ALKAKI DA RUWAN ZUMA(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

ALKAKI DA RUWAN ZUMA
Ingantaccen Tarihin Sayyadi
Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam
6
Muhammadu Zaben Allah
A daidai wannan lokacin da muke
magana a kan sa labari ya fara game
kasashen larabawa cewa, wani annabi
ya kusa bayyana wanda zai ceto
mutane daga halin la-haula da suka
shiga cikinsa. Don haka, sai aka samu
wasu bayin Allah suna gurin cimma
wannan matsayi kuma har suna
yunkurin kiran mutane zuwa ga gyara.
Daga cikin su akwai Umayyah bin
Abis Salt wanda annabi Sallallahu
Alaihi Wasallam ya ce kadan ya rage
ya musulunta saboda irin kalaman
tauhidi da kushe shirka da ke fita
bakinsa. (Sahih Muslim 7/49). Akwai
kuma Amru bin Nufail wanda ya rinka
hana mutane rufe ‘ya’yansu mata suna
ji suna gani da rayuwarsu. Akwai
Qussu bin Sa’idah wanda aka ce
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ya saurari jawabinsa a
kasuwar baje kolin fasaha da ake yi
shekara shekara a Ukaza.
Duka wadannan kowanen su ya yi fatar
kasancewa shi ne manzon karshe da
Allah zai aiko. Wannan daga bangaren
larabawa kenan. To, su kuma
Yahudawa, musamman mazauna
Madina daga cikin su, su ma sun yi
wannan hasashen na bayyanar sabon
manzo dogaro da abin da suke
karantawa a cikin At-Taurah. To,
amma fa a zatonsu lalle ne wannan
annabi ya bayyana daga cikin su tunda
yake tun bayan wucewar annabi
Ibrahim Alaihis Salam babu wani
annabi da aka taba aikowa wanda ba
dan gidansu ba. To, sai dai kamar
yadda bahaushe ke cewa, ana zaton
wuta a makera sai ta bulla a masaka. A
wannan karon madaukakin sarki ya
kauce ma gidan Banu Isra’ila zuwa
gidan ‘ya’yan baffansu Banu Isma’ila.
Daga cikin wannan tsarkakakkiyar
zuri’a ta Isma’ila ne Allah ya zabi gidan
Kinanata. Daga zuri’ansa sai ya zabi
Quraishawa. Daga cikin su kuma ya
zabi Banu Hashim. A cikinsu ne
gwanin sarki Allah ya zabo fiyayyen
halitta, shi ne Muhammad dan
Abdullahi Sallallahu Alaihi Wasallam,
bawan Allan da bai taba mafarkin
samun wannan matsayin ba duk da
yake shi ne ya cancance shi. Allah
Tabaraka Wa Ta’ala yana cewa:
(( ﻭﻣﺎ ﻛﻨﺖ ﺗﺮﺟﻮ ﺃﻥ ﻳﻠﻘﻰ ﺇﻟﻴﻚ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﺇﻻ ﺭﺣﻤﺔ
ﻣﻦ ﺭﺑﻚ، ﻓﻼ ﺗﻜﻮﻧﻦ ﻇﻬﻴﺮﺍ ﻟﻠﻜﺎﻓﺮﻳﻦ))
Ma’ana: “Ba ka kasance kana
tsammanin a aiko ma ka wannan
littafin ba, sai dai jinkayi ne kawai
daga ubangijinka. Don haka kada ka
zama mai goyon bayan kafirai”.
Suratul Ankabut: 86.
Kuma yana cewa:
(( ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻋﻠﻢ ﺣﻴﺚ ﻳﺠﻌﻞ ﺭﺳﺎﻟﺘﻪ))
Ma’ana: “Allah shi ne wanda ya fi
sanin a ina ne ya ke sanya sakonsa”
suratul An’am: 124.
To, da yake a can baya mun yi
maganar halin da duniya take ciki na
jahilci da son zuciya, tambayar da ya
kamata mu mayar da hankali gare ta ita
ce, me ya sa addini ya bulla a yankin
larabawa?! Ko kuma mu ce, me ya sa
Allah ya zabi labarawa da wannan
alheri?
Amsar wannan tambaya sai darasi na
gaba in Allah ya yarda.
Da fatar an sha ruwa lafiya.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates