Mas'alolin Azumi Na Daya

Tambaya: An tambayi Sheikh ibn uthaimeen: Hukuncin wanda yake bacci baki dayan Rana a watan Ramadan, Meye hukuncin azuminsa?
Amsa: Wannan mas’alar ta kunshi yanayi biyu:
1. Ya zamto cewa mutum yana baccin ne baki dayan rana kuma baya tashi sallah akan lokacinta, toh wannan mutumi mai laifi ne, ta yadda baya tashiwa yayi ibada akan lokacinta,
2. Ya zamto yana tashiwa yayi sallah akan lokacinta, toh wannan Bashi da Laifi, sai dai yana asarar alkhairi masu yawa, domin ya dace ace mai Azumi ya zamto ya shagaltar da lokacinsa baki daya wurin Sallah da zikiri da karatun Alkur’ani da sauran ayyukan Ibada.
Tambaya: An Tambayi Sheikh ibn uthaimeen: Meye hukuncin karya Azumin Ramadan ba tare da uzuri ba?
Amsa: karya Azumin Ramadan ba tare da uzuri ba babban laifi ne, kuma wanda yayi wannan aiki ya zama fasiqi, ya wajaba akansa ya tuba sannan kuma Ramako ya kamashi. Amma in yazamto cewa ana azumin Ramadana sai mutum yaki daukan Azumi da gangan, toh wannan babban laifi ne shima, kuma Mai wannan laifi fasiqi ne dole ya tuba zuwa ga Allah, amma Ramako baya kansa abisa zance mafi inganci, domin wannan ramako bazata amfanar dashi ba, domin baza’a amsa masa ba, domin Ka’ida shine: “Duk wata ibada da take da kayyadadden lokaci, idan aka jinkirta ta daga kan lokacinta, ba tare da wani uzuri ba to ba’a karbanta”. Domin Manzon Allah(Sallallahu Alaihi wasallam) Yace: “Duk wanda yayi aiki wanda babu umarninmu aciki to an mayar masa”
Kaga wanda yaki yin azumin Ramadana alokacinta yayi awani lokaci daban wanda babu umarnin Allah ko na Manzonsa na cewa ayi wannan azumi acikinta to yayi abinda ba’a umarceshi dashi ba.
Kamar yadda bazai yiwu mutum ya fara azumi ba kafin watan Ramadan, to haka nan bazai yiwu ya jinkirta ta ba tare da wani dalili ba.


Reference: A duba littafin
الصيام مجموعة أسئلة في أحكامها(للشيخ محمد بن صالح العثيمين).

SUNNAH CE KADA A CI KOME A SAFIYAR IDIN LAYYA HAR SAI AN DAWO DAGA IDI TUKUN

By: Dr. Ibrahim Jalo JalingoYana daga cikin abin da yake Sunnah a ranar idin Layya kada a ci abinci sai bayan an gama sallar idi tukun an dawo. Sannan shi kuma mai abin layya zai yi buda-bakin ne da hantar layyarsa; saboda dalili kamar haka:-
Imamut Tirmiziy ya ruwaito Hadithi na 546, da Imam Ahmad Hadithi na 22,984, da Imam Ibnu Khuzaimah Hadithi na 1426, da Imamud Daaraqudniy Hadithi na 1715, da Imam Ibnu Hibban Hadithi na 2812, da Imam Haakim Hadithi na 1088, da Imamul Baihaqiy cikin Sunan Hadithi na 6380, da Ma’arifatus Sunan Hadithi na 1912 da Isnadi Sahihi daga Sahabi Buraidah Bin Susaib Allah Ya kara masa yarda ya ce:
((كان النبي صلى الله عليه وسلم لا يخرج يوم الفطر حتى يطعم، ولا يطعم يوم الأضحى حتى يصلي)).
Read More…

HARAMUN NE MUSULMI YA WUCE GONA DA IRI GAME DA ZATIN MANZON ALLAH MAI TSIRA DA AMINCIN ALLAH(Dr Ibrahim Jalo Jalingo)

HARAMUN NE MUSULMI YA WUCE GONA DA IRI GAME DA ZATIN MANZON ALLAH MAI TSIRA DA AMINCIN ALLAH
Imamul Bukhaarii ya ruwaito hadithi na 3,445, da Imamu Muslim hadithi na 1,691 cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce:-
((لا تطروني كما أطرت النصارى ابن مريم انما انا عبد فقولوا: عبد الله ورسوله)). انتهى.
Ma’ana: ((kada ku wuce gona da iri cikin yabona, kamar yadda Kirista suka wuce gona da iri cikin yabon Dan Maryam, ni ba kowa ba ne face bawa, ku ce: bawan Allah kuma manzonSa)). Intaha.
‘Yan’uwa Musulmi! Ga shi dai kun ji da kunnuwanku cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya hana al’ummarsa wuce iyakar Sahari’ah cikin yabonsa, ma’ana su yi wata karya game da shi da nufin yabo, to amma kuma abin bakin ciki da mamaki sai ga shi an samu wasu nau’in ‘yan bidi’ah da suka bijire wa wannan hani nasa suka wuf suka fada cikin wannan musiba ta guluwwi !!
Misali: ya zo cikin babban littafin ‘Yan Darikar Tijjaniyyah mai suna Jawaahirul Ma’anii 1/147 kamar haka:-
((اول ما خلق الله تعالى روح محمد صلى الله عليه وسلم ثم نسل الله منها أرواح الكائنات ثم كون الله من جسد النبي صلى الله عليه وسلم أجساد الملائكة والأنبياء والأقطاب)). انتهى.
Ma’ana: ((Farkon abin da Allah Ya halitta shi ne ran Muhammad mai tsira da amincin Allah, sannan ya halitta sauran rayukan halittu daga shi (wannan ran) sannan kuma Allah Ya halicci jikkunan Mala’iku da Annabawa da Manyan waliyyai daga jikin Annabi Mai tsira da amincin Allah))!!! Intaha.
‘Yan’uwa Musulmi masu girmama Allah da Shari’ar da ya aiko ManzonSa da ita! Don Allah ku dubi abin da suka rubuta a nan na tabbatar da cewa: wai da Annabi Adamu da kuma Mala’iku da sauran halittu dukkansu zurriya ce daga Annabi Muhammad, duk kuwa da cewa ijama’in dukkan Musulmin kwarai ya kullu a kan cewa Annabi Muhammad yana daga cikin zurriyyar Annabi Adam ne ba wai shi Annabi Adam din ba ne yake daga cikin zurriyyar Annabi Muhammad mai tsira da amincin Allah ba, saboda Allah Madaukakin Sarki Ya ce cikin Suratul Hijri aya ta 28-29 :-
((وإذ قال ربك للملائكة اني خالق بشرا من صلصال من حما مسنون. فإذا سويته ونفخت فيه من روحي فقعوا له ساجدين)). انتهى.
Ma’ana: ((A lokacin da Ubangijinka Ya ce wa Mala’iku lalle ne ni Mai halittan wani dan adam ne daga wani irin laka busashshe, daga wani irin bakin tabo jirkitacce, to idan na daidaita shi, kuma na busa raiNa cikin shi, to sai ku fadi kuna masu yi masa sujjada)). Intaha.
Sannan kuma Ya ce cikin suratus Sajdah aya ta 7-8 :-
((الذي أحسن كل شيء خلقه وبدا خلق الانسان من طين. ثم جعل نسله من سلالة من ماء مهين)).
Ma’ana: ((Shi ne wannan da Ya kyautata dukkan kome da Ya halitta shi, sannan Ya fara halittar jinsin mutum ne da laka, daga nan Ya yi zurriyyarsa daga wani irin daskararren jini da kuma wani irin ruwa kaskantacce)). Intaha.
‘Yan’uwa Musulmi! Wannan shi ne abin da Allah Ya gaya mana a cikin Alkur’ani Mai girma, kuma jinsin mutum da ake nufi a cikin wadannan ayoyin shi ne Annabi Adam alaihis salam, ba wai Annabi Muhammad mai tsira da amincin Allah ba.
Muna fata masu bin Darikar Tijjaniyyah za su yi tunani mai zurfi, su gauggauta tuba zuwa ga Ubangijinsu, su kyautata Musuluncinsu, su yi watsi da irin wadannan akidu na ilhadi, su dawo su yi Musulunci irin wanda Annabi sa sahabbansa da kuma tabi’ansu suka yi.
Babu abin da muke nufi sai gyara iya iyawarmu, kuma Allah Shi ne madogararmu, muna kuma fata Ya taimake mu Ya nuna mana gaskiya gaskiya ce Ya ba mu ikon bin ta, Ya kuma nuna mana karya karya ce Ya ba mu ikon guje mata.

DORA DAMA A KAN HAGU CIKIN SALLA SHI NE SUNNAH, SAKIN HANNAYE CIKIN SALLA SABANIN SUNNAH NE(Dr Ibrahim Jalo Jalingo)

Imamush Shaukaanii ya ce cikin
littafinsa Nailul Autaar 2/205:
((Hadithan dora dama a kan hagu
ishrin ne suka zo daga Annabi mai
tsira da amincin Allah ta hanyar
mutum goma sha takwas, tsakanin
Sahabi da Tabi’i)).
Ga wasu daga cikin hadithan da
Imamush Shaukaanii ya yi
maganarsu:-
1- Imamu Muslim ya ruwaito hadthi
na 401 cewa: Annabi mai tsira da
amincin Allah: ((Ya kasance yana
dora hannun damansa a kan
hagunsa)).
2- Imamul Bukharii ya ruwaito
hadithi na 740 da Imam Malik cikin
Muwattaa hadithi na 546 cewa
Manzon Allah mai tsira da amincin
Allah yana umurtan sahabbansa
da dora dama a kan hagu:
((Mutane sun kasance ana
umurtan su da cewa: mutum ya
dora damansa a kan zira’insa na
hagu a cikin Salla)).
3- Imamut Tabaraanii ya ruwaito
cikin Almu’ujamul Kabiir hadithi na
11,323, da Imamud Daara Qudnii
cikin Babun Fi Akhzish Shimaal Bil
Yamiin hadithi na 3, da Imam Ibnu
Hibbaan dadithi na 1,770, da Imam
Sulaimaan Ibnu Dawud Attayaalisii
cikin Musnad hadithi na 2,776
cewa Annabi mai tsira da amincin
Allah ya kasance yana cewa: ((Mu
taron Annabawa an umurce mu da
gauggauta buda-baki, da jinkirta
sahur, da kuma mu dora
hannayenmu na dama a kan
hannayenmu na hagu)). Albaanii
ya inganta hadithin cikin Sahihul
Jami’is Sagiir 1/454.
4- Imam Ahmad ya ruwaito hadithi
na 15,090, da Imam Abu Dawud
Hadiyhi na 755, da isnadi sahihi
cewa Manzon Allah mai tsira da
amincin Allah ((Ya wuce wani
mutum yana salla amma ya dora
hannunsa na hagu a kan na dama,
sai ya balle hannun ya dora daman
a kan hagun)).
5- Imam Abu Dawud ya ruwaito
hadithi na 727, da Imam Nasa’ii
hadithi na 963, da Imam Ibnu
Khuzaimah hadithi na 480 da
isnadi sahihi cewa Manzon Allah
mai tsira da amincin Allah ((Ya
kasance yana dora dama a kan
bayan tafinsa na hagu, da kuma
wuyan hannu, da dantse)).
6- Imama Abu Dawud ya ruwaito
hadithi na 759, da Imam Ibnu
Khuzaimah hadithi na 479 cewa
Annabi mai tsira da amincin Allah
((Ya kasance yana sanya hannun
damansa a kan hagunsa, sannan
sai ya hada tsakaninsu a kan
kirjinsa alhalin yana cikin salla)).
TAMBAYOYI TARE DA
AMSOSHINSU:
(1) Idan wani ya ce: Amma kuma ai
Imamut Tabarii ya ruwaito cikin
littafinsa Almuujamul Kabiir hadithi
na 16,563, daga Sahabi Mu’azu
Dan Jabal ya ce:-
(( ﻛﺎﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺍﺫﺍ ﻛﺎﻥ ﻓﻲ
ﺻﻼﺗﻪ ﺭﻓﻊ ﻳﺪﻳﻪ ﻗﺒﺎﻟﺔ ﺃﺫﻧﻴﻪ، ﻓﺈﺫﺍ ﻛﺒﺮ ﺍﺭﺳﻠﻬﻤﺎ، ﺛﻢ
ﺳﻜﺖ، ﻭﺭﺑﻤﺎ ﻳﻀﻊ ﻳﻤﻴﻨﻪ ﻋﻠﻰ ﻳﺴﺎﺭﻩ )).
Ma’ana: ((Annabi mai tsira da
amincin Allah ya kasance idan
yana cikin sallarsa sai ya daga
hannu daura da kunnensa, idan ya
yi kabbara sai ya sake su, sai
kuma ya yi shiru, wani lokaci ma
nakan gan shi yana dora damansa
a kan hagunsa)). Wannan hadithi
ai shi ne hujjar sake hannu!!
Sai a ce da shi: Da farko dai ya
kamata ka san cewa wannan
hadithi maudhuu’i ne, watau
hadithi ne da cikin isnadinsa akwai
makaryaci kazzaabi wannan kuwa
shi ne: Khasiib Bin Jahdar, ya zo
cikin littafin Miizaanu Litidaal 1/653
kamar haka:-
(( ﺍﻟﺨﺼﻴﺐ ﺑﻦ ﺟﺤﺪﺭ: ﻋﻦ ﻋﻤﺮﻭ ﺑﻦ ﺩﻳﻨﺎﺭ، ﻭﺃﺑﻲ
ﺻﺎﻟﺢ ﺍﻟﺴﻤﺎﻥ، ﻛﺬﺑﻪ ﺷﻌﺒﺔ ﻭﺍﻟﻘﻄﺎﻥ ﻭﺍﺑﻦ ﻣﻌﻴﻦ.
ﻭﻗﺎﻝ ﺍﺣﻤﺪ: ﻻ ﻳﻜﺘﺐ ﺣﺪﻳﺜﻪ. ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ: ﻛﺬﺍﺏ
ﺍﺳﺘﻌﺪﻯ ﻋﻠﻴﻪ ﺷﻌﺒﺔ)).
Ma’ana: ((Khasiib Bin Jahdar: daga
Amr Bin Diinaar, da Abu Salihis
Sammaan: Shu’ubah, da Qattaan,
da Ibnu Ma’iin sun karyata shi.
Ahmad ya ce: Ba a rubuta
hadithinsa. Bukharii ya ce:
Makaryaci ne, Shu’ubah ya yi
bayanin karyarsa))
Na biyu: Da za a kaddara cewa
hadithin ingantacce ne, to da sai a
fassara shi da cewa: yana nufin
bayan Annabi ya daga
hannayensa daura da kunnuwansa
lokacin kabbarar harama, ya kan
sake hannayen nasa ne zuwa
kirjinsa, dole a yi irin wannan
fassarar saboda hadithin ya dace
da sauran hadithai ingantattu cikin
babin.
Babban masanin ilmin hadithi
Alhaafiz Ibnu Hajar ya ce cikin
littafinsa: Attalkhiisul Habiir 1/554:-
(( ﺗﻨﺒﻴﻪ: ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻐﺰﺍﻟﻲ: ﺳﻤﻌﺖ ﺑﻌﺾ ﺍﻟﻤﺤﺪﺛﻴﻦ
ﻳﻘﻮﻝ: ﻫﺬﺍ ﺍﻟﺨﺒﺮ ﺍﻧﻤﺎ ﻭﺭﺩ ﺑﺎﻧﻪ ﻳﺮﺳﻞ ﻳﺪﻳﻪ ﺍﻟﻰ
ﺻﺪﺭﻩ، ﻻ ﺍﻧﻪ ﻳﺮﺳﻠﻬﻤﺎ ﺛﻢ ﻳﺴﺘﺄﻧﻒ ﺭﻓﻌﻬﻤﺎ ﺍﻟﻰ
ﺍﻟﺼﺪﺭ. ﺣﻜﺎﻩ ﺍﺑﻦ ﺍﻟﺼﻼﺡ ﻓﻲ ﻣﺸﻜﻞ ﺍﻟﻮﺳﻴﻂ )).
Ma’ana: ((Fadakarwa: Gazaalii ya
ce: Na ji sashin malaman hadithi
na cewa: Wannan hadithi ya zo ne
a kan cewa yana sake hannayensa
ne zuwa girjinsa, ba wai yana sake
su ba ne, sannan daga baya ya
daga su zuwa girji ba. Ibnus
Salaah ya hikaito shi cikin
“Mushkilul Wasiit”)).
(2) Idan wani kuma ya ce: To ai an
samu daga cikin magabata
wadanda suka yi salla hannayensu
a sake, don mene ne za a ce da
mu yanzu: ba za mu yi salla
hannayenmu a sake ba?
To sai a ce da shi: Na farko dai ya
kamata ka san cewa ya kai
dan’uwa! Annabi Muhammad mai
tsira da amincin Allah shi ne kadai
wanda Allah Ya aiko shi zuwa gare
ka, bai aiko waninsa zuwa gare ka
ba a matsayin manzo, saboda
haka ba daidai ba ne ka bar
umurninsa shi Annabi Muhammad
ko kuma ka bar aikinsa, sannan ka
je kana riko da umurni ko da aikin
wani koma wane ne shi a wannan
duniya!
Abu na biyu: A lokacin da Sahabi
Abdullahi Dan Abbas ya yi
yunkurin tabbatar da sunnar
tamattu’i cikin Hajji, an samu wasu
mutane da suka ce da shi: Ai
Abubakar da Umar sun hana
Mut’ar Hajji, shi kuwa sai ya amsa
ya ce da su: ((Wani dutse ya yi
kusan sauko muku daga sama! Ina
ce muku: Manzon Allah mai tsira
da amincin Allah ya ce, sannan
kuna ce da ni: Abubakar da Umar
sun ce!)).
Wannan magana ta Abdullahi Dan
Abbas asalinta na cikin Musnadu
Ahmad hadithi na 3,121, da
Almuujamul Ausat na Tabaraanii
hadithi na 21, da Jami’u bayanil
ilmi na Ibnu Abdil Bar hadithi na
2,377, da Alfaqih wal Mutafaqqih
na Khatiibul Bagdaadii hadithi na
380.
Abu na uku shi ne: Barin aiki da
maganar Annabi ko aikinsa zuwa
yin aiki da maganar wani ko
aikinsa saba wa Ijma’in Al’ummah
ne, shi kuwa yin hakan haramun
ne a bisa ittifakin dukkan malaman
Duniya, idan Annabi ya yi umurni
da a yi Kablu a cikin salla sannan
ka ji wani kuma yana cewa a yi
sadlu domin ai sadlu ba ya bata
salla to lalle wannan mutum ya yi
haramun ya zama mai sabon Allah
a bisa ijma’in Maluman Musulunci!
Ya zo cikin littafin Iiqazul Himam
shafi na 68 cewa Imamush Shafi’ii
ya ce: ((Musulmi sun yi Ijma’i a kan
cewa duk wanda sunnar Manzon
Allah mai tsira da amincin Allah ta
bayyana gare shi, to, ba ya halatta
gare shi ya bar ta saboda yin riko
da maganar wani)).
(3) Idan wani ya ce: To ai sake
hannaye cikin salla shi ne
mazhabar Imam Malik, tunda mu
kuwa Malikiyyah ne ke nan dukkan
abin da Imam Malik ya yi na Addini
shi ne mu ma za mu yi!!
To sai a ce da shi: Na farko dai ya
kamata ka san cewa Allah
Madaukakin Sarki bai aiko maka
Imam Malik a matsayin manzo ba,
a’a Ya aiko maka Annabi
Muhammad ne a matsayin manzo
zuwa gare ka kai da sauran
mutanen Duniya baki daya, shi
kuwa Annabi Muhammad babu
inda ya ce da kai ka yi salla
hannayenka a sake, a’a abin da ya
ce da kai shi ne: Ka dora damanka
a kan hagunka cikin sallanka. Ta
kaka za ka bar nasa ka riki na wani
komin girmansa kuwa a idanunka?
A bu na biyu: cewa da ka yi:
mazhabar Imam Malik ita ce: yin
salla hannaye a sake, magana ce
mara dikka, saboda shi Imam Malik
yana da fatawowi daidai har guda
hudu ne cikin wannan mas’alar, ba
wai fatawa daya kawai ba.
Babban Malami cikin mazhabar
malikiyyah Imamul Baajii ya ce
cikin littafinsa Almuntaqaa 1/281:
Imam Malik yana da fatawowi hudu
da aka ruwaito daga gare shi cikin
wannan mas’alar: Fatawar farko:
Ash’hab ya ruwaito daga gare shi
cewa: Babu laifi a dora dama a kan
hagu cikin sallar nafila da farilla.
Fatawa ta biyu: Mutarrif da Ibnul
Maajishuun da kuma almajiransa
na Iraq sun ruwaito daga gare shi
cewa: Dora dama a kan hagu cikin
salla mustahabbi ne. Fatawa ta
uku: Mutanen Iraq sun ruwaito
daga Malikawa daga shi Imam
Malik cewa: Kada a dora dama a
kan hagu cikin salla. Fatawa ta
hudu: Ibnul Qaasim ya ruwaito
daga gare shi cewa: makruuhi ne a
dora dama a kan hagu cikin sallar
farilla, amma babu laifi a yi hakan
cikin sallar nafila.
A nan ai kun ga ya kamata a ce
imma Malikiyyar za a yi, to sai a yi
wacce ta dace da sunnar Annabi
mai tsira da amincin Allah, ba wai
wacce ta saba wa sunnar
Muhammadur Rasuulul Lahi ba,
Allah ya taimake kan yin aiki da
sahihiyar Sunnar ManzonSa.
(4) Idan wani ya ce: To mene ne
fahimtar Malamanmu na Da’awah
da Aqidah kuma cikin wannan
mas’alar?
Sai a ce da shi: Fahimtar mutanen
da muka sani daga cikinsu ita ce:
Yin salla hannaye a sake abu ne
da yake sabanin Sunnah. Misali:
Sheik Abdulaziz Bin Baz ya ce
cikin littafinsa na fatawa 11/144:-
(( ﺍﻟﺜﺎﺑﺖ ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺍﻧﻪ
ﻳﻘﺒﺾ ﻳﺪﻳﻪ ﺣﺎﻝ ﻗﻴﺎﻣﻪ ﻓﻲ ﺍﻟﺼﻼﺓ… ﺍﻣﺎ ﺇﺭﺳﺎﻝ
ﺍﻟﻴﺪﻳﻦ ﻓﻲ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻓﻤﻜﺮﻭﻩ ﻻ ﻳﻨﺒﻐﻲ ﻓﻌﻠﻪ ﻟﻜﻮﻧﻪ
ﺧﻼﻑ ﺍﻟﺴﻨﺔ )).
Ma’ana: ((Abin da ya tabbata daga
Annabi mai tsira da amincin Allah
shi ne cewa: Yana kame
hannayensa ne lokacin da yake
tsaye cikin salla ..Amma sake
hannaye a cikin salla makruhi ne,
yin sa bai kamata ba, saboda
kasancewarsa sabanin Sunnah)).
Sannan ya sake cewa cikin
wannan littafin nasa 11/145:-
(( ﻭﺑﻤﺎ ﺫﻛﺮﻧﺎﻩ ﺗﻌﻠﻤﻮﻥ ﺍﻥ ﺇﺭﺳﺎﻝ ﺍﻟﻴﺪﻳﻦ ﻻ ﻳﻘﺪﺡ
ﻓﻲ ﺍﺳﻼﻡ ﺍﻟﻤﺴﻠﻢ، ﻭﻻ ﻓﻲ ﺍﻛﻞ ﺫﺑﻴﺤﺘﻪ ﻟﻜﻨﻪ ﻣﻜﺮﻭﻩ
ﻭﻣﺨﺎﻟﻒ ﻟﻠﺴﻨﺔ ﻻ ﻳﻨﺒﻐﻲ ﻓﻌﻠﻪ )).
Ma’ana: ((Saboda abin da muka
ambata din nan ne za ku san
cewa: Sake hannaye ba ya soke
Musuluncin Musulmi, haka nan cin
yankansa, sai dai kuma shi
makruhi ne, kuma abu ne da ya
saba wa Sunnah, ba ya kamata a
yi shi)).
Sannan ya sake cewa cikin
wannan littafi nasa 29/239:-
(( ﻫﺬﺍ ﻣﻜﺮﻭﻩ، ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ ﺿﻤﻬﻤﺎ ﻭﺟﻌﻠﻬﻤﺎ ﻋﻠﻰ
ﺍﻟﺼﺪﺭ، ﻭﺟﻌﻞ ﺍﻟﻴﻤﻨﻰ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻴﺴﺮﻯ ﻭﺍﻟﺮﺳﻎ
ﻭﺍﻟﺴﺎﻋﺪ؛ ﻻﻧﻪ ﻗﺪ ﺛﺒﺖ ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﻣﻦ ﺣﺪﻳﺚ ﺳﻬﻞ ﺑﻦ ﺳﻌﺪ، ﻭﻭﺍﺋﻞ ﺑﻦ ﺣﺠﺮ،
ﻭﻫﻠﺐ ﺍﻟﻄﺎﺋﻲ ﻣﺎ ﻳﺪﻝ ﻋﻠﻰ ﺫﻟﻚ. ﺍﻣﺎ ﺍﻹﺭﺳﺎﻝ ﻓﻼ
ﺩﻟﻴﻞ ﻋﻠﻴﻪ، ﺑﻞ ﻫﻮ ﺧﻼﻑ ﺍﻟﺴﻨﺔ)).
Ma’ana: ((Wannan makruhi ne,
abin da yake Sunnah: Taro su da
sanya su a kan kirji, da kuma
sanya dama a kan tafin hagu da
wuyan hannu, da dantse, saboda
ya tabbata daga Annabi mai tsira
da amincin Allah daga hadithin
Sahl Dan Sa’ad, da Waa’il Dan
Hujur, da Hulb Attaa’ii abin da yake
nuna hakan. Amma sake hannaye
babu wani dalil a kansa, kai a
gaskiya ma shi sabanin Sunnah
ne)).
(5) Idan wani ya ce: Ko a cikin
shugabannin Mazhabar Imam
Malik akwai wadanda ke ganin
cewa da zarar an samu wata
fatawa a cikin Mazhabar
malikiyyah wacce ta saba wa
sahihiyar sunnar Manzon Allah, to,
a yi watsi da ita, a koma a yi riko
da sahihiyar sunnar Manzon Allah
mai tsira da amincin Allah kawai?
Amsa a nan ita ce: Lalle akwai su
da yawa, a gaskiya ma ni babu
wani shahararre daga cikinsu da
na sani yake cewa: Bayan
Bamalike ya fahimci cewa
sahihiyar Sunnah ta saba wa
malikancinsa ya yi watsi da
sahihiyar Sunnar ya cigaba da yin
aiki da abin da ya zo cikin
mazhabarsa kawai!! Ni ban san
wani mash’huri da ya fidi irin
wannan magana mara kan gado
ba. Gaskiyan lamari shi ne: Abin
da shugabannin mazhaba suke
cewa shi ne: Duk lokacin da wani
kaulin mazhaba ya yi karo da
sahihiyar Sunnah to sai a jingine
mazhabar a yi aiki da sahihiyar
Sunnah. Imam Malik da kansa
yana cewa kamar yadda ya zo
cikin littafin Tartiibul Madaarik
1/182:-
(( ﺍﻧﻤﺎ ﺍﻧﺎ ﺑﺸﺮ ﺃﺧﻄﺊ ﻭﺃﺻﻴﺐ، ﻓﺎﻧﻈﺮﻭﺍ ﻓﻲ ﺭﺃﻳﻲ
ﻓﻜﻞ ﻣﺎ ﻭﺍﻓﻖ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ ﻓﺨﺬﻭﻩ، ﻭﻛﻞ ﻣﺎ ﻟﻢ
ﻳﻮﺍﻓﻖ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ ﻓﺎﺗﺮﻛﻮﻩ )).
Ma’ana: ((Ni ba kowa ba ne face
mutum, ina yin kure kuma ina yin
daidai, sai ku rika yin nazari cikin
ijtihadina, dukkan abin da ya dace
da Alkur’ani da Sunnah sai ku rike
shi, kuma dukkan abin da bai dace
da Alkur’ani da Sunnah ba sai ku
bar shi)).
Sannan babban malami Jamaalud
Dinil Qaasimii ya ce cikin littafinsa:
Attahdiithu Fi Fununi Mustalahil
Hadith shafi na 245, da babban
malami Saalih Bin Muhammad
Alfullaanii cikin littafinsa: Iiqaazu
Himami Ulil Absar shafi na 89:
dukkansu biyun sun ce: Babban
malami cikin mazhabar Malikiyyah
Muhammad Almaqqarii ya ce cikin
littafinsa na Qwa’idul Fiqhi:-
(( ﻻ ﻳﺠﻮﺯ ﺍﺗﺒﺎﻉ ﻇﺎﻫﺮ ﻧﺺ ﺍﻻﻣﺎﻡ ﻣﻊ ﻣﺨﺎﻟﻔﺘﻪ
ﻷﺻﻮﻝ ﺍﻟﺸﺮﻳﻌﺔ ﻋﻨﺪ ﺣﺬﺍﻕ ﺍﻟﺸﻴﻮﺥ. ﻗﺎﻝ ﺍﻟﺒﺎﺟﻲ :
ﻻ ﺍﻋﻠﻢ ﻗﻮﻻ ﺍﺷﺪ ﺧﻼﻓﺎ ﻋﻠﻰ ﻣﺎﻟﻚ ﻣﻦ ﺍﻫﻞ
ﺍﻻﻧﺪﻟﺲ؛ ﻻﻥ ﻣﺎﻟﻜﺎ ﻻ ﻳﺠﻴﺰ ﺗﻘﻠﻴﺪ ﺍﻟﺮﻭﺍﺓ ﻋﻨﻪ ﻋﻨﺪ
ﻣﺨﺎﻟﻔﺘﻬﻢ ﺍﻷﺻﻮﻝ ﻭﻫﻢ ﻻ ﻳﻌﺘﻤﺪﻭﻥ ﻋﻠﻰ ﺫﻟﻚ.
ﺍﻧﺘﻬﻰ. ﻭﻗﺎﻝ ﺃﻳﻀﺎ: ﻗﺎﻋﺪﺓ: ﻻ ﻳﺠﻮﺯ ﺭﺩ ﺍﻷﺣﺎﺩﻳﺚ
ﺍﻟﻰ ﺍﻟﻤﺬﻫﺐ ﻋﻠﻰ ﻭﺟﻪ ﻳﻨﻘﺺ ﻣﻦ ﺑﻬﺠﺘﻬﺎ ﻭﻳﺬﻫﺐ
ﺑﺎﻟﺜﻘﺔ ﺑﻈﺎﻫﺮﻫﺎ؛ ﻓﺎﻥ ﺫﻟﻚ ﻓﺴﺎﺩ ﻟﻬﺎ ﻭﺣﻂ ﻣﻦ
ﻣﻨﺰﻟﺘﻨﺎ، ﻻ ﺍﺻﻠﺢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻤﺬﻫﺐ ﻟﻔﺴﺎﺩﻫﺎ، ﻭﻻ ﺭﻓﻌﻬﺎ
ﺑﺨﻔﺾ ﺩﺭﺟﺎﺗﻬﺎ، ﻓﻜﻞ ﻛﻼﻡ ﻳﺆﺧﺬ ﻣﻨﻪ ﻭﻳﺮﺩ ﺍﻻ ﻣﺎ
ﺻﺢ ﻟﻨﺎ ﻋﻦ ﻣﺤﻤﺪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ، ﺑﻞ ﻻ
ﻳﺠﻮﺯ ﺍﻟﺮﺩ ﻣﻄﻠﻘﺎ؛ ﻻﻥ ﺍﻟﻮﺍﺟﺐ ﺍﻥ ﺗﺮﺩ ﺍﻟﻤﺬﺍﻫﺐ
ﺍﻟﻴﻬﺎ )).
Ma’ana: ((Bai halatta bin zahirin
nassin Imami tare da sabawarsa
ga jigogin Shari’ah (Qur’ani da
Hadithi) a wurin korarrun
Shaihunai. (Imam) Baajii ya ce:
Ban san wani kauli da ya fi
tsananin saba wa Malik ba kamar
(kaulin) mutanen Andulus ba,
saboda Malik ba ya halattar da bin
masu ruwaya daga gare shi ba a
lokacin da suka saba wa Jigogi, su
ba sa dogara a kan haka. Intaha.
Sannan (Imam Baajii) ya sake
cewa: Qaa’idah: Bai halatta a yi
raddin Hadithai zuwa ga mazhaba
ta fiskar da zai rage wani abu na
armashinsu, kuma ya tafiyar da
amincewa da zahirinsu, domin
hakan bata su ne da kuma
wulakanta matsayinsu. Kada Allah
Ya kyautata mazhabobi ta hanyar
bacinsu (watau su hadithan) kada
(Allah Ya daukaka mazhabobin) ta
hanyar karya darajarsu (su
hadithan). Dukkan wata magana
Ana iya aiki da ita, ana kuma iya
yin watsi da ita, amma banda abin
da ya inganta a wurinmu daga
Muhammad mai tsira da amincin
Allah, ko kadan bai halatta a yi
raddin (maganarsa), domin abin da
ke wajibi shi ne: Yin raddin
mazhabobi zuwa gare ta)) (watau
maganar Annabi mai tsira da
amincin Allah).
(6) Idan wani ya ce: Dalilan nan
duka da ka kawo na cewa: dora
dama a kan hagu cikin salla shi ne
Sunnah, sake hannaye kuwa
sabanin Sunnah ne, wasu mutane
za su ce ba su gamsu da su ba,
hasali ma za su ce dukkan
hadithan masu rauni ne, saboda
haka yin salla hannaye a sake shi
ne daidai domin shi ne abin da
suka sani a mazhabar Malikiyya!!!
To, sai a ce da shi: Na farko dai da
ma ba dukkan gaskiyar da masu
wa’azi ke fada ba ne mutane ke
karba, Annabawa da Manzanni
sun gaya wa jama’arsu gaskiya,
amma an samu mutane da yawa
wadanda suka karyata su, suka yi
watsi da gaskiyar da suka fada
musu. Wannan shi ya sa za ka ga
‘yan bidi’ah da yawa suna karyata
ingantattun hadithan Buhari da
Muslim suka ruwaito cikin
sahihansu, matukar dai hadithan
sun saba wa abin da Dagutansu
suka dora su a kan shi iyazan
billah!
A bu na biyu shi ne: Ciwon son
zuciya na da wahalar waraka,
wannan shi ya sa duk yadda masu
wa’azi suka yi kokarin fahimtar da
Kiristoci cewa aqidarsu ta cewa
Allah yana da Da watau Isa, kuma
shi Allah Dayan uku ne! watau: shi
ne Allah Uba, sannan kuma akwai
Allah Da! Sannan kuma akwai
Allah Ruhu Mai tsarki! Duk lokacin
da masu wa’azi suka yi kokarin
fahimtar da su cewa wannan kure
ne bayyananne sai ka ga cewa
suna ta kawo tawilce-tawilce da
wasu shubuhohi domin tabbatar da
ra’ayinsu marar makama da hujja!!
Haka nan in ka dubi yan bidi’ah
nau’i daban-daban da ake da su
cikin Al’ummar Musulmi za ka rika
ganin yadda suke zaburowa da
karfi suna kare son zuciyarsu.
Misali yanzu in ka yi kokarin
fahimtar da batijjane cewa:
aqidarsa ta cewa Salatul Fatihi
saudaya tana daidai da Alkur’ani
sau dari shida wanda wannan
yana nufin ke nan Salatul Fatihi ta
fi Alkur’ani sau dari biyar da casa’in
da tara!! In ka shaida musu cewa
wannan akidah tasu wani nau’i ne
na ilhadi da raina Littafin Allah
Madaukakin Sarki, to nan da nan
za ka ga cewa sun yi ca a kanka
da zage-zage, da bace-bace, kuma
za ka ga cewa sun nace suna ta
yin tawilce-tawilce domin su
tabbatar da son zuciyarsa!!
To amma irin wannan hayaniya ta
yan bidi’ah, da ‘yan bin son zuciya
sam bai kamata ba a ce za ta hana
masu wa’azi ci gaba da shiryar da
Al’ummah zuwa ga sahihiyar
sunnar Annabi mai tsira da amincin
Allah ba.
Muna rokon Allah muna kaskantar
da kai a gabanSa da ya tausaya
Ya nuna mana gaskiya gaskiya ce
Ya ba mu ikon bin ta, Ya kuma
nuna mana karya karya ce Ya ba
mu ikon guje mata. Ameen.

HUKUNCIN MAIDA BUDE TARO KO RUFE SHI DA ADDU'A CIKIN JAM'I(Dr Ibrahim Jalo Jalingo)

KUSKUREN FAHIMTAR NASSIN
ALKUR’ANI KO SUNNAH NA
WASU MUTANE
GAME DA BAYANAN DA
MALAMAI SUKA YI NA
HUKUNCIN MAIDA BUDE TARO
KO RUFE SHI DA ADDU’A CIKIN
JAM’I WATA SUNNAR DA AKE
MAIMAITAWA A KULLUM
‘Yan’uwa Musulmi! Abin da
malaman Sunnah suke cewa shi
ne: A daina rikon bude taro ko rufe
shi da addu’a a matsayin wata
Sunnar da maimaitawa a kullum, ta
yadda imma ba a yi addu’ar ba sai
a rika ganin an bar wata falala mai
yawa ta wuce, alhalin shi wannan
lamari na bude taro da addu’a
babu inda aka ga cewa Annabi mai
tsira da amincin Allah ya yi shi
koda sau daya ne duk kuwa da
cewa yana da damar yin hakan da
yin hakan wani alheri ne, ke nan
malaman Sunnah sun fahimta
daga hakan cewa: Sunnar Annabi
mai tsira da amincin Allah cikin
mas’alar ita ce rashin aikata hakan,
domin kamar yadda daliban ilmi ne
suka san cewa: wani lokaci
Sunnah ta kan kasance ne ta
hanyar bari, wani lokacin kuwa ta
kan kasance ne ta hanyar yi.
Babban Malami a duniyar Sunnah
Shaikhul Islam Ibnu Taimiya -Allah
Ya yi masa rahama- ya ce cikin
littafinsa Majmuu’ul Fataawa
26/172 :-
(( ﻭﺍﻟﺘﺮﻙ ﺍﻟﺮﺍﺗﺐ ﺳﻨﺔ، ﻛﻤﺎ ﺍﻥ ﺍﻟﻔﻌﻞ ﺍﻟﺮﺍﺗﺐ ﺳﻨﺔ،
ﺑﺨﻼﻑ ﻣﺎ ﻛﺎﻥ ﺗﺮﻛﻪ ﻟﻌﺪﻡ ﻣﻘﺘﺾ، ﺍﻭ ﻓﻮﺍﺕ
ﺷﺮﻁ، ﺍﻭ ﻭﺟﻮﺩ ﻣﺎﻧﻊ، ﻭﺣﺪﺙ ﺑﻌﺪﻩ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻘﺘﻀﻴﺎﺕ
ﻭﺍﻟﺸﺮﻭﻁ ﻭﺯﻭﺍﻝ ﺍﻟﻤﺎﻧﻊ ﻣﺎ ﺩﻟﺖ ﺍﻟﺸﺮﻳﻌﺔ ﻋﻠﻰ
ﻓﻌﻠﻪ ﺣﻴﻨﺌﺬ، ﻛﺠﻤﻊ ﺍﻟﻘﺮﺍﻥ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺼﺤﻒ، ﻭﺟﻤﻊ
ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻲ ﺍﻟﺘﺮﺍﻭﻳﺢ ﻋﻠﻰ ﺍﻣﺎﻡ ﻭﺍﺣﺪ، ﻭﺗﻌﻠﻢ ﺍﻟﻌﺮﺑﻴﺔ
ﻭﺃﺳﻤﺎﺀ ﺍﻟﻨﻘﻠﺔ ﻟﻠﻌﻠﻢ، ﻭﻏﻴﺮ ﺫﻟﻚ ﻣﻤﺎ ﻳﺤﺘﺎﺝ ﺍﻟﻴﻪ ﻓﻲ
ﺍﻟﺪﻳﻦ، ﺑﺤﻴﺚ ﻻ ﺗﺘﻢ ﺍﻟﻮﺍﺟﺒﺎﺕ ﺍﻭ ﺍﻟﻤﺴﺘﺤﺒﺎﺕ
ﺍﻟﺸﺮﻋﻴﺔ ﺍﻻ ﺑﻪ، ﻭﺍﻧﻤﺎ ﺗﺮﻛﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﻟﻔﻮﺍﺕ ﺷﺮﻃﻪ ﺍﻭ ﻭﺟﻮﺩ ﻣﺎﻧﻊ. ﻓﺄﻣﺎ ﻣﺎ ﺗﺮﻛﻪ ﻣﻦ
ﺟﻨﺲ ﺍﻟﻌﺒﺎﺩﺍﺕ ﻣﻊ ﺍﻧﻪ ﻟﻮ ﻛﺎﻥ ﻣﺸﺮﻭﻋﺎ ﻟﻔﻌﻠﻪ ﺍﻭ
ﺍﺫﻥ ﻓﻴﻪ ﻭﻟﻔﻌﻠﻪ ﺍﻟﺨﻠﻔﺎﺀ ﺑﻌﺪﻩ ﻭﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ، ﻓﻴﺠﺐ
ﺍﻟﻘﻄﻊ ﺑﺎﻥ ﻓﻌﻠﻪ ﺑﺪﻋﺔ ﻭﺿﻼﻟﺔ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Dawwamanmen bari
Sunnah ce, kamar yadda
dawwamanmen aiki yake Sunnah,
sabanin abin da barin shi ya
kasance ne saboda rashin bukatar
yin shi, ko kuwa saboda rashin
sharadin yin shi, ko kuwa saboda
samuwar abin da ya hana yin shi,
sannan bayan (mutuwar Annabi)
bukatar yin hakan ta taso, ko
sharadin yin hakan ya samu, ko
abin da ke hana yin hakan ya kau,
ta yadda Shari’ah za ta nuna
halaccin yin shi, kamar hada
Alkur’ani a Mus’hafi, da hada
mutane bayan limami daya a cikin
sallar tarawihi, da koyon ilmin
Larabci, da haddace sunayen
masu nakalto ilmi, da wanin
wannan daga cikin abin da ake
bukatarsa cikin Addini, ta yadda
wajibai da mustahabbai na
Shari’ah ba sa cika sai tare da shi,
saboda da ma can (Manzon Allah)
mai tsira da amincn Allah ya bar
yin shi ne saboda kubucewar
sharadinsa, ko saboda samuwar
abin da ke hana yin shi. To amma
abin da (Annabi) ya bari daga
jinsin Ibadu tare da cewa da abin
wani abu ne da ya dace da
Shari’ah to da ya aikata shi, ko da
ya ba da izinin a yi shi, kuma da
ma Khalifofinsa da Sahabbai sun yi
shi a bayansa, (irin wannan kam)
wajibi ne a tabbatar da cewa lalle
yin shi bidi’ah ce kuma bata)).
Intaha.
Da wannan magana ta Shaikhul
Islam Ibnu Taimiya za mu fahimci
cewa: Sunnar Annabi mai tsira da
amincin Allah cikin bude taro ko
rufe taro da addu’ah ita ce: Barin
yin hakan, saboda masu yin haka
suna ganin wata ibada suke yi
saboda su samu biyan bukatar
Duniya da Lahira, wannan shi ya
sa ma in sun ga wasu sun yi taro
ba su yi ba sai su rika jin
haushinsu, kai su ma rika zaginsu
da yi musu jumhuru daban
daban!!!
RADDI:-
Idan wani ya kafa hujja da hadithin
Abdullahi Dan Umar wanda Tirmizi
ya ruwaito cikin Sunan hadithi na
3,502, da kuma Nasaa’i cikin
Sunan hadithi na 10,234 cewa:-
(( ﻗﻠﻤﺎ ﻛﺎﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﻘﻮﻡ
ﻣﻦ ﻣﺠﻠﺲ ﺣﺘﻰ ﻳﺪﻋﻮ ﺑﻬﺆﻻﺀ ﺍﻟﺪﻋﻮﺍﺕ ﻷﺻﺤﺎﺑﻪ :
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻗﺴﻢ ﻟﻨﺎ ﻣﻦ ﺧﺸﻴﺘﻚ ﻣﺎ ﺗﺤﻮﻝ ﺑﻪ ﺑﻴﻨﻨﺎ ﻭﺑﻴﻦ
ﻣﻌﺎﺻﻴﻚ، ﻭﻣﻦ ﻃﺎﻋﺘﻚ ﻣﺎ ﺗﺒﻠﻐﻨﺎ ﺑﻪ ﺟﻨﺘﻚ، ﻭﻣﻦ
ﺍﻟﻴﻘﻴﻦ ﻣﺎ ﺗﻬﻮﻥ ﺑﻪ ﻣﺼﺎﺋﺐ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ، ﻭﻣﺘﻌﻨﺎ
ﺑﺎﺳﻤﺎﻋﻨﺎ ﻭﺍﺑﺼﺎﺭﻧﺎ ﻭﻗﻮﺗﻨﺎ ﻣﺎ ﺍﺣﻴﻴﺘﻨﺎ، ﻭﺍﺟﻌﻠﻪ
ﺍﻟﻮﺍﺭﺙ ﻣﻨﺎ، ﻭﺍﺟﻌﻞ ﺛﺎﺭﻧﺎ ﻋﻠﻰ ﻣﻦ ﻇﻠﻤﻨﺎ،
ﻭﺍﻧﺼﺮﻧﺎ ﻋﻠﻰ ﻣﻦ ﻋﺎﺩﺍﻧﺎ، ﻭﻻ ﺗﺠﻌﻞ ﻣﺼﻴﺒﺘﻨﺎ ﻓﻲ
ﺩﻳﻨﻨﺎ، ﻭﻻ ﺗﺠﻌﻞ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﺍﻛﺒﺮ ﻫﻤﻨﺎ ﻭﻻ ﻣﺒﻠﻎ ﻋﻠﻤﻨﺎ،
ﻭﻻ ﺗﺴﻠﻂ ﻋﻠﻴﻨﺎ ﻣﻦ ﻻ ﻳﺮﺣﻤﻨﺎ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Kadan ne za a ce
Mnazon Allah mai tsira da amincin
Allah ya tashi daga wata majalisa
ba tare da ya yi wa Sahabbansa
addu’a da wadannan addu’o’i ba:
Ya Allah Ka ba mu wani abu na
tsoronKa da zai shiga tsakaninmu
da sabonKa, da wani abu na
da’arKa da zai kai mu aljannarKa,
da wani abu na yakini da zai kai
saukaka mana musibun Duniya, ka
jiyarda mu dadi da jinmu, da
ganinmu, da karfinmu matukar dai
Ka rayar da mu, Ka zamar da shi
mai gado gare mu, Ka sanya
ramuwar gayyarmu a kan wanda
ya zalunce mu, Ka taimake mu a
kan wanda ya nuna mana kiyayya,
kada Ka sanya musibarmu a cikin
addininmu, kada Ka sanya Duniya
mafi girman hamminmu, ko iya
matukar ilminmu, kada Ka dora
wanda ba ya tausaya mana a
kanmu)). Intaha.
Idan wani ya kafa hujja da wannan
hadithin to sai a ce da shi: Shi
wannan hadithin abin da kawai ya
ce shi ne: “Yan lokuta kadan ne za
ce Annabi ya tashi daga wata
majalisa ba tare da ya yi wa
sahabbansa addu’a ba” hadithin
bai ce Annabi yana ce wa
sahabbansa ne: ku yi salati goma-
goma sannan ya rika yin addu’a su
kuma suna cewa: ameen ba!!!
Babu wani magabaci da ya yi wa
hadithin wannan fahimta, babu
kuma wani malami daga cikin
masu yi wa hadithai sharhi -a iya
sanina- da ya yi wa hadithin
wannan fahimta, babu daya daga
cikin maluman Da’awah da Aqidah
da ya yi wa hadithin wannan
fahimta!!! Sannan ko shakka babu
da da wannan surar ce Annabi
yake yin addu’ar to da an nakalto
mana ita, saboda sura ce mai jan
hankulan mutane sosai, domin
kowa ya kan bar abin da yake yi ne
domin ya saurari mai yin addu’a
bayan ya yi salati sannan kuma ya
rika fadar ameen.
Sannan a cikin hadithin an ce:-
(( ﻣﻦ ﻣﺠﻠﺲ))
Watau: daga ma ko wace majlisa.
Ke nan wannan ya hada da
majalisar tattauna lamuran duniya
na yau da gobe, da majalisar wani
darasi, da majalisar koma mene
ne. In da kuwa lalle yana yin
addu’ar ne a bisa surar da muke yi,
to da kuwa an nakalto mana ita.
Sannan kuma da Malumanmu na
Da’awah da Aqidah ba su hana yin
addu’a cikin irin ita wannan surar
ba a farko ko karshen majalisar
wani darasi, ko majalisar karatun
Kur’ani ba, da sauransu.
Sannan abu na biyu shi ne: Mene
ne ya hada tsakanin cewa Annabi
yana yi wa Sahabbansa addu’a
cikin mafi yawan majalisu, da
kuma cewa Annabi yana addu’ar
bude taro da rufe taro cikin jam’i, in
ba ta’assubanci da son zuciya ba?
Ga misali: Abu Dawuda ya ruwaito
hadithi na 3,203, da Tirmizi hadithi
na 1,024, da Nasa’ii hadithi na
1,986’ da Ibnu Majah hadithi na
1,498, da Ahmad hadithi na 17,581
daga Sahabi Abu Hurairah da
waninsa cewa Annabi mai tsira da
amincin Allah ya kasance yana yi
wa Sahabbai rayayyu da matattu
maza da mata manya da yara
addu’a cikin sallar janaza. Ga ma
yadda nassin yake:-
(( ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﺤﻴﻨﺎ ﻭﻣﻴﺘﻨﺎ ﻭﺻﻐﻴﺮﻧﺎ ﻭﻛﺒﻴﺮﻧﺎ
ﻭﺫﻛﺮﻧﺎ ﻭﺍﻧﺜﺎﻧﺎ ﻭﺷﺎﻫﺪﻧﺎ ﻭﻏﺎﺋﺒﻨﺎ. ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻣﻦ ﺍﺣﻴﻴﺘﻪ
ﻣﻨﺎ ﻓﺎﺣﻴﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻻﻳﻤﺎﻥ ﻭﻣﻦ ﺗﻮﻓﻴﺘﻪ ﻣﻨﺎ ﻓﺘﻮﻓﻪ ﻋﻠﻰ
ﺍﻻﺳﻼﻡ. ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻻ ﺗﺤﺮﻣﻨﺎ ﺍﺟﺮﻩ ﻭﻻ ﺗﻀﻠﻨﺎ ﺑﻌﺪﻩ .((
ﺍﻧﺘﻬﻰ.
Ma’ana: ((Ya Allah Ka gafarta wa
rayayyunmu da matattunmu, da
kanananmu da manyanmu, da
mazanmu da matanmu, da
halartattunmu da wadanda ba sa
nan daga cikinmu. Ya Allah wanda
Ka raya shi daga cikinmu to Ka
raya shi a kan Imani, Wanda kuma
Ka matar daga cikinmu to Ka matar
da shi a kan Musulunci. Ya Allah
kada Ka haramta mana ladansa,
kada kuma Ka batar da mu
bayansa)). Intaha.
A nan addu’a ce da Annabi yake yi
wa Sahabbansa, rayayyu da
matattu, amma kuma shi kadai
yake yin ta ba ma dole ba ne
jama’ar da ke tare da shi su abin
da yake fada, kuma babu salatin
Annabi goma-goma a cikinta, babu
kuma fadar ameen daga sauran
jama’a. Lalle yadda ita wannan
addu’ar take to haka ma addu’ar:-
(( ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻗﺴﻢ ﻟﻨﺎ ﻣﻦ ﺧﺸﻴﺘﻚ ﻣﺎ ﺗﺤﻮﻝ ﺑﻪ ﺑﻴﻨﻨﺎ ﻭﺑﻴﻦ
ﻣﻌﺎﺻﻴﻚ……)).
take, wannan shi ya sa ma su
wadannan kalmomi ba sa canja
wa, kamar yadda wadancan su ma
ba sa canjawa.
Sannan abu na biyu shi ne: Akwai
gurare da yawa da Annabi mai
tsira da amincin Allah yake yi wa
Sahabbai addu’a, to amma
maluman Sunnah ba su fahimci
cewa addu’ar jam’i ne yake yi ba.
Misali:-
1-Hadithi na 5108 da Abu Dawud
ya ruwaito, na 4623 da Abu Ya’ala
ya ruwaito cikin Musnad, na 140 da
Ibnul Jaaruud ya ruwaiton cikin
Muntaqa daga A’isha Allah Ya kara
mata yarda ta ce:-
((ﻛﺎﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﺆﺗﻰ
ﺑﺎﻟﺼﺒﻴﺎﻥ ﻓﻴﺪﻋﻮ ﻟﻬﻢ ﺑﺎﻟﺒﺮﻛﺔ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Manzon Allah mai tsira
da amincin Allah ya kasance ana
zuwa masa da yara yana musu
addu’ar samun albarka)). Intaha.
Wannan hadithin Albanii ya
inganta shi cikin Alkalimut Tayyib
1/162. Lalle a nan hadthin ba ya
nufin jam’in addu’a Annabi yake yi
watau ya umurci mutane su daga
hannu suna cewa Ameen shi kuwa
yana Ddu’a.
2-Hadithi na 502 da Bukharii ya
ruwaito cikin Al’adabul Mufrad, da
hadithi na 9969 da Baihaqii ya
ruwaito cikin Shu’abul Iman cewa:-
(( ﺟﺎﺀﺕ ﺍﻟﺤﻤﻰ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﻓﻘﺎﻟﺖ: ﺍﺑﻌﺜﻨﻲ ﺍﻟﻰ ﺍﺛﺮ ﺍﻫﻠﻚ ﻋﻨﺪﻙ. ﻓﺒﻌﺜﻬﺎ ﺍﻟﻰ
ﺍﻷﻧﺼﺎﺭ ﻓﺒﻘﻴﺖ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﺳﺘﺔ ﺍﻳﺎﻡ ﻭﻟﻴﺎﻟﻴﻬﻦ ﻓﺎﺷﺘﺪ
ﺫﻟﻚ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﻓﺎﺗﺎﻫﻢ ﻓﻲ ﺩﻳﺎﺭﻫﻢ ﻓﺸﻜﻮﺍ ﺫﻟﻚ ﺍﻟﻴﻪ،
ﻓﺠﻌﻞ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﺪﺧﻞ ﺩﺍﺭﺍ ﺩﺍﺭﺍ
ﻭﺑﻴﺘﺎ ﺑﻴﺘﺎ ﻳﺪﻋﻮ ﻟﻬﻢ ﺑﺎﻟﻌﺎﻓﻴﺔ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Zazzabi ya zo gurin
Annabi mai tsira da amincin Allah
sai ya ce: aika ni zuwa ga mutanen
da suka fi soyuwa gare ka. Sai ya
aika da shi zuwa ga Ansarawa, ya
je ya zauna a cikinsu yini shida da
dare shida, hakan ya tsananta a
kansu, sai ya je musu cikin
unguwarsu, sai suka yi masa
kukan wannan zazzabin. Sai
Annabi mai tsira da amincin Allah
ya rika shiga bangare bangare,
gida gida yana musu addu’ar
samun lafiya)). Intaha. Wannan
hadithin Albaanii ya inganta shi
cikin Silsilah Sahihah lamba na:
2502. A nan ma babu wani mai
sharhin hadithai da ya ce addu’ar
jam’i aka yi Annabi na addu’a
saura jama’a na cewa: ameen.
3-Hadithi na 1668 da Malik ya
ruwaito cikin Muwattaa, da hadithi
na 17,959 da Tabaraanii ya
ruwaito cikin Almu’ujamul Kabir, da
hadithi na 9,503 da Abdur Razzaq
ya ruwaito cikin Musannaf daga
Abu Burdah cewa:-
(( ﺍﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﻮﻡ ﺣﻨﻴﻦ ﺃﺗﻰ
ﺍﻟﻘﺒﺎﺋﻞ ﻳﺪﻋﻮ ﻟﻬﻢ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Annabi mai tsira da
amincin Allah ya je wa Kabilu a
ranar yakin Hunain yana musu
addu’a)). Intaha. Mai littafin
Majma’uz Zawaa’id 5/407 ya ce:
Mazajen isnadin Mazajen Buharii
da Muslim ne, in banda Abdullahi
Ibnul Mugiirah shi kuwa thiqah ne.
A nan ma babu wanda ya ce
Annabi ya je yana addu’ar ne
sannan ya umurci Kabilun da su
rika cewa: ameen.
4- Hadithi na 4,546 da Haakim ya
ruwaito cikin Mustadrak daga
Waliid Dan Uqbah cewa:-
(( ﻟﻤﺎ ﻓﺘﺢ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻣﻜﺔ
ﺟﻌﻞ ﺍﻫﻞ ﻣﻜﺔ ﻳﺄﺗﻮﻥ ﺑﺼﺒﻴﺎﻧﻬﻢ ﻓﻴﻤﺴﺢ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻋﻠﻰ ﺭﺅﻭﺳﻬﻢ ﻭﻳﺪﻋﻮ ﻟﻬﻢ .((
ﺍﻧﺘﻬﻰ.
Ma’ana: ((Lokacin da Manzon Allah
mai tsira da amincin Allah ya bude
Makka, mutanen Makka sun yi ta
kawo yaransu Manzon Allah yana
ta shafan kawunansu yana musu
addu’a)). Intaha. A nan ma babu
wani mai sharhin hadithi da ya ce:
Annabi ya ce su yi ta cewa ameen
ne a lokacin da yake yi wa yaran
nasu addu’a. watau babu wanda
ya ce addu’ar jam’i Annabi ya yi.
AMSA KAN WATA MAGANAR
KUMA
Idan wani ya kafa hujja da
wadannan Nassosi kamar:-
(( ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ ﺟﺎﺀﻭﺍ ﻣﻦ ﺑﻌﺪﻫﻢ ﻳﻘﻮﻟﻮﻥ ﺭﺑﻨﺎ ﺃﻏﻔﺮﻟﻨﺎ
ﻭﻻﺧﻮﺍﻧﻨﺎ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺳﺒﻘﻮﻧﺎ ﺑﺎﻹﻳﻤﺎﻥ.(( ﺍﻟﺤﺸﺮ:١٠ .
Ma’ana: ((Wadanda suka zo daga
bayansu suna cewa: Ya
Ubangijinmu! Ka gafarta mana, da
kuma ‘yan’uwanmu wadanda suka
riga mu yin Imani)). Intaha. Da
kuma:-
(( ﻗﻞ ﻣﺎ ﻳﻌﺒﺆ ﺑﻜﻢ ﺭﺑﻲ ﻟﻮﻻ ﺩﻋﺎﺅﻛﻢ.(( ﺍﻟﻔﺮﻗﺎﻥ:
٧٧.
Ma’ana: ((Ka ce: Ubangijina ba ya
kulawa da ku, in ba domin
addu’arku ba)). Intaha. Da kuma:-
(( ﻭﺍﺫﺍ ﺳﺎﻟﻚ ﻋﺒﺎﺩﻱ ﻋﻨﻲ ﻓﺎﻧﻲ ﻗﺮﻳﺐ ﺃﺟﻴﺐ ﺩﻋﻮﺓ
ﺍﻟﺪﺍﻉ ﺍﺫﺍ ﺩﻋﺎﻥ.(( ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ: ١٨٦ .
Ma’ana: ((Idan bayiNa suka
tambaye ka labariNa to Ni kusa
Nake, kuma ina amsa addu’ar mai
addu’a in ya kira Ni)). Intaha. Da
kuma sauran Nassosi masu kama
da haka ya ce kuma: Lalle mu
muna hana a yi sa Musulmi addu’a
ne, alhalin Allah Ya ce a roke Shi
zai kuma amsa!!!
Farko dai sai a ce da su tarihi ne
yake maimaita kan sa, tsakanin
maluman Sunnah da kuma masu
bidi’a da bautar son zuciya. Misali:
lokacin da Shehu Uthmanu Dan
Fodiyo ya ce cikin littafin shi
Ihya’us Sunnah shafi na 102:-
(( ﻭﻣﻦ ﺫﻟﻚ ﺍﻟﺪﻋﺎﺀ ﺩﺑﺮ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﺑﻜﻴﻔﻴﺔ ﻣﻌﻠﻮﻣﺔ
ﻭﻫﻮ ﺍﻥ ﻳﺪﻋﻮ ﺍﻻﻣﺎﻡ ﻭﻳﺆﻣﻦ ﺍﻟﻨﺎﺱ، ﻭﻫﻮ ﺑﺪﻋﺔ
ﻣﻜﺮﻭﻫﺔ ﻓﻲ ﻣﺬﻫﺐ ﻣﺎﻟﻚ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Daga cikin wannan
akwai addu’a bayan Salla a bisa
wani yanayi sananne, shi ne kuwa:
Liman yana addu’a Mamu suna
cewa ameen. Shi wannan bidi’a ce
makruuhiya a cikin mazhabar
Imam Malik)). Intaha. A lokacin da
Shehu Dan Fodiyo da kuma ire-
irensa suka fadi haka saboda
neman jama’a su yi Musuluncisu
kamar yadda Annabi da Sahabbai
suka yi an samu wasu masu
ta’assubanci wadanda kiyayya da
hasada suka cika zukatansu, da
suka ki yin aiki da wannan bayani
na ilmi da so wa Musulmi alheri,
suka koma suna ta kafa hujja da
irin wadannan dalilai aammah,
wadanda masu ilmi sun san cewa
ba za nuni a kan bigiren da aka yi
sabani a kan shi. Kamar dai
mutumin da za ka ce da shi: ka
daina yin Salatul fatih ka rika yin
Salatin da Annabi mai tsira da
amincin Allah ya koya wa
Sahabbai. Sannan shi kuma ya
rika gaya wa jama’a cewa: Kai din
nan ka hana a rika yi wa Annabi
salati!!! Ko kuma ka ce a daina
zikirin bidi’ah na ihu da bugun kirji,
ko bisa wani adadi wanda ba
Shari’a ce ta bayyana ba. Sai kuma
a ce: Kai din nan wai ka hana a yi
wa Allah zikiri duk kuwa da cewa
Nasosi da yawa sun yi umurni da
yin hakan!!
Na biyu sai a ce da su: Irin wannan
tuhumar ba sabon lamari ba ne ga
Maluma masu da’awah wadanda
suke kokarin maida mutane a kan
Sunnar Annabi mai tsira da
amincin Allah cikin dukkan
lamuransu. Imam Abdur Razzaq ya
ruwaito cikin littafinsa Musannaf
atharii na 4,755 da kuma Imamul
Baihaqii a cikin Assunanul Kubra
atharii na 4,621 daga Sa’id Dan
Musayyib cewa:-
((ﺍﻧﻪ ﺭﺃﻯ ﺭﺟﻼ ﻳﺼﻠﻲ ﺑﻌﺪ ﻃﻠﻮﻉ ﺍﻟﻔﺠﺮ ﺍﻛﺜﺮ ﻣﻦ
ﺭﻛﻌﺘﻴﻦ ﻳﻜﺜﺮ ﻓﻴﻬﺎ ﺍﻟﺮﻛﻮﻉ ﻭﺍﻟﺴﺠﻮﺩ، ﻓﻨﻬﺎﻩ، ﻓﻘﺎﻝ:
ﻳﺎ ﻣﺤﻤﺪ! ﻳﻌﺬﺑﻨﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺼﻼﺓ؟ ﻗﺎﻝ: ﻻ ﻭﻟﻜﻦ
ﻳﻌﺬﺑﻚ ﻋﻠﻰ ﺧﻼﻑ ﺍﻟﺴﻨﺔ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Ya ga wani mutum yana
salla fiye da raka’a biyu bayan
fitowar alfijir yana yawaita ruku’i da
sujjada cikin sallar, sai ya hana
shi. Sai mutumin ya ce: Ya Abu
Muhammad! Yanzu a kan salla ne
Allah zai azabtar da ni? Sai ya ce:
A’a zai azabtar da kai ne a kan
sabawa Sunnah)). Intaha. Sheik
Albani bayan ya kawo wannan
magana cikin littafinsa Irwa’ul Galil
2/236 kuma ya inganta isnadinta
sai ya ce:-
(( ﻭﻫﺬﺍ ﻣﻦ ﺑﺪﺍﺋﻊ ﺃﺟﻮﺑﺔ ﺳﻌﻴﺪ ﺑﻦ ﺍﻟﻤﺴﻴﺐ ﺭﺣﻤﻪ
ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ، ﻭﻫﻮ ﺳﻼﺡ ﻗﻮﻱ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﺒﺘﺪﻋﺔ ﺍﻟﺬﻳﻦ
ﻳﺴﺘﺤﺴﻨﻮﻥ ﻛﺜﻴﺮﺍ ﻣﻦ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﺑﺎﺳﻢ ﺍﻧﻬﺎ ﺫﻛﺮ
ﻭﺻﻼﺓ، ﺛﻢ ﻳﻨﻜﺮﻭﻥ ﻋﻠﻰ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺍﻧﻜﺎﺭ ﺫﻟﻚ
ﻋﻠﻴﻬﻢ، ﻭﻳﺘﻬﻤﻮﻧﻬﻢ ﺑﺎﻧﻬﻢ ﻳﻨﻜﺮﻭﻥ ﺍﻟﺬﻛﺮ ﻭﺍﻟﺼﻼﺓ !!
ﻭﻫﻢ ﻓﻲ ﺍﻟﺤﻘﻴﻘﺔ ﺍﻧﻤﺎ ﻳﻨﻜﺮﻭﻥ ﺧﻼﻓﻬﻢ ﻟﻠﺴﻨﺔ ﻓﻲ
ﺍﻟﺬﻛﺮ ﻭﺍﻟﺼﻼﺓ ﻭﻧﺤﻮ ﺫﻟﻚ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Wannan yana daga cikin
kyawawan jawaban Sa’idu Dan
Musayyib Allah Madaukakin Sarki
Ya yi masa rahama, sannan kuma
shi makami ne mai karfi a kan ‘yan
bidi’a da suke ganin kyawun da
yawa daga cikin bidi’o’i da sunan
cewa: Ai zikiri ne, da Salla! Sannan
kuma su yi wa Ahlus Sunnah
inkarin inkarin da suke yi musu,
kuma su tuhumce su da cewa:
Suna hana zikirin Allah da kuma
Salla!! Wanda kuma a gaskiyar
al’amari su suna musu inkarin
barin Sunnah ne da suka yi cikin
Zikirin da kuma Sallar, da abin da
ya yi kama da haka)). Intaha.
Muna rokon Allah Madaukakin
Sarki ya nuna mana gaskiya
gaskiya ce ya kuma ba mu ikon
aiki da ita. Ya kuma nuna mana
karya karya ce ya ba mu ikon guje
mata. Ameen.

MAICECE MU'UJIZA ? (DARASI NA FARKO){Mal.Aminu Ibrahim Daurawa}

Abubuwan mamaki da zai iya
faruwa ta hannun dan Adam, gaba
daya kashi goma ne.
Na daya Mu’ujiza ko aya daga
Annabawa.kamar sandar Annabi
musa, ko raya matacce da warkar
da makaho da kuturu ga Annabi
isa, ko bubbugowar ruwa ta
hannun Annabi Muhammad saw.
Na biyu, Irhasat, abin mamaki
dake faruwa ta hannun Annabi
kafin aikoshi da manzanci, kamar
duwatsu da suke yiwa Annabi saw
sallama idan ya wuce ta gabansu
kafin aiko shi.
Na uku, karama, wanda take
faruwa, ta hannun waliyan Allah
kamar sayyadina Umar (ra ) ya
kirawo wani tabii mai suna sariya,
daga tsawon fiye da kilometer
1000, ya kuma jishi ba tare da
amfani da wayar sadarwa ba.
Na hudu Alma’una, shine wata
gudunmawa ta gaggagawa da
Allah yake yiwa wani bawansa
daya shiga wani matsatsi ko
damuwa, kamar yadda yazo a
cikin sharhin akidatul- dahawiyya
na shaik Usaimin, cewa wani
bawan Allah,tsoho ya dorawa
jakinsa kaya, sai jakin ya mutu
kafin zuwa gida sai ya roki Allah
ya rayashi domin ya isar masa da
kayansa zuwa gida, jakin ya tashi,
sai bayan sun isa gida sannan ya
mutu.
Na biyar tsafi wanda yake faruwa
ta hannun matsafa, kamar
matsafan lokacin Annabi musa, da
sukayi fito- na- fito dashi Allah ya
bashi nasara akan su.
Na shida, siddabaru ko rufa-ido,
wanda zakaga masu wasa da
miciji sukeyi, kamar kaga mutum
ya shiga cikin jaki ta jela ya fito ta
baki, ko ya zura allura ta kofar
hanci daya ,ya fito da ita ta kofa
daya.
Na bakwai, Ihana, (wato wulakanci
da kunyatarwa)wanda yake
faruwa ta hannun wanda yayi
daawar Annabta ta karya, kamar
Musailamul kazzab, lokacin da
yaji cewa wani mai ciwon ido yazo
wajen Manzon Allah saw yayi
masa Addu’a ya warke, shima sai
yace akawo masa mai ciwan ido
zaiyi masa Addu’a, da aka kawo
mai ciwon idon,yanayi masa tofi
sai idon ya rufe, ya dena gani
gaba daya.
Na takwas, istidraji, shine abin
mamaki da yake faruwa ta hannun
wanda yayi daawar uluhiyya, wato
matsayin Allantaka, kamar Dujal
wanda zaizo da abubuwan
mamaki, yace ayi ruwa ayi, yace
kasa ta tsage, yaje makabarta
yace matattu su tashi, kuma aga
sun tashi, irin wannan shi ake kira
shigo- shigo ba zurfi, ko talala, ko
jarrabawa, daga Allah domin yaga
zaa bishi, ko zaabi dujal mai ido
daya, wanda da shine Allah da
gaske yaya ya zama mai ido
daya?
Na tara, abubuwan mamaki ta
hanyar koyo, da kwarewa ko wata
baiwa, mutum yana iya zuwa da
abin mamaki wanda sauran
mutane za suyi mamaki, kamar
yadda muke gani, cikin shirye-
shirye na wasanni ko wata bajinta
ta hawa igiya ko nutso a ruwa, ko
kokawa ko daga wani abu mai
nauyi, da sauransu.
Na goma kayan kere- keren
zamani na kimiya da fasaha,
wadanda suke ta fitowa, a baya
babu su, na kayan sadarwa, da
abubuwan hawa,da sauransu, duk
abinda zaka gani daga dan Adam
na mamaki baya fita daga
wadannan abubuwa goma,
Wanda za muyi magana akai itace
mu’ujiza wanda kalmace ta larabci
tana nufin gajiyarwa, wato abinda
ya zama gagara koyo, ko gagara
misaltau, abinda yafi karfin wani
dan Adam wanda ba Annabi ba,
yazo dashi, don haka mu’ujiza
tana nufin wani abin mamaki da
daure kai, wanda Allah yake
gudanar dashi ta hannun Annabi
wanda zai tabbatar da cewa,
sakon da suke dauke dashi daga
wajen Allah yake, kuma ga dalili
akan haka wanda bai yarda ba
shima, yayi irin abinda sukayi ko
yazo da sheda akan haka.
Mu’ujiza ta kasu kashi uku, ko
tana shiga layi uku, duk wata
mu’ujiza ta Annabi, tana zama ko
nuna ilmi, ko wadata, ko iko da isa
wanda yafi karfin tunanin dan
Adam.
Dukkan mu’ujizozin da zamu kawo
na Annabi akan wannan layin
suke, ko, ilmi ko wadata, ko
kudura wato iko da isa.

LAYYAR MUTANE BIYU ZUWA SAMA DA DABBA DAYA(Dr Ibrahim Jalo Jalingo)

‘Yan’uwa masu daraja! Wannan
mas’ala ana kiran ta mas’alar
“Mutane da yawa su hada kudi su
sai dabba daya saboda su yi
Hadaya da ita ko kuwa su yi Layya
da ita”.
To Maluman Musulunci suna da
kauli biyu cikin mas’alar:-
Kaulin farko: Yana halatta mutum
biyu har zuwa bakwai su hada kudi
su sai rakumi guda, ko saniya guda
su yi hadayarsu da ita, ko su yi
layyarsu da ita.
Wannan ita ce mazhabar mafi
yawan malaman Musulunci:
Hanafiyyah, da Shafi’iyyah, da
Hambaliyah, da Zahiriyyah, da
sauransu.
Dubi kadan daga cikin littattafansu:
Almabsuut 12/11, Badaa’i’us
Sanaa’i’i 5/71, da Almajmuu’u
8/398, Raudhatut Taalibiin 2/467,
da Almugnii 5/549, 13/392, Al-
Insaaf 4/76, Al-Fuu3/541.
Hujjarsu ita ce abin da Imam
Muslim ya ruwaito hadithi na 1,318,
da Imam Ahmad hadithi na 14,148,
da Imam Abu Dawud hadithi na
2,807, da Imamut Tirmizii hadithi
na 904, da Imamun Nasaa’ii hadithi
na 4,398, da Imamut Tabraaanii
hadithi na 6,432, da Imamul
Baihaqii cikin As-Sunanul Kubraa
hadithi na 19,710 daga Sahabi
Jabir Dan Abdullahi ya ce:-
((ﺧﺮﺟﻨﺎ ﻣﻊ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﻣﻬﻠﻴﻦ ﺑﺎﻟﺤﺞ ﻓﺎﻣﺮﻧﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﺍﻥ ﻧﺸﺘﺮﻙ ﻓﻲ ﺍﻹﺑﻞ ﻭﺍﻟﺒﻘﺮ ﻛﻞ ﺳﺒﻌﺔ ﻣﻨﺎ ﻓﻲ
ﺑﺪﻧﺔ )).
Ma’ana: ((Mun fita tare da Manzon
Allah mai tsira da amincin Allah
muna masu daga murayarmu da
yin talbiyyar aikin Hajji, sai Manzon
Allah mai tsira da amincin Allah ya
umurce mu da yin tarayya cikin
Rakuma, da Shanu, dukkan mutum
bakwai cikinmu rakumi daya ko
saniya daya)). Intaha.
Kauli na biyu: Ba ya halatta mutum
biyu zuwa sama su hada kudi su
sai rakumi daya ko saniya daya
domin su yi Hadayar wajibi ko
hadayar nafila da ita, ko domin su
yi Layya da ita.
Wannan shi ne Mash’huurin zance
cikin Mazhabar malamanmu na
Malikiyyah.
Dubi kadan daga cikin littattafansu:
Al-Muntaqaa 3/95, Azzakiirah
4/152-153, Alfuruu 1/391.
A gaskiya malumanmu na
Malikiyyah ba su da wata ayah, ko
wani hadithi da ya yi nassi a kan
wannan mazhaba tasu, to amma
wasunsu sun ce madogararsu cikin
wannan mazhaba ita ce: Fadar
Allah Madaukakin Sarki:-
((ﻳﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺍﻣﻨﻮﺍ ﻻ ﺗﻘﺘﻠﻮﺍ ﺍﻟﺼﻴﺪ ﻭﺍﻧﺘﻢ ﺣﺮﻡ
ﻭﻣﻦ ﻗﺘﻠﻪ ﻣﻨﻜﻢ ﻣﺘﻌﻤﺪﺍ ﻓﺠﺰﺍﺀ ﻣﺜﻞ ﻣﺎ ﻗﺘﻞ ﻣﻦ
ﺍﻟﻨﻌﻢ ﻳﺤﻜﻢ ﺑﻪ ﺫﻭﺍ ﻋﺪﻝ ﻣﻨﻜﻢ ﻫﺪﻳﺎ ﺑﺎﻟﻎ ﺍﻟﻜﻌﺒﺔ….)
).
Ma’ana: ((Ya ku wadanda suka yi
imani kada ku kashe farauta alhali
kuna masu harama. Kuma wanda
ya kashe shi daga cikinku bisa
ganganci, sai ya bada sakayyar
misalin abin da ya kashe, cikin
dabbobin ni’imah, masu adalci biyu
daga cikinku ne za su yi masa
hukunci, a matsayin wata hadaya
mai zuwa Dakin Ka’abah…)).
A nan sai suka ce: Tun da Allah ya
wajabta wa mai kashe farauta
bayar da misalin a bin da ya kashe
cikin dabbobin gida na ni’imah
wanda za a kai har Ka’abah a
matsayin hadaya, ke nan idan
muka halattar da haduwar mutum
bakwai a kan rakumi ko saniya
daya, wannan zai kai mu ga cewa:
ko wanne daga cikinsu ya yi
hadaya ne da kashi daya cikin
bakwai na rakumin ko na saniyar!!
Wanda kuma ya fitar da kashi daya
kawai cikin bakwai na rakumi ko
saniya, to lalle wannan bai bayar
da misalin dabbar farauta da ya
kashe ba!!.
A gaskiya wannan hujja da sashin
malamanmu na Malikiyyah suka
fada, lalle yin Kiyasi ne domin
kalubalantar hukuncin da nassi ya
zo da shi karara, wannan kuwa
abu ne da sam bai dace ba. Allah
ya shiryar da mu zuwa ga abin da
yake daidai har kullum.
SAHIHIN HUKUNCI CIKIN
MAS’ALAR:
Sahihiyar magana cikin wannan
mas’ala ita ce: Halal ne mutum
bakwai su hada kudi su sai rakumi
daya ko saniya daya, domin su yi
Hadaya da shi ko kuwa Layya da
shi. Wallahu A’alam.