ALKAKI DA RUWAN ZUMA(Dr. Mansur Sokoto)

·

·

ALKAKI DA RUWAN ZUMA
Ingantaccen Tarihin Sayyadi
Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam
4
Kasashen Da Ke Akwai Kafin Zuwan
Manzon Allah (S)
3. Qasashen Turawa
Ban da wadancan kasashe da muka
fada a baya akwai kasashen turawa da
kuma Japan, da kasar Sin, da Indiya.
Su kuma wadannan kasashen
rayuwarsu ta fi kama da ta dabbobin
dawa a wancan lokaci. Ba abin da ba
sa bauta ma, tun daga rana da wata da
ruwa da taurari har su shanu da
makamantansu. Kai, har Farji ma
akwai masu bauta a cikin su. Wai,
saboda shi ne mafitar kowa, don haka
shi ne Allan! Babu kasuwar da ke ci a
cikin su sai ta almara da tatsuniya.
Kuma dukkan su sun yi imani cewa, ba
a tashin kiyama. Amma sun yi amanna
cewa, duk wanda ya mutu zai sake
dawowa duniya a wata sifa daban ba ta
mutum ba. Ya’allah ko kare ko biri ko
mage ko wani abu daban.
4. Sai kuma Yahudawa wadanda suka
yi kaka-gida musamman a kasar Sham
(Syria) da Iraqi da kuma Hijaz (yankin
da Saudia take ciki a yau). Su ma dai
kamar Nasara sun dade da canja
addininsu. Kuma sun musanya littafin
da Allah ya saukar ma Annabi Musa
(AS) da wasu surori da suka kago suna
karantawa, inda suka mayar da Allah a
matsayin ubangijinsu su kaxai ba da
sauran mutane ba. Suna da wani littafi
da suka kira “Talmud” wanda suka
fifita shi a kan At-Taurah. A cikin sa
sun zava ma kansu irin rayuwar da
suke ganin ta dace da su a matsayin
zababbun bayi wadanda Allah ya yi
kowa don ya bauta masu. Haka kuma
sun kitsa labarai iri daban daban na cin
mutuncin annabawa da manzannin da
Allah ya aiko ma su. Sa’annan sun yi
fice wajen cin rashawa da algussu
wajen sana’a da kuma kudi da ruwa.
Zamu ci gaba in Allah ya so.
Zamu daina amfani da (Q,V,X)
wadanda mun sa su ne don masu
amfani da font na Rabi’at Muhammad
wanda yake ba da haruffan Hausa
masu lankwasa.
Ku dakace mu.

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: