪﻯ ، ﺃﺣﺼﻰ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻌﺒﺎﺩ ﺃﻓﻌﺎﻟﻬﻢ ﻭﺃﻗﻮﺍﻟﻬﻢ ، ﻓﻲ
ﻛﺘﺎﺏ ﻻ ﻳﻀﻞ ﺭﺑﻲ ﻭﻻ ﻳﻨﺴﻰ ، ﺃﺣﻤﺪﻩ ﻭﺃﺗﻮﺏ
ﺇﻟﻴﻪ ، ﻟﻪ ﻣﺎ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﻤﻮﺍﺕ ﻭﻣﺎ ﻓﻲ ﺍﻷﺭﺽ ﻭﻣﺎ
ﺑﻴﻨﻬﻤﺎ ﻭﻣﺎ ﺗﺤﺖ ﺍﻟﺜﺮﻯ .
ﻭﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ ﺗﻘﺪﺱ
ﻭﺗﻌﺎﻟﻰ، ﺟﻠﺖ ﻋﻈﻤﺘﻪ ، ﻭﻋﻤﺖ ﻗﺪﺭﺗﻪ ، ﻭﺗﻤﺖ
ﻛﻠﻤﺘﻪ ﺻﺪﻗﺎً ﻭﻋﺪﻻً )) ﻭﺇﻥ ﺗﺠﻬﺮ ﺑﺎﻟﻘﻮﻝ ﻓﺈﻧﻪ ﻳﻌﻠﻢ
ﺍﻟﺴﺮ ﻭﺃﺧﻔﻰ (( .
ﻭﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻧﺒﻴﻨﺎ ﻣﺤﻤﺪﺍً ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ ، ﺻﻔﻴﺎً
ﻣﺠﺘﺒﻰ، ﺑﻌﺜﻪ ﺭﺑﻪ ﺑﺎﻟﺤﻖ ﻭﺍﻟﻬﺪﻯ ، ﻓﻤﺎ ﺿﻞ ﻭﻣﺎ
ﻏﻮﻯ ، ﻭﻣﺎ ﻧﻄﻖ ﻋﻦ ﺍﻟﻬﻮﻯ ، ﺇﻥ ﻫﻮ ﺇﻻ ﻭﺣﻲ
ﻳﻮﺣﻰ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺑﺎﺭﻙ ﻋﻠﻴﻪ ، ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺃﺯﻭﺍﺟﻪ
ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺨﻴﺮ ﻭﺍﻟﺘﻘﻰ ، ﻭﻋﻠﻰ ﺻﺤﺎﺑﺘﻪ ﻣﺼﺎﺑﻴﺢ
ﺍﻟﺪﺟﻰ ، ﻭﻧﺠﻮﻡ ﺍﻟﻬﺪﻯ ، ﻭﺍﻟﺘﺎﺑﻌﻴﻦ ﻟﻬﻢ ﺑﺈﺣﺴﺎﻥ
ﻓﻲ ﺍﻵﺧﺮﺓ ﻭﺍﻷﻭﻟﻰ . . . ﺃﻣﺎ ﺑﻌﺪ :
ﻓﺎﺗﻘﻮﺍ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻮﻥ ﺣﻖ ﺍﻟﺘﻘﻮﻯ ﻭﺍﺳﺘﻌﻴﻨﻮﺍ
ﺑﺎﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﻧﻴﻞ ﺍﻟﺮﺿﺎ ﻭﺍﻋﺒﺪﻭﻩ ﻭﻻ ﺗﺸﺮﻛﻮﺍ ﺑﻪ ﺷﻴﺌﺎً
ﻭﺍﺷﻜﺮﻭﻩ ﻛﻤﺎ ﻫﺪﺍﻛﻢ ﻭﺇﻥ ﻛﻨﺘﻢ ﻣﻦ ﻗﺒﻠﻪ ﻟﻤﻦ
ﺍﻟﻀﺎﻟﻴﻦ [ ﻳﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺁﻣﻨﻮﺍ ﺍﺗﻘﻮﺍ ﺍﻟﻠﻪ ﺣﻖ ﺗﻘﺎﺗﻪ
ﻭﻻ ﺗﻤﻮﺗﻦ ﺇﻻ ﻭﺃﻧﺘﻢ ﻣﺴﻠﻤﻮﻥ ] ﺛﻢ ﺃﻧﻲ ﺃﺣﺬﺭﻛﻢ ﻣﻦ
ﺷﺪﺓ ﺑﻄﺸﻪ ﻭﻋﻈﻴﻢ ﻋﻘﺎﺑﻪ ﻭﺃﻧﺬﺭﻛﻢ ﻣﻦ ﻳﻮﻡ ﻳﺸﻴﺐ
ﻟﻬﻮﻟﻪ ﺍﻟﻮﻟﺪﺍﻥ .
ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻮﻥ !
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
HADISIN “KADA KA YI FUSHI”
An gabatar da ita a ranar 22 ga
Shawwal 1431H
Godiya ta tabbata ga Allah Mahalicci
wanda ya sifaita kan sa da hakuri da
rangwame da yafewa. Na sheda babu
wanda ya cancanci bauta sai Allah.
Na shaida Muhammadu bawan Allah
ne kuma manzonsa. Allah ya aiko shi
don ya haskaka rayuwar ‘yan adam,
ya shiryar da su ga hanya mikakkiya.
Babu shakka Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wa Alihi Wasallam ya ida
manzanci ta hanyar maganarsa da
aikinsa, kuma aikinsa bai taba saba
ma zancensa ba. Allah ya yi tsira da
aminci ga wannan manzo zababbe da
iyalansa da sahabbansa baki daya.
Ya ku bayin Allah! Hudubarmu a yau
tana magana ne game da hadisin
sayyidina Abu Huraira Radiyallahu
Anhu wanda Imamul Bukhari ya
ruwaito shi a ingantaccen littafinsa
(Hadisi na 6116) inda ya ce, wani
mutum ya zo ya nemi shawarar
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa
Alihi Wasallam game da abin da zai
taimaka masa ga rayuwa. Sai Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam ya ce masa: “Kada kayi
fushi”. Shi kuma ya rinka maimaita
tambayarsa da neman shawararsa –
kamar yana ganin Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam
bai ba shi amsa ba. Sai Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam ya yi ta maimaita masa
wannan nasihar tasa yana cewa :
“Kada kayi fushi”.
Wannan hadisi Imamul Hakim ma ya
ruwaito shi a littafinsa Mustadrak
(3/713). Haka ma Ibnu Hibban a
Sahihinsa (12/501), da Baihaki a
cikin Sunan al-Kubra (10/105), da
Imamu Ahmad a cikin Musnad
(2/362), da Malik a cikin Muwadda
(2/905), da Dabarani a Mu’ujamul
Kabir (2/261) da dai sauran su.
Kuma dukkan su sun ruwaito shi ne
ta hanyar sayyidina Abu Huraira
Radiyallahu Anhu. A ruwayar Tirmidhi
(2020) sai da ya kara da cewa,
Manzon Allah ka nuna ma ni aikin da
zai shigar da ni aljanna, wanda kuma
zan iya kiyaye shi, amma kar ka
tsawaita. Sai Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wa Alihi Wasallam ya ba shi
wannan amsar. Ita kuma riwayar
Dabarani a cikin Mu’ujam al-Ausad
(2374) ta hikaito cewa, mai tambayar
Abud Darda’i ne Radiyallahu Anhu.
Malamai sun ambaci darussa da
dama a cikin wannan hadisi. Daga
ciki suka ce yana nuna:
1. Muhimmancin shawartar masana
da mutanen kirki.
2. Kuma ya nuna almajiri na iya
maimaita tambayarsa don neman
karin bayani.
3. Malami kuma ba dole ne sai ya
canza maganarsa ba idan ya san ita
ta dace don naci daga bangaren mai
tambaya.
4. Amsar da Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wa Alihi Wasallam ya bayar
kuma ta nuna yadda ya kamata mai
fatawa ya rinka la’kari da yanayin mai
tambaya domin ya ba shi amsar da
za ta dace da shi; ta amfane shi.
5. Kuma yana da kyau malamai su
zama masu hakuri ga ire-iren
tambayoyin mutane.
6. Fushi kuma dabi’a ce maras kyau
wadda shedan ya kan farauci dan
adam da sauki ta hanyar ta.
7. Dole ne mutum ya koyi kauce ma
abubuwan da ke fusata shi. Idan
kuma ya riga ya fusata to matsala ta
faru, domin shi fushi barawon
hankali ne.
8. Kuma wajibi ne mutum ya dauki
matakan da zasu hana fushin ya ja
ragamarsa.
9. Kamilin mutum shi ne wanda ya ke
iya kwankwade fushinsa; a gan shi
yana dariya a lokacin da ya fusata.
Idan so samu ne ma zai kyautata ma
wanda ya munana ma sa.
10. Haka kuma malamai suka ce
wannan ya nuna duk alheri na nan
tattare da hakuri kamar yadda duk
sharri ya tattara a fushi. Don haka
ma Ahnaf bin Kais ya ke cewa, ba a
gane na kwarai sai an fusatar da shi.
Shi kuma Ibnul Kayyim ya ce, fushi
naman dawa ne, da zaran ka sake shi
to, da kai zai fara. (Littafin Jami’ al-
Ulum Wal Hikam, na Ibnu Rajab
(2/16-17).
A cikin wannan huduba muna son mu
duba me yake jawo fushi? Sannan
wane irin hatsari yake da shi wanda
har ya sa Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wa Alihi Wasallam yake ta
maimaita ma wannan bawan Allah
cewa, kada ya yi fushi? Wadanne irin
hanyoyi ne wanda aka jarraba da
fushi zai bi don ya magance ma
kansa wannan matsala?
Fushi na daga abubuwa guda hudu
da ake son musulmi ya rinjayi kansa
idan sun same shi. Su ne: Tsoro da
Sha’awa da Kwadayi da kuma Fushi.
Fushi ya kasu kashi biyu ta fuskar
hukuncinsa a Shari’a. Akwai fushin
da Allah ke so, shi ne wanda aka yi
shi a sakamakon kishi don an keta
alfarmar musulunci ko an taka dokar
Allah, ko an yi zalunci ko cin mutunci
ko duk wani abin da bai dace ba a
cikin Shari’ar Allah. Irin wannan
fushin ne annabi Musa Alaihis Salam
ya yi a lokacin da ya karbo Attaura
daga wurin Allah amma ya isko
jama’arsa na bautar marakin zinari.
Amma duk da haka fushi bai bar shi
da hayyaci ba don sai da ya yi jifa da
alluna masu tsarki. Fushi na biyu shi
ne wanda mutum ya ke yi don an
taba shi. Wannan kuma shi ne wanda
uwarmu A’isha ta fadi Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam
bai taba yin sa ba. Yana yin fushi ne
kawai in an keta dokar Allah ko an
nemi sassafci ga wani hukuncin
Allah kamar yadda ya fusata da aka
nemi ya sauya hukuncin haddi a kan
wata mata mai daraja da tayi sata,
har ya ce: Na rantse da Allah, da
Fatima diyar Muhammadu Sallallahu
Alaihi Wa Alihi Wasallam ta yi sata da
na yanke hannunta. Ai wannan shi ya
bata al’ummomin da suka gabace ku.
Yana nufin tsaida doka da hukunci
kan talakawa a kyale manyan gari
(Sahihu Muslim, hadisi na 4410). Da
kuma irin fushin da ya yi lokacin da
ya ga hotuna a labulen dakinta (Ita
uwarmu A’isha Radiyallahu Anha) har
ya ce mata: Ba wanda zai sha azaba
a lahira kamar masu kwaikwayon
halittar Allah (Sahihu Muslim, hadisi
na 5527). Haka kuma lokacin da ya
ga wasu sahabbai suna jayayya a kan
sha’anin kaddara ya fusata kwarai da
gaske, har ya ce: Wannan shi ya
halaka al’ummomin baya. Musnad
Ahmad (2/178).
Ya ku ‘yan uwa musulmi! Abubuwan
da ke janyo fushi a cikin jama’a suna
da yawa. Watakila mafi girmansu a
rayuwarmu ta yau su ne wadanda
matsalolin rayuwar aure ke
haddasawa. An yi rikici a kan rashin
dadin abinci, ko cefane ba ya isa, ko
gida ba tsafta, ko mai gida yana kai
talatainin dare bai dawo ba, ko yana
wata dabi’a wadda matarsa ba ta so
kamar shan taba, ko maigida yana
matsantawa ba ya bari a je ziyarar
‘yan uwa, da dai wasu matsaloli
makamantan haka. Yau da gobe idan
rikici ya yi yawa sai Shaidanur Rajimi
ya samu kafa ta sanya kiyayya da
jiyewa da jin haushi da rashin
nasiha. Sai ka ga rayuwar ma’aurata
ta koma kamar ta abokan gaba. Daga
nan in ba a ci sa’a ba sai shaidan ya
tsaga gidan ya raba shi biyu ko ukku
ko fiye da haka.
Haka kuma daga cikin dalilan yawan
fushi a wajen jama’a akwai talauci.
Wani talakka duk mutane haushi suke
ba shi. In sun yi dariya sai ya ga
kamar izgili ne suke ma shi, in sun
gumde fuska kuma ya ce kyamarsa
su ke yi don yana talakka. Idan aka ci
rashin sa’a irin wannan mutum
matarsa na neman abinda ba ya da
shi, ko yaransa na bukatar abinda ya
fi karfinsa, to, a nan fa shaidan ya
samu wurin shan inwa, ba zai bar shi
ya huta ba dare da rana; tunani ya ke
ta yaya zai fita kunci da damuwa?
Watakila daga nan shaidan ya kawata
ma sa sha’awar abin wani, ya
mallake shi ta hanyar sata ko kwace
ko zamba.
Daga cikin dalilan yawan fushi a cikin
al’umma akwai bayyanar zalunci. Duk
mutumin da aka zalunta zai rinka
samun wata irin damuwa da jin
haushi ga wanda ya zalunce shi.
Wannan shi ya ke faruwa idan uba
yana zaluntar dansa, ko dan kasuwa
yana cutar makwaucinsa ko shugaba
yana sama da fadi da kayan na kasa
da shi. Daga nan zaka ga wanda aka
zalunta ya fara shirin kai hari ta irin
nasa hanyoyin da yake iyawa. Ba
kuma lalle ne shaidan ya bar shi ya
yi tunanin dacewar matakin da zai
dauka ko ya gano sharrin da matakin
zai iya haifarwa ba. Akwai sojoji da
dama da suka bindige masu
gidajensu har lahira saboda fushi a
kan sun zalunce su.
Haka kuma akwai ciwon hasada daga
cikin abubuwan da ke haifar da fushi
da bala’oin da ke biyowa bayan sa.
Wani kudin dan uwansa sun tsone
mai ido, wata kyawon kawarta na ba
ta haushi, ko tana kyashin ta fi ta
miji mai dadin zama. Wani mukamin
duniya yake gune ma, wani ilmin
wane ya ke ba shi takaici ko yawan
tarin jama’ar da ke son sa ko su ke
goyon bayan sa. Daga nan kuma
shaidan sai ya gwada ma sa ya zai yi
ya gusar da ni’imar Allah da ya yi ma
bawansa ko baiwarsa. Shi ba zai iya
ba, kuma ba zai fasa yin himmar yin
haka ba. Don haka babu dan wahala
a duniya kamar mai hasada. Akwai
kuma wasu dalilai ban da wadannan
da ke sa fushi kamar ji-da-kai,
yawan gardama, da sakin magana ba
kaidi da wasu mutane suke yi.
Fushi ba ya kawo alheri ko kadan.
Sau da yawa yake sa mai yin sa ya yi
da-na-sanin da bai karewa har
karshen rayuwarsa. Fada min ina
amfanin da-na-sani ga mutumen da
ya yi fushi da dansa ya rufe shi cikin
shago ba iska, ya tafiyarsa, koda ya
dawo ya isko dan nasa ya mutu don
babu iskar da zai shaka? Ko
mutumen da ya daure dansa tam-
tam-tam don ya yi masa laifi, daga
karshe hannu ya lalace har sai da
aka gunce! Kullum in ya kalli yaronsa
da gundulallen hannu wane irin da-
na-sani ya ke ji? Mutane nawa ne
suke da-na-sanin sun saki matansu,
iyayen diyansu, daga bisani Allah ya
dawo da so da kauna a tsakaninsu
bayan dama ta kubuce mu su, ko
kuma yaransu sun lalace don sun
rasa uwar da za ta dauke su ta kula
da su tsakani da Allah? Wasu ma –
tsakani da Allah – in ka ji dalilin
sakin matansu abin zai ba ka haushi,
ya ba ka takaici. Halin fusata kenan.
Wani Malami a Riyadh ya bada
labarin wata uwargida da ta kona
hannun mai aikin gidanta, wai don
tayi kure ta kone rigar maigida wajen
guga! Bayan ta gama duk zage-zage
da cin mutuncin da take mata, sai ta
jawo hannunta ta dora a kan dutsi ta
kone ta. Safiya ta yi, uwargida ta tafi
anguwa tana jiran ta dawo ta isko
mai aiki ta gama dahuwa, komi ya
kankama ayi kalaci a ba maigida,
ashe ke wannan baiwar Allah ke
kwana da kunar zuciya, kuma duk
dibarun duniya don fashe haushi da
ramuwar gayya sun kare, shawarar da
shedan ya samar a matsayin mafita
ita ce ta kulle gida, ta yi layya da dan
jaririn uwargida da ta bari yana
rarrafe, tayi ma uwargida ferfesu da
shi! Uwargida ta sha gara! To, amma
me ya biyo baya bayan ta san abinda
ya faru? Uwargida dai ta samu
tabuwar hankali, mai gida kuma ya
kamu da ciyon zuciya, ita mai aiki ba
a sake jin labarinta ba!!!.
Likitoci sun tabbatar da cewa, akwai
curutoci masu dinbin yawa wadanda
fushi ke haddasawa a sanadiyyar
karin bugun zuciya da ruwan
Adrenalin ke sabbabawa. Wadannan
ruwan suna dirowa ne daga wajen
gidibe idan mutum ya fusata sai su
gauraya da jini su sabbaba karin
bugun zuciya gwargwadon karfin
fushin da ya yi, har zuciyarsa ta kan
iya bugawa sau 150 a cikin dakika
daya maimakon bugu 72, sai jinin da
zuciya ke aika ma jiki ya zarce
mikidarin da ake bukata, shi ke sa
fuskarsa ta yi ja, jijiyoyinsa sun tashi
tsaitsaye, idanunsa sun kara fadi,
bakinsa na bari, jikinsa na makarkata.
