Kaffarar Rantsuwa

Danna nan domin shiga karatu Online

Tambaya: Yaya akeyin kaffarar rantsuwa?

Amsa: Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.

Da farko ya kamata mu sani cewa Rantsuwa ya rabu kashi uku. Akwai wanda ake masa kaffara, akwai kuma wanda ba’ayi masa komai.

Na farko: Yasasshen Rantsuwa; shine kaman rantsuwa da mutum zaiyi ba tare da ya ƙulla a zuciyarsa ba. Misali a tambayeshi wani abu sai yace: Eh wallahi, ko A’a Wallahi, wannan irin rantse rantsen bashi da kyau. Amma mutum ba zaiyi kaffara a kansu ba.

Na biyu: Rantsuwar ƙarya(Aimanul Gamus): Shine mutum ya rantse a kan ƙarya. Wannan shima babban laifi ne amma babu kaffara akansa.

Na uku: Rantsuwa da aka ƙulla; Shine mutum ya ƙulla abu a zuciyarsa sannnan ya rantse. Misali yace: Wallahi bazan yi kaza ba. Ko wallahi zanyi kaza. Kuma mutum yazo baiyi ba, to wannan akwai kaffara akansa. Amma wasu maluman suna ga cewa idan Mutum ya katange ranstuwan da Insha’Allah to babu kaffara akansa. Misali Mutum yace: Wallahi bazan yi kaza ba Insha’Allah. Ko wallahi zanyi kaza Insha’Allah.

Yaya ake Kaffarar Ranstuwa?

  • Ciyar da Miskinai goma: Za’a baiwa kowani miskini rabin sa’i. Ko kilo ɗaya da rabi. Ko a dafa abinci a baiwa ko wani miskini daidai inda zai ishe shi.
  • Tufatar da Miskinai goma: za’a tufatar da miskinai goma. Kowa za’a bashi tufar da zata ishe shi yin Sallah aciki.
  • Ƴanta Bawa ko baiwa Mumina: Na uku shine ƴanta baiwa ko bawa mumini.

I dan Mutum bai samu daman yin wa’innan abubuwa ba sai yayi na huɗu. Shine:

  • Yin Azumin kwana uku a jere: Wannan shine kaffarar Rantsuwa na ƙarshe ga wanda bai samu abubuwan da suka gabata ba.

Sannan Jumhurin Maluma sun tafi kan cewa baya wadatar wa a cire Kuɗi a matsayin kaffarar rantsuwa. Misali mutum ya lissafa nawa ne Kuɗin ciyar da miskinai goma sai ya cire ƙimar kuɗin ya bada shi sadaƙa, wannan bai yi ba.

Ibnu Qudama Allah yayi masa Rahama yace:

Baya wadatar wa a cire ƙimar kuɗin ciyar wa ko tufatar wa a kaffarar rantsuwa, domin Allah ya ambaci abinci ne, saboda haka yin kaffara da waninsa ba zai wadatar ba. Kuma domin Allah ya bada zaɓi ne tsaƙanin abubuwa guda uku, da ace ya halatta ayi amfani da kuɗi wurin yin kaffara da Allah bai taƙaita kan wa’innan abubuwa guda uku ba.

Almugni:11/256

Sheikh Bin Baz Allah yayi masa Rahama yace:

Kaffarar da za’a bayar ya zama abinci ba kuɗi ba, domin wannan shine abinda yazo acikin Alqur’ani da Sunnah,

Fatawa Islamiyya: 3/481

Sheikh Bin Uthaymeen Allah yayi Masa Rahama yace:

Idan Mutum bai samu bawa ko baiwa ba, bai samu kayan da zai tufatar ba, bai samu abinci da zai ciyar ba to zaiyi azumi uku a jere

Fatawa Manaril Islam: 3/667

A Taƙaice

Wanda yayi Rantsuwa zai aikata wani abu, kuma ya ƙulla a zuciyarsa, ko yayi Rantsuwa ba zaiyi abu ba to ya Wajaba a gareshi yayi Kaffara. Kaffarar kuwa shine: Ciyar da miskinai goma, ko tufatar dasu, ko ƴanta bawa ko baiwa. Wanda kuma bai samu wannan ba duka to sai yayi Azumin kwana uku a jere.

Allah shine mafi sani.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates