ALKAKI DA RUWAN ZUMA(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

ALKAKI DA RUWAN ZUMA
Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta
Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi
Wasallam 7
Me Ya Sa Aka Zabi Yankin
Larabawa?
Duk abin da Allah madaukaki ya yi ba
zai rasa wata gwaninta ba ko kuma
wata hikimar da take tattare da shi. Ko
dai mu bil adama mu gano haka ko
kuma basirarmu ta kasa ganewa.
Amma game da lamarin fitar da
manzanci daga yankin larabawa
hikimar a fili take, ba ta ko bukatar
wani dogon tunani. Muna iya lura da
wadannan dalilai kamar haka:
1. Duk da yake duniyar duka ta rikice,
babu wasu jama’a da suke kusa da
fitira; tsarin halittar Allah ga dan Adam
kamar su larabawa. Ina nufin su
mutane ne masu kama da farar takarda
wacce take jiran a rubuta duk abin da
aka ga dama a kan ta. Su dai sun yarda
ba su sani ba, kuma suna neman a
sanar da su. Ba zaka hada su da
wadanda ke ganin suna kan wani ilimi
ba kuma suna jayayya akan sa alhalin
ilimin na jabu ne.
2. Dalili na biyu shi ne irin kyawawan
dabi’unsu da suka zarce na sauran
mutanen wancan lokaci. Domin kuwa
duk da kasancewar su ma’abota shan
giya da caca da sauransu, amma suna
da karimci matuka. Balarabe kan iya
shiga kowace irin wahala don tara abin
duniya, amma bai taba jin wahalar fitar
da shi ya yi kyauta ko ya yi taimako in
dai za a yabe shi ko da a bayan
mutuwarsa. Wannan ya sa sahabbai ba
su samu damuwa ba sam wajen
taimakon musulunci da dukiyarsu tun
da yake daman halinsu ne da suka
saba.
Sa’annan suna da kunya da sadaukar da
kai da jarunta. Al-Alusi ya kawo
labarai daban daban a kan
sadaukantaka da jarunta da karimcin
larabawa a cikin littafinsa “Bulug Al-
Arab Fi Ma’arifati Ahwal Al-Arab” a
juz”i na daya sai a duba shi. Sa’annan
mutane ne masu kaifi daya; ba sa
karya. Ga kuma tsananin cika alkawali.
Labarin Harith dan Abbad jagoran
kabilar Bakr lokacin da suka yaki
Taglibawa ya ishe mu misali.
Ku dakaci wannan labari.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates