ALKAKI DA RUWAN ZUMA(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

ALKAKI DA RUWAN ZUMA
Ingantaccen Tarihin Sayyadi
Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam 5
Kasashen Da Suka Kafu Kafin Zuwan
Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam
5. Sai kuma larabawa kasashen
wadanda su suke a tsallaken tekun
Fasha. Su kuma sun dauka cewa
addinin annabi Ibrahim Alaihis Salam
suke a kan sa. Kuma haka abin yake
can da farko. Amma daga bisani wani
basarake daga kabilar Khuza’ah* ana
ce ma sa Amru dan Luhayyu ya yi
wata tafiya a yankin Balqa’a ta cikin
kasar Jordan don neman magani, sai ya
ga mutanen kasar sun dukufa ga bautar
gumaka. Daga nan shi ma ya nemi a ba
shi izni inda ya zo da gunkin “Hubal”
suka fara bautar sa. (Al-Asnam, na
Ibnul Kalbi, shafi na 6).
* (Khuza’ah su ne kabilar da suka kori
Jurhumawa – wadanda suka kafa garin
Makka – daga cikin ta, suka kuma
shigo da bautar gumaka. Daga baya
Allah ya kawo dangin annabinsa a
zamanin Qusayyu suka karbi ragamar
tafi da garin na Makka, suka raya shi,
kuma suka kula sosai da masu zuwa
aikin Hajji)
Daga nan kuma abin ya ci gaba har aka
samar da gumaka da yawa, ta yadda
kowace kabila ta yi nata gunki, ko
wace zuri’a tana da nata. Kai, duk ma
wani dutse sai da ya zamo ma su abin
bauta. Aka cika dakin Allah makil da
gumaka wadanda adadinsu ya kai
gunki dari uku da sittin (360). Ba kuma
abinda za su yi sai sun nemi iznin
gumakan nan ta hanyar yin kuri’a a
gaban su. Wani dalili kuma da ya
karfafi bautar gumaka a wajen
mutanen Makka shi ne wata bidi’a da
suka kago ma kansu wacce Ibnul Kalbi
ya ruwaito mana inda yake cewa:
“Mutanen Makka sun kasance duk
wanda zai yi tafiya a cikin su saboda
girmama Haramin Makka sai ya nemi
wani dutse daga cikin birnin ya yi
tafiya da shi. Duk kuwa inda ya sauka
sai ya kafa shi ya rinka zagayar sa
kamar yadda ake dawafin Ka’aba”.
Daga kan wannan bidi’ar ne shedan ya
ja su zuwa bautar duwatsu. Wal iyadhu
billah. (Al- Asnam, shafi na 8.
Wani abin da yake da muhimmanci a
sani shi ne cewa, larabawa da suka
shigo da bautar gumaka sun gauraya
addinin su ne da wannan sabon addini
da suka kwaikwaya. Saboda haka, ba
sa bautar gumakan a matsayin
iyayengiji sai dai a cewar su don su
kusantar da su zuwa ga Allah. Suna
cewa: “Mu ba mu bautar su don kome
sai don su kusantar da mu zuwa ga
Allah” Suratuz Zumar: 3. Haka kuma
ba su neman kome a wurin su na
alkiyama sai dai abin duniya. Ba su
kuma kiran su a lokacin tsanani da
matsuwa, kamar idan sun shiga jirgin
ruwa ga abin da Allah ya ce: “Kuma
idan suka hau jirgin ruwa sai su kira
Allah suna masu tsarkake ma sa addini.
A lokacin da ya kubutar da su sai ga su
suna masu yi ma sa tarayya”. Suratul
Ankabut: 65. Kenan sun yi imani da
Allah, kuma suna girmama dakinsa
amma saboda jahilci suka riki gumaka
a matsayin wani tsani zuwa ga Allah
wajen biyan bukatun duniya. Ya Allah
ka raba mu da jahilci.
6. Sai nahiyarmu ta Afrika:
Ba wani addini saukakke da aka taba
jin labarinsa a wannan nahiya daidai
lokacin da muke magana a kan sa.
Tsafe-tsafe da canfe-canfe da
bukukuwan gargajiya sune addinin
mutanen wannan sashe na duniya a
lokacin.
A takaice dai muna iya cewa, duniya ta
koma dulum shekaru sama da dari
biyar bayan tafiyar annabi Isah (AS).
Duniya ko ina ta cika da zalunci. A
yayin da jin dadi da sakewa na neman
kashe mahukunta, yunwa da fatara
gami da nauyin haraji su kuma sun ci
zarafin sauran jama’a bayin Allah.
Yaki ya game ko ina. Dokar dawa ita
ce tsarin tafi da kasashe; mai karfi ya
cinye maras karfi babu mai cewa komi.
Ta fuskar zamantakewa tsakanin
jama’a kuwa, mace ba ta da wani
matsayi a duniyar wancan lokaci. A
kasar Indiya sau da yawa mace kan
kone kanta idan mijinta ya riga ta
cikawa don kauce ma irin bakin ciki da
kuncin rayuwar da za ta iya shiga a
bayan sa. A kasashen turawa har
jayayya a kan “ko ita ma macce mutum
ce?!!!”. A kasar larabawa ma ba wani
banbanci ke akwai ba. Domin kuwa
mutum ya fi son ka kwashe shi mari da
ka yi masa albishir an haifa ma sa ‘ya
mace. (Alqur’ani mai girma, Suratun
Nahl:58 da kuma Zukhruf:17). Namiji
kuma yana iya auren ko mace nawa ya
ga dama. Sannan da rana tsaka
balarabe yakan iya rufe ‘yarsa ta
cikinsa a karkashin kasa da ranta da
lafiyarta saboda tsabar jahilci. Dalili
wai, kada ta girma ta janyo ma sa abin
kunya! Ko kuma ya kashe ta ne saboda
tsoron talauci domin ita ‘ya mace ci-
ma-kwance ce ba ta noma ba ta yaki
balle ta nemo abinci. Kai, in ban da
shan giya da dara da caca ba abin da
larabawa suka sa gaba.
A daidai wannan lokacin ne Allah
cikin rahamarsa ya kalli banu Adama
da idon rahama, ya yada ma su haske
wanda zai tsamar da su daga dimuwa
da gigita ya mayar da su cikin
hayyacinsu, ya aza su ga godabe
mikakke da zai samar ma su jin dadin
rayuwa a duniya da kyakkyawar
makoma a gobe kiyama. A nan ne
Allah ya kaddara haifuwar manzon
karshe Muhammadu dan Abdullahi
Sallallahu Alaihi Wasallam.
Zamu ci gaba in Allah ya so.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates