ALKAKI DA RUWAN ZUMA(Dr. Mansur Sokoto)

·

·

ALKAKI DA RUWAN ZUMA
Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta
Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi
Wasallam
Fitowa ta 9
Me Ya Sa Aka Zabi Yankin
Larabawa?
3. Akwai yanayin kasar larabawan ita
kanta wadda ta fado a tsakiyar duniya
mai dauke da mutane a wancan lokaci.
Don haka yaduwar musulunci zuwa
sauran sassan duniya zai fi sauki a can
bisa ga ko ina daga sauran kasashe.
4. In ka hada wannan da kasancewar
daman can akwai dakin Allah na farko
a garin Makka, wanda kuma wadannan
bayin Allah suke girmama shi matuka
har ba sa bari ayi kowane irin fada ko
tashin hankali a kewayensa.
5. Ga kuma su larabawan suna rike da
sauran addinin annabi Ibrahim (AS)
duk da shigar da maguzanci da suka yi
a cikin sa. Misali, suna wankan janaba,
suna jana’iza, suna dawafi, suna azumi
a ranar Ashura. Idan kuma ka kalli
yanayinsu a auratayya da hukuncin
shika (saki) da idda da diyya dss zaka
san lalle suna da sauran abinda ya rage
ma su na addinin gaskiya. Daga cikin
abinda suke a kan sa na addinin annabi
Ibrahim (AS) akwai aikin Hajji da
Umra – ko da kuwa sun yi dawafi
tsirara a wasu lokuta. Ko da kuma
Quraishawa sun ki fita Arafat don ji-ji-
da-kai.
To, ka ga bayyanar musulunci a
wannan wurin a gyara kurakuransu ya
fi tasowar sa daga wani wuri inda za a
koya ma mutane sabon addinin da ba
su san makamarsa ba.
Mu kwana a nan. Gobe in Allah ya so
sai mu dora.

One response to “ALKAKI DA RUWAN ZUMA(Dr. Mansur Sokoto)”
  1. Sulaiman Avatar

    Allah ya kara wa malam lfy.

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: