ALKAKI DA RUWAN ZUMA( Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

ALKAKI DA RUWAN ZUMA
Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da
Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi
Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala
Alihi Wasallam
Fitowa Ta 34
Daga Cikin Fifikonsa
3. Matsayin iyalansa (kashi na biyu)
Sanin duk mai bibiyar tarihin
musulmin farko ne cewa, iyalan
annabi Sallallahu Alaihi Wasallam
sun kasance abin girmamawa da
darajantawa matuka a tsakanin
musulmi, musamman ma dai
sahabban manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam. Wannan shi ya sa
al’ummar musulmi ta shiga wani hali
mawuyaci a lokacin da kaddarar
Allah ta gudana, ‘yan Shi’a suka
gayyaci sayyidi Husaini kuma suka
tozarta shi, suka mika shi aka kashe
shi a cikin garinsu tare da danginsa;
jikokin manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam. Al’ummar musulmi ta
girgiza matuka da wannan al’amari.
Abin tambaya a nan shi ne, su wane
ne iyakan annabi?
Amsa mafi sauki ga wannan tambaya
ita ce, su ne wadanda Allah ya
haramta ma su cin sadaka saboda
dangantakarsu ta zumunta da
manzon Allah. A madadin haka ya ce
a ba su daga cikin khumusin ganima.
Wadannan sun hada da, matansa da
‘ya’yansa da duk musulmin da ya fito
daga zuri’ar Abdulmuttalib kakan
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam. Bari mu kawo hujjoji daki
daki a kan wannan bayani.
1. Matan manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam:
Matan aure a kowane gida su ne
asalin iyali. Kamar yadda Allah ya
kira matar annabi Ibrahim a matsayin
iyalinsa. Ita ma matar annabi Musa
ya kira ta a matsayin iyalinsa. Matan
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam su ma ayoyin da muka
kawo na suratul Ahzab sun tabbatar
ma su da wannan suna. Kasancewar
su cikin iyalansa ya sa ba a ba su
sadaka sai dai a ba su daga cikin
khumusin ganima. Wannan shi ya sa
a lokacin da gwamnan Madina Khalid
bn Sa’id bn Al-Ass ya aika ma Nana
A’isha da nagge daga cikin shanun
sadaka sai ta maida ma sa, ta ce ai
mu iyalan Muhammad Sallallahu
Alaihi Wasallam sadaka ba ta halalta
a gare mu. Al-Musannaf na Ibn Abi
Shaiba (3/214). Ya kuwa za ayi
daudar dukiyar jama’a ta halalta ga
matan manzon Allah alhalin ko
‘yantaccen bawan manzon Allah (S)
da ya so ya raka wani ma’aikacin
zakka dan kabilar Bani Makhzum don
a raba da shi, annabi Sallallahu
Alaihi Wasallam ce ma sa ya yi ya yi
hakuri domin ba zai iya cin sadaka
ba saboda “Yantaccen bawan mutane
a cikinsu ya ke. Mu kuma zakka ba ta
halalta a gare mu”. As-Sunan na Abu
Dawud, hadisi na 1650 da As-Sunan,
hadisi na 657 da As-Sunan na
Nasa’i, hadisi na 2611.
Wannan kuma shi ne dalilin da ya sa
matan annabi suka shiga a cikin
salati kai tsaye kamar yadda ya zo a
wasu ruwayoyi. Duba: Jala’ul Afham
na Ibn Al-Qayyim, shafi na 331-333.
Kuma da annabi Sallallahu Alaihi
Wasallam ya ce “Ya Allah! Ka sanya
arzikin iyalan Muhammadu ya zamo
sese-da-sese”. Ai ba zai yiwu ace
iyalansa a nan ba matansa yake nufi
ba. A kullum mu tuna cewar da Allah
ya yi: “Ya ku matan annabi! Ba ku
kasance kamar kowa daga cikin mata
ba” Suratul Ahzab: 32. Saboda me ba
su daidai da sauran mata? Saboda
sun zama iyalan gida mafi daraja.
2. Mutanen “Kisa’i”:
Su ne mutane hudu da manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam ya shigar
da su a cikin bargonsa a yayin da
Allah ya saukar da waccan ayar kan
matansa, kuma ya roki Allah ya
shigar da su a cikin ta. Su ne,
Sayyidi Ali da matarsa Nana Fatima
da ‘ya’yansu biyu; Hasan da Husain
(RA). Da wannan su ma nassi ya
tabbatar da kasancewar su cikin
iyalan annabi.
3. Sauran ‘ya’yan manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam, wadanda
suka hada da, Al-Qasim da At-Tayyib
da Ibrahim da Zainab da Rukayya da
Ummu Kulthum da kuma zuri’arsu
gaba daya. Idan Durratu ‘yar Abu
Lahabi – baffan manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam – tana
cikin iyalansa kamar yadda manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam da
kansa ya fada (Majma’uz Zawa’id na
Haithami, hadisi na 15402), to, ina
kuma ga ‘ya’yan cikinsa?!
4. Sai kuma sauran dangin manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam
‘ya’ya da jikoki da zuri’ar
Abdulmuttalib. Akwai hadisai da
dama da suke tabbatar da haka,
kamar hadisin Durratu da muka kawo
a baya. Amma bari mu kara guda
daya a nan shi ne hadisin ‘ya’ya biyu
na baffannin manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam wadanda suka nemi
ya sanya su a cikin aikin zakka
domin su samu abin yin aure, sai ya
ce ma su “Ai zakka ba ta halalta ga
iyalan Muhammad, domin kazantar
mutane ce”. Sannan ya yi umurni aka
ba su kudin aure daga cikin
Khumusin ganima. Wadannan
matasan kuwa su ne Abdulmuttalib
dan Harith dan Abdulmuttalib da
kuma Fadhl dan Abbas dan
Abdulmuttalib. Duba Sahih Muslim,
hadisi na 1072.
Wannan ya nuna karara cewa, duk
dangin manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam na kusa, wadanda suka
hada kaka da shi suna cikin iyalansa.
Sharadi babba a wannan babi shi ne
kasancewar mutum musulmi bayan
zaman sa da ko jika ga
Abdulmuttalib. Ka ga shi Abu Lahabi
bai samu wannan falala ba. Ba don
kome ba sai don ya kafirce ma dan
baffan nasa da Allah mahalicci ya
aiko. Amma ‘yarsa Durratu da ta mika
wuya ta bi gaskiya kuma har ta yi
hijira, sai annabi Sallallahu Alaihi
Wasallam ya hana a cuta ma ta ta
hanyar yin maganar mahaifinta da
ayoyin da suka sauka a kansa. Kuma
a kan ta ya hau mimbari ya yi huduba
yana cewa, “Me ya sa ake cuta min a
cikin iyalaina”! Su ma ‘yan uwanta
guda biyu; Utbah da Mut’ib duk sun
musulunta, kuma suna cikin iyalan
fiyayyen halitta. Sai dan uwansu
guda daya shi ne Utaibah Allah bai
ma sa rabo ba. Shi ne kuma wanda
ya saki Ummu Kulthum -‘yar manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam –
bisa ga umurnin babansa.
Yanzu dai, ka ji su wane ne iyalan
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam amma fa a mahangar
mabiya tafarkin Sunnah. Su kam ‘yan
sha biyu sun jajirce ne cewa
mutanen Kisa’i su hudu ne kawai
iyalan annabi. Suka fitar da matansa
da ma sauran ‘ya’yansa da duk
danginsa daga cikin iyalan babban
gida. A haka kuma suke ganin su ne
masoyan Ahlulbaiti! Gidan da suke
cin zarafin matansa suna yi ma su
kage da kazafi. Ka samu littafinmu SU
WANE NE MASOYAN AHLULBAITI? Za
ka sha mamaki matuka game da irin
cin zarafin da suke ma sauran
‘ya’yan annabi da danginsa bayan
sun kore su daga zama cikin
Ahlulbait. Ya Allah muna sheda ma
ka cewa, mun barranta daga duk
wanda ya cutata ma manzonka a
game da iyalansa ko almajiransa.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

One response to “ALKAKI DA RUWAN ZUMA( Dr. Mansur Sokoto)”
  1. Murjanatu salihu gulma Avatar
    Murjanatu salihu gulma

    Allah subhanahu wata’ala ya bamu ikon bin sunnar manzonmu sau da kafa,ya kuma kare mu daga shubuhohin zamaninnan

Leave a Reply

Categories
Latest updates