Yawan fushi – in ji su likitoci – na
kawo ragewar karfin mazakuta a
wurin namiji da raunin matunta a
wajen macce saboda tasirin da fushi
ya ke da shi wajen hana zagayawar
jini a jikin mutum bisa tsarin da Allah
ya yi masa a tsawon lokacin fushin.
Kai har da ciwon shuga ma bincike
ya tabbatar da yawan fushi na haifar
da shi, saboda ruwan Adrenalin na
raunana karfin Insolin wanda
Pancreas ke furzowa don ya kone
shugan da ke cikin jikin mutum. Daga
nan in shuga ya tattara ya daddabe
bai kone ba sai wannan mugun ciwo
ya kama mutum. Allah ya kiyaye mu.
Yawan fushi kuma yana haddasa
curutocin da likitoci ba su gane kan
su, sai a yi ta yawon asibiti babu
amfani, damuwa ta kara shigar marar
lafiya, daga nan kuma sai ka ji ya
kamu da hawan jini. Wal iyazu billah.
Wani ikon Allah da ya kamata mu
sani shi ne, akwai bukatar wannan
ruwan Adrenalin a jikin dan Adam
amma karfin fushi na sa ya zo da
yawan da zai kawo cuta. Idan mutum
na mallakar kansa a lokacin da ya
fusata to, wannan ruwa zai digo
kadan yadda zai amfane shi. (Duba
Al Ghadab Wa Kaifa Alajahul Islam,
na Muhammad Mustafa al-Samri,
1418H da kuma Ilmun Nafs Fi
Hayatinal Yaumiyyah, na Dr.
Muhammad Usman Najati, shafi na
73).
Fushi ya kan mayar da mutum kamar
dabba, sai ka gan shi ba ya cikin
kwanciyar hankali, nan take ya yanke
ma kansa shawarar da ke ruguza
rayuwarsa, ko ya furta Kalmar da za
ta daure shi, ko ya bar wani
muhimmin abinda ke amfaninsa.
Kamar yadda yake sa zace-zace da
tuhumce-tuhumce wadanda ba su da
tushe, nan take sai wannan ya yi
tasiri ga kyawo da dadin
zamantakewarsa da mutane. Karamin
abu mai fushi kan fankama shi,
babban laifi (kamar wata mummunar
kalma ta zagi) sai fusatacce ya dauke
ta ba komi ba, da zaran ya huce sai
ya gane ya yi wauta, ko ya dawo da-
na-sanin da ba ya da amfani. Mu yi
tunanin abin da manzon tsira
Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam
yake cewa:
« ﻟﻴﺲ ﺍﻟﺸﺪﻳﺪ ﺑﺎﻟﺼﺮﻋﺔ، ﺇﻧﻤﺎ ﺍﻟﺸﺪﻳﺪ ﺍﻟﺬﻱ ﻳﻤﻠﻚ
ﻧﻔﺴﻪ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻐﻀﺐ« ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ 6114
ﻭﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ 2609
Sannan mu karanta Suratu Ali Imran:
133-134 da kuma Suratus Shura:
36-37.
Idan an jarrabe ka – ya kai dan uwa
musulmi – da ciwon fushi, to ga
maganinsa:
1. Yi kokari ka sa ma rayuwarka
cewa, fushi babban ciwo ne wanda
bai dace ka zauna da shi ba. Mataki
na farko kenan.
2. Ka dauki fushi a matsayin wani
abin sha da ya wajaba a hadiye shi
kamar yadda shan magani mai daci –
wani lokaci – yake zama wajibi. Idan
ka saba zaka rinka jin sa kamar
kankara a zuciyarka saboda sanyi.
3. Ka tuna ladar da Allah ya tanada
wa masu hakuri wadda ya ce ba ta da
lissafi, ga kuma Allah yana son masu
hakuri, yana tare da masu hakuri.
Masu hakuri har shelanta su ake yi a
filin alkiyama kuma Allah ba ya fushi
da su.
4. Fushi ya kan zo ne idan mutum ya
ji an kware shi ko an cuce shi. Ka
dauka cewa, rayuwa ba ta mikewa ba
a samu wata damuwa ba. Kuma
wanda ya cuta ma ka kansa ne ya
cuta ma domin sakamakon cutar
kansa za ta kare. Sannan ya saba ma
Allah idan ya cuce ka, to kai ma sai
ka biye ma sa duk ku saba ma Allah?
5. Ka yi tunanin hadarin fushi da
abubuwan da ya ke janyo ma ka. Ko
wadanda ya taba janyo maka a can
baya.
6. Duk abinda ka san yana fusata ka
yi kokari ka kauce ma sa. Don haka
ka daina tuna laifin da aka yi maka a
baya. Wannan ita ce fassarar da
wasu malamai suka yi ma wannan
hadisi na “Kada ka yi fushi”. Suka ce,
ai fushi dabi’a ce, mutum ba ya iya
hana kansa yin fushi, amma yana
kauce ma abubuwan da ke sa ya
fusata.
7. Idan ka ji fushi zai kama ka yi
sauri ka nemi tsarin Allah. Ka ce: ﭷ ﭸ
ﭹ ﭺ ﭻ
8. Idan ko har fushin ya riga ya kama
ka, to har yanzu akwai matakin da
zaka dauka. Yi sauri ka canza
yanayinka; idan kana tsaye ne sai ka
zauna. In ko kana zaune to, sai ka
kwanta.
9. Hanzarta kayi alwala, domin fushi
gobara ne ruwa ke maganin sa.
10. Idan ba a ci nasara ba har yanzu,
to ka fuskanci gabas ka yi sallah ko
da raka’a biyu, ka yi ta ambaton Allah
har zuwa wani lokaci. Babu yadda za
a yi musulmi ya dauki wadannan
matakai guda goma duk da haka ya
kasa rinjayar shaidan.
11. Kada ka yi magana a lokacin da
kake cikin fushi duk wada ta ke
kwantar ka. Musamman kuma addu’a,
domin in ka yi ta bisa ga lokacin
ijaba za a karbe ta kuma kayi da-na-
sanin ta. Kuma ka sani sau da yawa
shiru ya fi bada amsa ga wanda ya
fusata bisa ga yin magana.
12. Kada ka taba yarda ka dauki
kowane irin mataki a lokacin da kake
cikin fushi, duk yadda kake ganin ya
yi daidai, domin idan ka huce zaka
tabbata a zauce ka ke lokacin da
kake cikin fushin, ba cikakken hankali
kake da shi ba. Wannan ita ce
hikimar da ta sa Shari’a ta hana
alkali ya yanke hukunce idan yana
fusace, koda da nassi zai yi
hukuncin.
13. Idan imaninka ya kai, to yi kokari
ka kyautata ma wannan da ya fusata
ka, kana mai neman yardar Allah da
yin haka. Wannan shi ne ma’anar aya
ta 34 zuwa 35 a Suratu Fussilat.
Duk wadannan matakan Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam ya koyar da su a cikin
hadissai daban daban. Haka ma
aikinsa ya nuna cewa, shiriyar da ya
dora mu a kanta shi ne mutum na
farko da yake aiki da ita. Dubi yadda
wani bakauye ya riske shi ta baya, ya
ja rigarsa da karfi har ta shake mai
wuya, har ta yi shayi ga wuyansa. Da
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa
Alihi Wasallam ya juwo kuma a
husace sai bakauye ya ce, ka ba ni
cikin dukiyar Allah da ya ba ka! Sai
Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam
ya yi murmushi, nan take ya sa aka
kyautata ma sa. Wane ne a cikin
tarihi ya taba irin afuwar da
Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam
ya yi a lokacin da mutanen Makka
suka fado hannunsa ba su da wan
ceto ranar Fathu Makkah? Wannan
shi ne tafarkin annabawa. Dubi irin
ta’addancin da Annabin Allah Yusuf
Alaihis Salam ya gamu da shi. Da ya
samu dama kuma duba abinda ya ce
ma ‘yan uwansa da suka zalunce shi:
Babu laifi a kanku a yau, Allah zai
gafarta maku, kuma shi ne mafi
jinkan masu jinkai. Suratu Yusuf: 92.
Babu shakka wannan shi ya sa
tarihin magabata yake cike da irin
wannan yanayi na kyautatawa don
koyi da manzon rahama Sallallahu
Alaihi Wa Alihi Wasallam kamar
kissar da aka sani ta sayyidina Umar
Radiyallahu Anhu a lokacin da wani
bakauye ya zage shi, amma da Hurru
bin Kais ya karanta ma sa aya sai ya
tsaya kan ta. Da labarin Ali bin
Husain da kuyangarsa da ta zubar da
ruwan zafi a jikinsa amma ya diyauta
ta. Wani kuma ya zagi Ibnu Abbas
son ransa, sai da ya kare Ibnu Abbas
ya ce, kana da wata bukata mu yi
ma? Sai ya noke kai ya ji kunya.
Akwai wani sarki da ana iya cewa ya
fi kowa kai matuka ga bin wannan
tafarki a cikin abinda muka samu a
kundin tarihi. Wannan sarki shi ne
sayyidina Mu’awiyah dan Abu Sufyan,
yardar Allah ta tabbata a gare su. Ya
bayyana siyasarsa inda yake cewa:
“Na sanya wani zare tsakanina da
dukkan mutane. Sashensa yana a
hannuna, daya sashensa kuma yana
a hannunsu. Duk lokacin da na ga
sun ja, ni sai in sassauta. Idan kuwa
suka sassauta nasu sashen sai ni
kuma in dan ja da tsauri. Yana kuma
cewa: “Ba wani abin sha mai dadi da
ya kai magana mai zafi idan ka
hadiye ta don neman yardar Allah”.
Kuma yana cewa: “Ina daukaka kaina
daga barin wani laifi ya rinjayi
hakurina, ko wani rashin hankali ya
rinjayi hankalina, ko wata al’aura ta
rinjayi suturtawata, ko wata
munanawa ta rinjayi kyautatawata”.
Idan ka bi rayuwarsa a aikace a cikin
kundin tarihi za ka tabbata da gaske
yake wannan magana.
Ya kai dan uwa musulmi! Yana da
kyau ka gano cikin wani nau’i na
mutane kake. Domin kuwa, mutane
sun kasu kashi hudu dangane da
fushi. Na biyar dinsu shi ne wanda
ba a samu ba: Mai saurin fushi da
saurin hucewa, Mai nakin fushi mai
nakin hucewa, wadannan suna da
yawa kwarai a cikin mutane. Sai mai
saurin fushi mai nakin hucewa.
Wannan ya fi kowa yawan samun
matsala ga rayuwa. Na hudun shi ne
mai nakin fushi mai saurin hucewa.
Wadannan su ne kadan a cikin
mutane, kuma kamar haka ne dabi’ar
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa
Alihi Wasallam ta kasance. Na biyar
dinsu shi ne wanda ba ya fushi sam
sam. To, wannan ba mu ji labarinsa
ba tukuna, sai dai hikayoyi da ba za
a rasa ba kamar yadda aka ba da
labarin Ma’an bin Za’ida. In da za a
sami musulmi a haka, ya zan ba ya
fushi ko me aka yi har in an taba
addini ko an saba ma Allah to, da ba
ta zamo sifa ta kwarai a gare shi ba.
Muna iya lura cewa Allah Tabaraka
Wa Ta’ala ya sifaita kansa da yin
fushi ga kafirai da wasu masu laifi –
kamar masu kisan kai, kuma duk sifar
da Allah yake sifaituwa da ita to, idan
ana samun ta ga dan adam samun
nata ya fi zama kamala bisa ga
rashin ta. Bisa ga haka dole ne
musulmi su fusata ba idan an ci
mutuncin addini ko anyi wasa da
dokokinsa ko anyi izgili da littafin
Allah da makamantansu. A irin
wannan yanayi ma fusatar musulmi
da bayyana jin ciwonsu shi ke nuna
karfin imanin su. Sai dai a kowane
yanayi abinda ake bukata ga musulmi
ya sa natsuwa ga daukar matakin da
zai biya bukatarsa ba tare da ya yi
ma kansa wani dameji ba ko ya
samar da mikin da bai warkewa.
Ya ku ‘yan uwa musulmi! Mu yawaita
tuna nasihar Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wa Alihi Wasallam a gare mu,
ita ce: “Kada mu yi fushi”. A gaya ma
maigida da matarsa: “Kada kuyi
fushi”. A fada ma maigida da
lebaransa: “Kada kuyi fushi”. Haka
shi ma Malami da almajiransa: “Kada
kuyi fushi”. Sai kuma aboki da
abokinsa: “Kada kuyi fushi”.
Makwauci da makwaucinsa, dan
kasuwa da kwastomansa, officer da
yaransa, sarki da talakkansa.. Idan
mun bi wannan shawara ta Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam zamu samu rayuwa mai
ni’ima da ci gaba da nagarta. Mu
rinka lissafin kalmominmu kafin mu
fade su. Duk matakin da zamu dauka
mu fara auna shi da Shari’a, sannan
mu dubi akibarsa da abin da zai iya
jawowa. Mu tuna Allah ya kira mu ga
hakuri, ya kuma yi muna alkawali
babba idan mun amsa kira.
Ya Allah ka yi muna baiwa da hakuri,
ka sa mu cikin bayinka salihai
wadanda ke shan inuwar al’arshinka
ranar kiyama.
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺻﻞّ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺑﺎﺭﻙ ﻋﻠﻰ ﻋﺒﺪﻙ ﻭﺭﺳﻮﻟﻚ ﻧﺒﻴﻨﺎ
ﻣﺤﻤﺪ، ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺃﺯﻭﺍﺟﻪ، ﻭﺍﺭﺽ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻋﻦ
ﺻﺤﺎﺑﺘﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ ﻭﻋﻦ ﻭﺍﻟﺘﺎﺑﻌﻴﻦ ﻭﻣﻦ ﺗﺒﻌﻬﻢ
ﺑﺈﺣﺴﺎﻥ ﺇﻟﻰ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺪﻳﻦ ، ﻭﻋﻨﺎ ﻣﻌﻬﻢ ﺑﻌﻔﻮﻙ
ﻭﺟﻮﺩﻙ ﻭﺇﺣﺴﺎﻧﻚ ﻳﺎ ﺃﻛﺮﻡ ﺍﻷﻛﺮﻣﻴﻦ ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺃﻋﺰ
ﺍﻹﺳﻼﻡ ﻭﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ، ﻭﺃﺫﻝ ﺍﻟﺸﺮﻙ ﻭﺍﻟﻤﺸﺮﻛﻴﻦ،
ﻭﺍﺧﺬﻝ ﺍﻟﻄﻐﺎﺓ ﻭﺍﻟﻤﻼﺣﺪﺓ ﻭﺳﺎﺋﺮ ﺃﻋﺪﺍﺀ ﺍﻟﺪﻳﻦ ،
ﻭﺍﺟﻌﻞ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﺒﻠﺪ ﺁﻣﻨًﺎ ﻣﻄﻤﺌﻨًﺎ ﺳﺨﺎﺀً ﺭﺧﺎﺀً ﻭﺳﺎﺋﺮ
ﺑﻼﺩ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ،
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻧﺼﺮ ﺩﻳﻨﻚ ﻭﻛﺘﺎﺑﻚ ﻭﺳﻨﺔ ﻧﺒﻴﻚ ﻭﻋﺒﺎﺩﻙ
ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺃﻳﺪ ﺑﺎﻟﺤﻖ ﻭﺍﻟﺘﺴﺪﻳﺪ ﻭﺍﻟﻌﻮﻥ
ﻭﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ ﻋﻠﻤﺎﺀ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ، ﻭﺍﺣﻔﻈﻔﻬﻢ ﺑﺤﻔﻈﻚ،
ﻭﺍﻛﻸﻫﻢ ﺑﺮﻋﺎﻳﺘﻚ، ﻭﺭﺩ ﻋﻨﻬﻢ ﻛﻴﺪ ﻋﺪﻭﻙ ﻭﻋﺪﻭﻫﻢ
ﻳﺎ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ .
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﺟﻌﻠﻬﻢ ﻧﺼﺮﺓ ﻷﻭﻟﻴﺎﺋﻚ ﻭﺍﺟﻤﻊ ﺑﻬﻢ ﻛﻠﻤﺔ
ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺤﻖ ﻭﺍﻟﻬﺪﻯ ﻳﺎ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ .
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺃﺑﺮﻡ ﻷﻣﺔ ﺍﻹﺳﻼﻡ ﺃﻣﺮ ﺭﺷﺪ ﻳﻌﺰ ﻓﻴﻪ ﺃﻫﻞ
ﺍﻟﻄﺎﻋﺔ، ﻭﻳﺬﻝ ﻓﻴﻪ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﻤﻌﺼﻴﺔ، ﻭﻳﺆﻣﺮ ﻓﻴﻪ
ﺑﺎﻟﻤﻌﺮﻭﻑ ، ﻭﻳﻨﻬﻰ ﻓﻴﻪ ﻋﻦ ﺍﻟﻤﻨﻜﺮ، ﺇﻧﻚ ﻋﻠﻰ
ﺳﻤﻴﻊ ﺍﻟﺪﻋﺎﺀ .
” ﺭﺑﻨﺎ ﺁﺗﻨﺎ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﺣﺴﻨﺔ ﻭﻓﻲ ﺍﻵﺧﺮﺓ ﺣﺴﻨﺔ ﻭﻗﻨﺎ
ﻋﺬﺍﺏ ﺍﻟﻨﺎﺭ ” ﺳُﺒْﺤَﺎﻥَ ﺭَﺑِّﻚَ ﺭَﺏِّ ﺍﻟْﻌِﺰَّﺓِ ﻋَﻤَّﺎ ﻳَﺼِﻔُﻮﻥَ
* ﻭَﺳَﻼﻡٌ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟْﻤُﺮْﺳَﻠِﻴﻦَ * ﻭَﺍﻟْﺤَﻤْﺪُ ﻟِﻠَّﻪِ ﺭَﺏِّ
ﺍﻟْﻌَﺎﻟَﻤِﻴﻦَ .

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates