ALKAKI DA RUWAN ZUMA(Dr. Mansur Sokoto)

·

·

ALKAKI DA RUWAN ZUMA
Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta
Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi
Wasallam
Fitowa ta 14
Alfijir Ya Keto
An haifi fiyayyen halitta Muhammadu
dan Abdullahi bisa ga mafi rinjayen
zaton masana tarihi a ranar litinin
wadda ta zo daidai da 8 ga watan
Rabi’ul Awwal, shekara ta 13 kafin
hijira, 20 kenan ga watan Afrilun
shekarar 571 ta miladiyya. Amma a
wani kauli an ce 2 ga watan Rabi’u din
ne. A wani kaulin kuma 12 ga watan.
To, sai dai 2 ga wata talata ce, 12 kuma
jum’ah. Ga shi kuwa manzon Allah (S)
da kansa ya fadi cewa an haife shi ne a
ranar litinin, daya daga cikin dalilan da
suka sa yake azumtar wannan rana a
kowane sati. Sahihu Muslim, hadisi na
1162. Haka shi ma ra’ayin da ke cewa,
an haife shi ne a cikin watan azumi shi
ma ba ya da karfi sosai. Duba: Al-
Mawahib Al-Ladunniya, na Qastalani
(1/25) da Al-Bidaya Wan-Nihaya na
Ibn Kathir (2/260) da Al-Mi’yar Al-
Mu’rib na Wansharishi (7/100).
An haifi fiyayyen halitta ne a wani
wuri kusa da Ka’aba, wata 2 kacal
bayan yakin giwaye da madaukakin
sarki ya fada a Suratul Fil. A lokacin
haifuwarsa mahaifiyarsa ta ga wani irin
haske wanda ya haska ma ta benayen
kasar Sham. Shakka babu! Haske ne ta
haifo ma duniya wanda aka dade ana
jiran sa. Duba: Al-Musnad na Imam
Ahmad (5/262) da Al-Mustadrak na
Imam Al-Hakim (2/600) da Majma’
Az-Zawa’id na Haithami (8/222).
Maccen da ta karbi bikin manzon Allah
(S) ita ce kuyangar mahaifinsa; Ummu
Aiman. Haka kuma nono na farko da
ya tsotsa daga kirjin Suwaiba ne;
kuyangar baffansa Abu Lahabi. Babbar
alama mai nuna cewa, shi ne manzon
da ya zo ya ‘yanta bayi, ya fitar da
al’ummar duniya daga kangin bauta.
Duba: Ar-Rahmah Al-Muhdah, na
Sheikh Dr. Ali Muhammad As-Sheikh,
bugun Dar Maktabat Al-Iman,
Tarabulus, Lebanon, na farko,
1434H/2013M, shafi na 22.
Kafin mu fantsama a cikin tarihinsa
daga haifuwa zuwa jana’iza zai yi kyau
mu tsaya mu yi nazari kyakkyawa a
kan asalinsa. Domin duk wanda yake
tunanin cewa, manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam fulawar juji ne;
ma’ana, shi kadai ne nagartacce ba tare
da duge da asali gami da zumu ba to,
ya kwana da sanin cewa ya kurba giyar
gigita.
Allah ya hada mu a darasi na gaba.

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: