Mas'alolin Azumi Na Daya

Tambaya: An tambayi Sheikh ibn uthaimeen: Hukuncin wanda yake bacci baki dayan Rana a watan Ramadan, Meye hukuncin azuminsa?
Amsa: Wannan mas’alar ta kunshi yanayi biyu:
1. Ya zamto cewa mutum yana baccin ne baki dayan rana kuma baya tashi sallah akan lokacinta, toh wannan mutumi mai laifi ne, ta yadda baya tashiwa yayi ibada akan lokacinta,
2. Ya zamto yana tashiwa yayi sallah akan lokacinta, toh wannan Bashi da Laifi, sai dai yana asarar alkhairi masu yawa, domin ya dace ace mai Azumi ya zamto ya shagaltar da lokacinsa baki daya wurin Sallah da zikiri da karatun Alkur’ani da sauran ayyukan Ibada.
Tambaya: An Tambayi Sheikh ibn uthaimeen: Meye hukuncin karya Azumin Ramadan ba tare da uzuri ba?
Amsa: karya Azumin Ramadan ba tare da uzuri ba babban laifi ne, kuma wanda yayi wannan aiki ya zama fasiqi, ya wajaba akansa ya tuba sannan kuma Ramako ya kamashi. Amma in yazamto cewa ana azumin Ramadana sai mutum yaki daukan Azumi da gangan, toh wannan babban laifi ne shima, kuma Mai wannan laifi fasiqi ne dole ya tuba zuwa ga Allah, amma Ramako baya kansa abisa zance mafi inganci, domin wannan ramako bazata amfanar dashi ba, domin baza’a amsa masa ba, domin Ka’ida shine: “Duk wata ibada da take da kayyadadden lokaci, idan aka jinkirta ta daga kan lokacinta, ba tare da wani uzuri ba to ba’a karbanta”. Domin Manzon Allah(Sallallahu Alaihi wasallam) Yace: “Duk wanda yayi aiki wanda babu umarninmu aciki to an mayar masa”
Kaga wanda yaki yin azumin Ramadana alokacinta yayi awani lokaci daban wanda babu umarnin Allah ko na Manzonsa na cewa ayi wannan azumi acikinta to yayi abinda ba’a umarceshi dashi ba.
Kamar yadda bazai yiwu mutum ya fara azumi ba kafin watan Ramadan, to haka nan bazai yiwu ya jinkirta ta ba tare da wani dalili ba.


Reference: A duba littafin
الصيام مجموعة أسئلة في أحكامها(للشيخ محمد بن صالح العثيمين).

Addu'a Takwabin Mumini

Addu’a shine babban takwabi awurin mumini wanda yafi ko wani irin Makami da zaiyi amfani dashi, babu wani abu da ya kamata mumini ya runguma ya lazimta a kowani lokaci irin addu’a, domin shine ibada, kamar Yadda Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya fadi kuma shine hanyar tsira daga kowani irin musiba, da damuwa, da cututtuka, na jiki da na zuciya. sannan babu wani abu mai mayar da Qaddara sai Addu’a, Sannan Allah madaukakin Sarki yana son Masu Rokonsa.
To Amma ya akeyin addu’a? Kuma meye sabuban karban addu’a da sabuban rashin karbansa? Wannan shine zamu tattauna akansa cikin wannan rubutu namu.
1. Sabuban Karban Addu’a da Sabuban Rashin Karbansa:

  • Ikhlasi: Kamar yadda ikhlasi shine kashin bayan ibadodi haka nan yake a addu’a, shima yana bukatar ikhlasi, ka roki Allah shi kadai, ba tare da ka hadashi da kowa.
  • Samun Yaqini: babban sababin karban addu’a shine yaqini, ya zamto cewa kana addu’a kuma kana samun Yaqini acikin zuciyarka cewa Allah Madaukakin Sarki zai amsa maka, kada kana addu’a kana cewa shin Allah zai amsa kuwa? Ko bazai amsa ba. Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) yace: “Ku roqi Allah kuna masu Yaqinin zai amsa muku”
  • Cin Halal: yana daga cikin sabbuban karban Addu’a Ta’amuli da Halal, ya zamto cewa mutum baya harka da haram, domin cin haram yana sabbaba rashin karban Addu’a.

YADDA MUSULMI ZAI YI TA'AMULI DA BUKIN KIRSIMETI

By: Dr. Ibrahim Jalo JalingoDa yake a Nigeria ana zaman cakuda ne tsakanin al’ummar Kirista da al’ummar Musulmi. Sannan da yake shi Musulunci addini ne da ya bayyanar da hukuncin dukkan wani lamari da ya shafi rayuwar dan Adam, ko dai ta hanyar nassi, ko ta hanyar zahiri, ko ta hanyar ishaarah da iimaai. Sannan da yake akwai karkatattu da dama da suke halatta abin da Shari’ah ba ta halatta ba, ko haramta abin da Shari’ah ba ta haramta ba, lalle ya dace a yi wa al’ummar Musulmi bayanin hukuncin abin da ya shafi wannan Idi na Kirsimeti ta bangarorinsa da ke iya shafar wasu al’ummar Musulmi.
To amma kafin mu shiga bayanin wadannan hukunce-hukunce ya kamata Musulmi su san abubuwa kamar haka:-
1. Shi dai bukin kirsimeti wata bidi’ah ce da bata da Kiristoci suka kirkira sannan suka maida ita wata ibada da ake samun lada ta hanyar yin ta kamar dai yadda wasu Musulmi suka kirkiri bidi’ar idin Maulidi, Kiristoci sun kirkiri wannan bidi’ar ce kuwa a shekarar Miladiyyah ta 360, watau a cikin karni na hudu bayan haifuwar Annabi Isa alaihis salam.
2. Ya kamata kowa ya san cewa ba ya halatta Musulmi ya yi tarayya da wadanda ba musulmi ba cikin bukukuwansu na idi, watau ta hanyar halartan wasu tarurruka da za su kira, ko ta hanyar ba su wani taimako domin karfafa idodin nasu, wannan dai shi ne hanyar Salafus Salih: Sahabbai, da Taabi’ai, da Taabi’uttaabi’in; dalili kuwa shi ne:-
Imamul Baihaqiy ya ruwaito cikin As-Sunanul Kubraa hadithi na 19,334 cewa Sayyidina Umar Dan Khattab Allah Ya kara masa yarda ya ce: ((اجتنبوا اعداء الله في عيدهم)). Ma’ana: ((Ku nisanci makiya Allah cikin idinsu)).
Sannan Shaikhul Islam Ibnu Tamiyyah ya ce -kamar yadda ya zo cikin Al-Mustadrak Alaa Fataawaa Ibnu Tamiyyah 1/108, da Mukhtasarul Fataawaa Misriyyah1/517 :-
((وليس للمسلمين ان يعينوهم على أعيادهم لا ببيع ما يستعينون به على عيدهم ولا باجارة دوابهم ليركبوها في عيدهم لان أعيادهم مما حرمه الله تعالى ورسوله صلى الله عليه وسلم لما فيها من الكفر والفسوق والعصيان)). انتهى.
Ma’ana: ((Musulmi ba su da damar su taimaka musu cikin idodinsu, ko dai ta hanyar sayar musu da abin da za su karfafu da shi, ko ta hanyar ba da hayar dabbobinsu domin su hau su cikin idinsu, saboda idodinsu na daga cikin abin da Allah Madaukakin Sarki da kuma manzonSa mai tsira da amincin Allah suka haramta, saboda abin da yake cikinsu na kafirci da fasikanci da kuma sabo)).
Read More…

SUNNAH CE KADA A CI KOME A SAFIYAR IDIN LAYYA HAR SAI AN DAWO DAGA IDI TUKUN

By: Dr. Ibrahim Jalo JalingoYana daga cikin abin da yake Sunnah a ranar idin Layya kada a ci abinci sai bayan an gama sallar idi tukun an dawo. Sannan shi kuma mai abin layya zai yi buda-bakin ne da hantar layyarsa; saboda dalili kamar haka:-
Imamut Tirmiziy ya ruwaito Hadithi na 546, da Imam Ahmad Hadithi na 22,984, da Imam Ibnu Khuzaimah Hadithi na 1426, da Imamud Daaraqudniy Hadithi na 1715, da Imam Ibnu Hibban Hadithi na 2812, da Imam Haakim Hadithi na 1088, da Imamul Baihaqiy cikin Sunan Hadithi na 6380, da Ma’arifatus Sunan Hadithi na 1912 da Isnadi Sahihi daga Sahabi Buraidah Bin Susaib Allah Ya kara masa yarda ya ce:
((كان النبي صلى الله عليه وسلم لا يخرج يوم الفطر حتى يطعم، ولا يطعم يوم الأضحى حتى يصلي)).
Read More…

MA'ANAR SALAFIYYAH

By: Dr. Ibrahim Jalo JalingoMa’anar Salafiyyah shi ne: bin hanyar magabata; watau Sahabbai, da Taabi’ai, da Taabi’ut Taabi’iina, da Taabi’ut Taabi’it Taabi’iina wajen girmama Annabi mai tsira da amincin Allah, da barin maganar kowa a duk lokacin da ta yi karo da maganarsa, da nuna fashi da damuwa a duk lokacin da aka ga wani ya yi watsi da maganar; Saboda wannan matsayi lalle shi ne matsayin Sahabbai, da Taabi’ai, da Taabi’ut Taabi’iina, da Taabi’ut Taabi’it Taabi’iina. Ga misalai kadan na irin yadda Sahabbai suke girmama maganar Annabi, suke bin maganarsa sau-da-kafa, suke kuma nuna fushinsu a kan duk wani da ya ki bin maganarsa ya koma yana bin maganar waninsa:- 1. Bukhariy ya ruwaito Hadithi na 3093, da Muslim Hadithi na 1759 cewa babban Sahabi Sayyidina Abubakar As-Siddiq ya ce:-
((لست تاركا شيئا كان رسول الله صلى الله عليه وسلم يعمل به الا عملت به فاني اخشى ان تركت شيئا من أمره ان أزيغ)).
Read More…

IDAN IDI YA KASANCE A RANAR JUMA'A TO BABU WAJIBCIN SALLAR JUMA'A A RANAR:

By: Dr. Ibrahim Jalo Jalingo


Idan idi ya kasance a ranar Juma’a to babu wajibcin sallar Juma’a a ranar; wannan hukuncin ne za a iya fahimta in aka yi kyakkyawan nazari cikin hadithai biyar da suka zo cikin wannan babin, hadithan kuwa su ne kamar haka:- (1) Imam Abu Dawud ya ruwaito hadithi na 1,070 da Imam Ibnu Majah hadithi na 1,326 da isnadi sahihi daga Iyas Dan Abii Ramlah ya ce:-
((شهدت معاوية بن ابي سفيان وهو يسال زيد بن أرقم قال: أشهدت مع رسول الله صلى الله عليه وسلم عيدين اجتمعا في يوم؟ قال: نعم. قال: فكيف صنع؟ قال: صلى العيد ثم رخص في الجمعة، فقال: من شاء ان يصلي، فليصل))
. Ma’ana: ((Na halarci Mu’awiyah Dan Abii Sufyaan yana tambayar Zaid Dan Arqam ya ce: Ko ka halarci Idi biyun da suka hadu a rana guda tare da Manzon Allah? Sai ya ce: Na’am. Sai ya ce: to yaya ya yi? Sai ya ce: Ya yi sallar Idin sannan ya rangwanta yin sallar juma’a, ya ce: Wanda ya so yin sallar sai ya yi sallar)). (2) Imam Ibnu Majah ya ruwaito hadithi na 1,329 da isnadi sahihi daga Sahabi Abdullahi Dan Umar ya ce:-
Read More…

Muhadarorin Sheikh Albani Zaria

Copyright: Darul-Hadith Assalafiyyah, Zaria.


Tarihin Albani ZariaRaddi Kan Qazafin AlmizanMatsalolin Jahiliyya 1Matsalolin Jahiliyyah 2TarbiyyahKaren Bana 1Karen Bana 2Karen Bana 3Karshen Alewa 2Karshen Alewa 3Karshen Alewa 4Iyaye Mata 1Iyaye Mata 2Hukuncin Sallolin IdiHukuncin Laya 1Hukuncin Laya 2Hukuncin Laya 3Hukuncin Laya 4Hukunce Hukuncen IdiBayani Kan Bid’ah 1Bayani Kan Bid’ah 2Bayani Kan Bid’ah 3AshuuraaAdaidaita Sahu 1Adaidaita Sahu 2Adaidaita Sahu 3Adaidaita Sahu 4Jahiliyya 1Jahiliyya 2Jahiliya 3Jahiliyya 4Jahiliyya 5Jihadin Dan Fodio 1Jihadin Dan Fodio 2|Jihadin Dan Fodio 3Gulma 1Gulma 2Click Here For Any Inquiry, Also Don’t Forget to Like My page on Facebook for latest update

Islamic Conference hosted by Jibwis Nigeria

this are some audio files from the “islamic conference” hosted by Jibwis Nigeria 2016.
Audio 1 | Server 2
Audio 2 | Server 2
Audio 3 | Server 2
Audio 4 | Server 2
Audio 5 | Server 2
Audio 6 | Server 2
Audio 7 | Server 2
Audio 8 | Server 2
Audio 9 | Server 2
Audio 10 | Server 2
Audio 11 | Server 2
Audio 12 | Server 2
Audio 13 | Server 2
Audio 14 | Server 2


Click Here To Report any Error.