ALKAKI DA RUWAN ZUMA 56( Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

Musulmi Sun Ci Gaba Da Fuskantar
Wulakanci
Abdullahi bn Mas’ud Radhiyallahu
Anhu ya bayyana irin halin da
musulmi suka shiga a wancan lokaci.
Yana cewa: “Mutane bakwai ne aka
fara sanin musuluncinsu. Su ne:
Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam da Abubakar da Ammar da
mahaifiyarsa Sumayya. Sai kuma
Suhaibu da Bilal ba Miqdad. Shi dai
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam, Allah ya ba shi kariya ta
hanyar baffansa Abu Talib. Abubakar
shi ma da danginsa ne Allah ya yi
ma sa shamaki daga gare su. Sauran
kuwa sun sha azaba wadda ba ta
misaltuwa. Aka rinka sanya ma su
walkin karfe ana azabta su a rana.
Duk cikin su babu wanda ba a
dimauta hankalinsa aka tilasta shi
furta kafirci ba in ban da Bilal. Shi
kam babu yadda ba su yi da shi ba,
har suka gaji suka mika shi ga
shaidanun yara suna yawo da shi
rango rango a cikin Makka. Shi kuma
ba abinda yake fadi sai “Ahad!
Ahad!!” Yana nuni zuwa ga imaninsa
da tauhidi, kuma yana tabbata ma su
ba gudu babu ja da baya. Musnad na
Imam Ahmad, hadisi na 3832. Kuma
isnadin labarin yana da kyau.
Allahu Akbar! Bilal bawan Allah. Shi
ba wata kabila ko wasu dangi ko
wani gida da yake kariyar sa. Shi ba
dan gari ba ne, ba kuma farar fata ne
ba. Ba shi da karfi, ba shi da ‘yanci
domin bawa ne wanda aka saya da
kudi. Amma fa yana da zuciya mai
karfi, da imani mai kauri, da
sadaukantaka wacce ‘ya’ya masu
‘yanci suke bukatar su koya daga
wurinsa. Don haka bai fasa yin da’ar
da ta dace ga maigidansa Umayyatu
dan Khalaf ba. Amma maganar akida
ya riga ya zaba ma kansa wacce yake
ganin za ta fis she shi. Kuma duk
wani mataki da za a dauka ba zai
hana shi bayyana akidarsa ba. Ana
cikin haka ne watarana Allah – cikin
ikonsa – ya biyo da Abubakar
Radhiyallahu Anhu ta inda Umayyatu
yake azabta bawan nasa. Da
Abubakar ya gane ma idonsa abin da
ke faruwa sai ya tsaya ya yi ma
Umayyatu wa’azi yana ce ma sa, ka ji
tsoron Allah ka fita batun wannan
taliki. Umayyatu ya kada baki ya ce,
to wane ne ya lalata min shi ba kai
ba? Ka saye shi kawai in kana so ka
sake shi. Take sayyidina Abubakar ya
karbi tayinsa; ya sayi Bilal ya ‘yanta
shi. Daga nan Bilal ya fara shakar
kanshin ‘yanci da bautar Allah a cikin
sarari ba tare da tsangwama ba. Tun
da yake yanzu ya zama da mai ‘yanci
kamar kowa.
Shi kuma sayyidina Abubakar ba
wannan ne karon farko da yake
diyauta bayin Allah masu shan
wahala a hannun kafirai ba. Domin
shi ne ya diyauta Amir bin Fuhairata –
wanda ya halarci Badar da Uhud
kuma ya samu shahada a Ma’una.
Haka kuma ya diyauta bayi mata da
dama. Cikin su har da Ummu Ubais
da Zinnirah wadda kafirai suka yi ma
ta duka har suka tsiyaye idonta.
Kuma suka rika yi ma ta gori cewa,
don tana zagin Lata da Uzza ne suka
makantar da ita. Amma da ta roki
Allah sai ya warkar da ita, ganinta ya
dawo garau. Haka kuma Abubakar
Radhiyallahu Anhu ya diyauta
Nahdiyyah da ‘yarta a lokacin da ya
gan su uwargidansu ta aike su nikan
gari tana fadin wallahi ba zan taba
diyauta ku ba. Bayan da ya yi
cinikinsu ya biya sai ya ce ma su ku
ajiye ma ta garinta. Sai suka ce, ko
dai mu fara kai ma ta nikan mu
dawo? Ya ce, in kuna so ku kai ma ta
ba laifi. As-Sirah An-Nabawiyyah na
Ibn Hisham, (1/393). Akwai kuma
wata kuyangar da ya isko Umar bn
Khattab na azabtar da ita. Ita ma ya
saye ta ya diyauta ta.
Idan ana maganar wahalar da
musulmi suka sha a hannun kafirai
ba zai yiwu a manta da Yasir da
iyalinsa ba. Asalin Yasir dan kasar
Yemen ne. Alherin Allah ya ingizo shi
zuwa Makka wajen neman wani dan
uwansa. Ya zauna a karkashin Abu
Huzaifa bn Mughirah Al-Makhzumi
wanda ya aurar ma sa kuyangarsa
Sumayya suka haifi Ammar. Da
musulunci ya zo su duka ukun suka
sa hannu biyu suka karbe shi.
Makhzumawa kuwa suka rinka azabta
su azaba wadda ba ta misaltuwa.
Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam da
kansa ya gane ma idonsa irin azabar
da ake yi ma su. Ya rika ba su hakuri
yana cewa, “Ku yi hakuri iyalan Yasir,
babu shakka aljanna ce makomar
ku”. Sahih As-Sirah An-Nabawiyyah,
na Ibrahim Al-Ali, shafi na 97-98.
Ita dai Sumayya Abu Jahli ne ya
kashe ta. Shi kuma Yasir kaifin azaba
ya gama da shi. Suka bar dansu
Ammar yana dandanar zafin azaba a
cikin zafin duwatsun Makka har
sukan gigita shi ya furta kalmar
kafirci bai sani ba don su sassafta
ma sa. Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam ya yi ma su addu’a
yana cewa, “Ya Allah ka gafarta ma
iyalan Yasir. Kuma ma ai ka riga ka
gafarta ma su”. Majma’ Az-Zawa’id!
Na Haithami, (9/293).
Jan 18 at 11:11pm
Like · Comment · Share
Hide story
Ibraheem Muazzam Ibraheem
Funtua and 332 others like this.
Write a comment…
Comment
Basheer Lawan Nguru
ALLAH YA KARAWA WADANNAN BAYIN
ALLAH NA FARKO DARAJA DA
MATSAYI A ALJANNAH DOMIN IRIN
TSIYA DA AZABA DA KAFIRAN
WANNAN ZAMANIN SUKA YI MUSU.
Like · Reply · Jan 19 at 12:00am
Auwal Saleh
Allah saka Dr…Muna sauraron Karatu
daga Sheik Mai Hula yanzu haka a Jos
Like · 1 · Reply · Jan 18 at 11:14pm
Moh’d Abubakar Yarima
Allahu akbar kuma ahakan wasu
wadanda basuda adalci suke zagin
Abubakar ko mutum bayaso in yayarda
yamutu ranar gobe alqiyama sai yaga
Manzon Allah saw da Abubakar awaje
daya Malam Allah yaqara maka lafiya
ciwon hannu dakayi fama dashi Allah
yasa kaffarane kuma darasin alkaki da
ruwan zuma Allah yasa yazama
sanadiyar shi ganka aljannah amin
Like · 13 · Reply · Jan 18 at
11:44pm
7 replies
Sulaimans Kankara
Allahu Akbar! Allahu Akbar!! Allahu
Akbar!!! kaji wanda yayi amfani da
dukiyar da Allah ya hore masa yayi wa
addinin Allah Hidima tun a lokacin yin
haka na da tsada amman shine wasu
wadanda basu da rabon duniya da
lahira suke zagi da cin mutunci! Allah
ina rokonka don soyayyar da nike yi
wa ManzonKa (SAW) ka kara yardarka
ga aboki kuma surikin Annabinka
watau Abubakar (RA) da sauran
sahabbai baki daya. Kai kuma Dr.
Mansur Sokoto ina rokon Allah ya
sanya ka gama da duniya lafiya ranar
kiyama kuma Allah ya hada ni da kai
da Annabi Muhammdu (SAW) da
Abubakar, Umar, Usman, Aliyu (RA) da
duk sauran sahabban Annabi
Muhammadu (SAW) da wadanda suka
biyo bayansu da kyautatawa a cikin
aljannarSa Amin.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates