ALKAKI DA RUWAN ZUMA 37(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

ALKAKI DA RUWAN ZUMA
Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam
Fitowa Ta 37
Daga Cikin Fifikonsa
4. Darajar Sahabbansa (kashi na uku)
Wasu Darajoji da Allah ya Kebanci Wasu Daga Cikin Daidaikunsu Da Su:
1. Akwai wanda mala’ika Jibril (AS) yake saukowa a cikin siffarsa. Shi ne jekadan manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Dihyah bn Khalifa Al-Kalbi
2. Sai wacce Allah ya daura aurenta a sama. Ita ce, Zainab bint Jahsh.
((فلما قضى زيد منها وطرا زوجناكها))
3. Akwai wanda Allah ya kira shi abokin manzon Allah. Shi ne Abubakar Siddiq. Suratut Taubah: 40.
((إذ يقول لصاحبه لا تحزن..))
4. Akwai wanda ya sha nono tare da manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, uwa daya ta yi renon su. Shi ne Usman bn Maz’un.
5. Akwai wadanda suka limanci manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam a sallah. Su ne Abubakar Siddiq da Abdurrahman bn Auf.
6. Akwai wanda ya yi aiki da wata aya shi kadai kafin a shafe hukuncinta. Shi ne Ali bn Abi Talib.
7. Akwai sahabin da manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce Allah ya yi magana da shi gaba da gaba. Shi ne Abdullahi bn Haraam mahaifin Jabir.
8. Akwai cikin su wanda Mala’iku suka gaisa da shi; suka yi ma sa sallama. Shi ne Imran bn Husain.
9. Akwai kuma wanda manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce Mala’iku suna jin nauyin sa. Shi ne surukinsa Usman bn Affan.
10. Sai wanda Mala’iku suka yi ma sa wankan janaba bayan ya yi shahada yana dauke da ita. Shi ne Hanzalah bn Abi Amir.
11. Akwai wanda manzon Allah ya ce, al’arshin Ubangiji mai rahama ya girgiza saboda mutuwarsa. Shi ne Sa’ad bn Mu’az.
12. Akwai wanda manzon Allah ya ce, Allah ya sanya ma sa fukafukai biyu cikin aljanna. Shi ne Ja’afar bn Abi Talib.
13. Akwai wanda manzon Allah ya ce, ya ji sawun tafiyarsa cikin aljanna. Shi ne Bilal bn Rabah.
14. Akwai wanda manzon Allah ya fanshe shi da iyayensa. Shi ne Sa’ad bn Abi Waqqas.
15. Akwai manzon Allah ya ce, shi ne sakataren wannan al’umma: Abu Ubaida bn Jarrah.
16. Akwai manzon Allah ya ce, su ne shugabannin matasan aljanna: Al-Hasan da Al-Husain ‘ya’yan Ali.
17. Akwai wanda yawun manzon Allah ne suka fara shiga cikinsa tun zuwan sa duniya. Shi ne: Abdullah bn Zubair.
18. Akwai wanda Allah ya fadi sunansa karara cikin Alkur’ani. Shi ne Zaid bn Haritha.
((فلما قضى زيد منها وطرا زوجناكها))
Suratul Ahzab: 37
19. Akwai wanda Allah ya fadi imaninsa a cikin Alkur’ani. Shi ne Abdullahi bn Salam.
((وشهد شاهد من بني إسرائيل على مثله فآمن واستكبرتم..)) سورة الأحقاف: ١٠
Suratul Ahqaf: 10
20. Akwai manzon Allah ya ce, wanda zai shiga aljanna babu hisabi. Shi ne Ukasha bn Muhsan.
21. Akwai wanda manzon Allah ya ce, Allah yake ma sa ilhami. Shi ne Umar bn Khattab.
22. Akwai wanda manzon Allah ya ce, shi ne shugaban makarantan Kur’ani na wannan al’umma: Ubayyu bn Ka’ab.
23. Akwai wanda ya karanta ma manzon Allah Alkur’ani bisa ga umurninsa. Manzon Allah ya saurare shi har ya yi kuka. Shi ne Abdullahi bn Mas’ud.
24. Akwai wanda manzon Allah ya tsaya bayan gidansa yana sauraren karatunsa. Shi ne Abu Musa Al-Ash’ari.
25. Akwai wanda manzon Allah ya dauki shawararsa a yakin Hunain. Shi ne Al-Hubab bn al-Mundhir.
26. Akwai kuma wanda manzon Allah (S) ya karbi shawararsa a Khandaq. Shi ne Salman al-Farisi.
27. Akwai wanda yake abokin sirrin manzon Allah ne. Shi ne Huzaifa bn Al-Yaman.
28. Akwai wanda manzon Allah ya amince ma sa a kan iyalansa. Shi ne Abdurrahman bn Auf.
29. Akwai wanda manzon Allah ya ce, shi ne ya fi kowa sanin ilimin halal da haram a cikin wannan al’umma. Shi ne Mu’az bn Jabal.
30. Akwai shugabar matan aljanna. Kamar yadda manzon Allah ya fadi. Ita ce ‘yarsa Nana Fatima.
31. Akwai wacce Allah ya gina ma ta gida a cikin aljanna. Kuma ya ce manzon Allah ya yi ma ta bushara. Ita ce uwargidansa Nana Khadija.
32. Akwai kuma wacce manzon Allah (S) ya ce ya shiga aljanna sai ya gan ta a ciki. Ita ce Rumaisa’u bint Malhan.
33. A cikin su akwai wacce manzon Allah (S) ya ce, ta yi tuban da, da an raba shi ga mutane 70 daga cikin mutanen Madina ya ishe su.
Akwai kuma jekadun manzon Allah da wakilanci da marubutanshi da wanzamanshi da ladananshi dss dss.
Dan uwa, dubi yadda Allah ya daukaka wadannan bayi nasa, ya fifita su da darajoji iri iri kowacce kana sha’awar ace kai ne ka same ta, amma sai ‘yan Shi’a suka sanya wariya a tsakanin su; su yaba ma wannan, su kushe ma wannan. Suka kago labarai marasa tushe da inganci suka jingina ma su suna yaudarar jahilai da su. Ya Allah! Muna godiya gare ka da ka ba mu hasken sanin littafinka, muka gano matsayin wadannan mutane da ka zaba daga cikin maganarka. Muka so su, muka kaunace su, muka yi uzuri ga wadanda ka jarabce su daga cikin su. Muka ce ma su gaba daya “Radhiyallahu anhum” kamar yadda ka ce ma su. Allah! Muna tawassuli da imanin da muka yi da Alkur’ani ka shiryi masu tsarkin zuciya daga cikin yan uwanmu wadanda wancan santsi ya kwashe su, ka hade mu da su gaba daya a tafarkin gaskiya don mu hadu a cikin rahamarka. Ya Allah! Kai mi ji ne, mai karbawa.
Zamu rufe wannan magana da kalaman sayyidi Abdulqadir Aljailani jikan sayyidi Al-Hasan dan Ali dan abu Talib yardar Allah ta tabbata a gare su a cikin littafinsa “Al-Gunya Li Talibi Tariq Al-Haqq” (ma’anar sunan littafin JAGORAN MASU NEMAN GASKIYA”. Ga abin da ya ce:
“Kuma Ahlus Sunnah sun hadu a kan wajabcin kamewa daga abin da ya gudana a tsakanin su, da barin fadin kurakuransu, da bayyana kyawawan ayyukansu da darajojinsu, da barin lamarinsu ga Allah madaukakin sarki, tare da duk abin da ya faru a tsakaninsu na sabani tsakanin Ali da Dalha da Zubair da Nana A’isha da Mu’awiyah, yardar Allah ta tabbata a gare su gaba daya bisa bayanin da muka gabatar. Kuma wajibi ne a bai wa kowane mai girma girmansa kamar yadda Allah buwayayyen sarki ya ce:
“Kuma wadanda suka zo bayan su suna cewa, ya Ubangijinmu! Ka yi gafara gare mu da kuma ga wadanda suka riga mu yin imani, kuma kada ka sanya jin haushi a cikin zukatanmu ga wadanda suka yi imani. Ya Ubangijinmu! Hakika kai mai jinkai ne, mai tausayi”
Kuma ya ce:
“Waccan al’umma ce da ta shude, abin da suka aikata nasu ne, wanda kuka aikata ku ma naku ne, kuma ba za a tambaye ku game da abin da suka kasance suna aikatawa ba”.p
Kuma manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce: “Idan aka ambaci sahabbaina ku kame bakinku”.
A wani lafazin cewa ya yi: “Ku yi hattara da fadin abin da ya gudana tsakanin sahabbaina, domin da dayanku ya yi sadakar kimanin dutsen Uhud na zinari ba zai kai mudun dayansu ko rabinsa ba”.
Sannan ya ci gaba da kawo hadisai masu tarin yawa a kan darajojinsu.
Duba littafinsa: “Al-Gunya Li Talibi Tariq Al-Haqq”, bugun Kamfanin mustafa Al-Babi na kasar Masar, shafi na 79.
Ya Allah ka isar da rahamarka da jinkayinka da kyautatawarka zuwa ga kabarin sayyidi Abdulqadir Al-Jailani, ka yi jagora ga mabiyansa zuwa ga hanyar gaskiya.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates