HUKUNCIN MAIDA BUDE TARO KO RUFE SHI DA ADDU'A CIKIN JAM'I(Dr Ibrahim Jalo Jalingo)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

KUSKUREN FAHIMTAR NASSIN
ALKUR’ANI KO SUNNAH NA
WASU MUTANE
GAME DA BAYANAN DA
MALAMAI SUKA YI NA
HUKUNCIN MAIDA BUDE TARO
KO RUFE SHI DA ADDU’A CIKIN
JAM’I WATA SUNNAR DA AKE
MAIMAITAWA A KULLUM
‘Yan’uwa Musulmi! Abin da
malaman Sunnah suke cewa shi
ne: A daina rikon bude taro ko rufe
shi da addu’a a matsayin wata
Sunnar da maimaitawa a kullum, ta
yadda imma ba a yi addu’ar ba sai
a rika ganin an bar wata falala mai
yawa ta wuce, alhalin shi wannan
lamari na bude taro da addu’a
babu inda aka ga cewa Annabi mai
tsira da amincin Allah ya yi shi
koda sau daya ne duk kuwa da
cewa yana da damar yin hakan da
yin hakan wani alheri ne, ke nan
malaman Sunnah sun fahimta
daga hakan cewa: Sunnar Annabi
mai tsira da amincin Allah cikin
mas’alar ita ce rashin aikata hakan,
domin kamar yadda daliban ilmi ne
suka san cewa: wani lokaci
Sunnah ta kan kasance ne ta
hanyar bari, wani lokacin kuwa ta
kan kasance ne ta hanyar yi.
Babban Malami a duniyar Sunnah
Shaikhul Islam Ibnu Taimiya -Allah
Ya yi masa rahama- ya ce cikin
littafinsa Majmuu’ul Fataawa
26/172 :-
(( ﻭﺍﻟﺘﺮﻙ ﺍﻟﺮﺍﺗﺐ ﺳﻨﺔ، ﻛﻤﺎ ﺍﻥ ﺍﻟﻔﻌﻞ ﺍﻟﺮﺍﺗﺐ ﺳﻨﺔ،
ﺑﺨﻼﻑ ﻣﺎ ﻛﺎﻥ ﺗﺮﻛﻪ ﻟﻌﺪﻡ ﻣﻘﺘﺾ، ﺍﻭ ﻓﻮﺍﺕ
ﺷﺮﻁ، ﺍﻭ ﻭﺟﻮﺩ ﻣﺎﻧﻊ، ﻭﺣﺪﺙ ﺑﻌﺪﻩ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻘﺘﻀﻴﺎﺕ
ﻭﺍﻟﺸﺮﻭﻁ ﻭﺯﻭﺍﻝ ﺍﻟﻤﺎﻧﻊ ﻣﺎ ﺩﻟﺖ ﺍﻟﺸﺮﻳﻌﺔ ﻋﻠﻰ
ﻓﻌﻠﻪ ﺣﻴﻨﺌﺬ، ﻛﺠﻤﻊ ﺍﻟﻘﺮﺍﻥ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺼﺤﻒ، ﻭﺟﻤﻊ
ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻲ ﺍﻟﺘﺮﺍﻭﻳﺢ ﻋﻠﻰ ﺍﻣﺎﻡ ﻭﺍﺣﺪ، ﻭﺗﻌﻠﻢ ﺍﻟﻌﺮﺑﻴﺔ
ﻭﺃﺳﻤﺎﺀ ﺍﻟﻨﻘﻠﺔ ﻟﻠﻌﻠﻢ، ﻭﻏﻴﺮ ﺫﻟﻚ ﻣﻤﺎ ﻳﺤﺘﺎﺝ ﺍﻟﻴﻪ ﻓﻲ
ﺍﻟﺪﻳﻦ، ﺑﺤﻴﺚ ﻻ ﺗﺘﻢ ﺍﻟﻮﺍﺟﺒﺎﺕ ﺍﻭ ﺍﻟﻤﺴﺘﺤﺒﺎﺕ
ﺍﻟﺸﺮﻋﻴﺔ ﺍﻻ ﺑﻪ، ﻭﺍﻧﻤﺎ ﺗﺮﻛﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﻟﻔﻮﺍﺕ ﺷﺮﻃﻪ ﺍﻭ ﻭﺟﻮﺩ ﻣﺎﻧﻊ. ﻓﺄﻣﺎ ﻣﺎ ﺗﺮﻛﻪ ﻣﻦ
ﺟﻨﺲ ﺍﻟﻌﺒﺎﺩﺍﺕ ﻣﻊ ﺍﻧﻪ ﻟﻮ ﻛﺎﻥ ﻣﺸﺮﻭﻋﺎ ﻟﻔﻌﻠﻪ ﺍﻭ
ﺍﺫﻥ ﻓﻴﻪ ﻭﻟﻔﻌﻠﻪ ﺍﻟﺨﻠﻔﺎﺀ ﺑﻌﺪﻩ ﻭﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ، ﻓﻴﺠﺐ
ﺍﻟﻘﻄﻊ ﺑﺎﻥ ﻓﻌﻠﻪ ﺑﺪﻋﺔ ﻭﺿﻼﻟﺔ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Dawwamanmen bari
Sunnah ce, kamar yadda
dawwamanmen aiki yake Sunnah,
sabanin abin da barin shi ya
kasance ne saboda rashin bukatar
yin shi, ko kuwa saboda rashin
sharadin yin shi, ko kuwa saboda
samuwar abin da ya hana yin shi,
sannan bayan (mutuwar Annabi)
bukatar yin hakan ta taso, ko
sharadin yin hakan ya samu, ko
abin da ke hana yin hakan ya kau,
ta yadda Shari’ah za ta nuna
halaccin yin shi, kamar hada
Alkur’ani a Mus’hafi, da hada
mutane bayan limami daya a cikin
sallar tarawihi, da koyon ilmin
Larabci, da haddace sunayen
masu nakalto ilmi, da wanin
wannan daga cikin abin da ake
bukatarsa cikin Addini, ta yadda
wajibai da mustahabbai na
Shari’ah ba sa cika sai tare da shi,
saboda da ma can (Manzon Allah)
mai tsira da amincn Allah ya bar
yin shi ne saboda kubucewar
sharadinsa, ko saboda samuwar
abin da ke hana yin shi. To amma
abin da (Annabi) ya bari daga
jinsin Ibadu tare da cewa da abin
wani abu ne da ya dace da
Shari’ah to da ya aikata shi, ko da
ya ba da izinin a yi shi, kuma da
ma Khalifofinsa da Sahabbai sun yi
shi a bayansa, (irin wannan kam)
wajibi ne a tabbatar da cewa lalle
yin shi bidi’ah ce kuma bata)).
Intaha.
Da wannan magana ta Shaikhul
Islam Ibnu Taimiya za mu fahimci
cewa: Sunnar Annabi mai tsira da
amincin Allah cikin bude taro ko
rufe taro da addu’ah ita ce: Barin
yin hakan, saboda masu yin haka
suna ganin wata ibada suke yi
saboda su samu biyan bukatar
Duniya da Lahira, wannan shi ya
sa ma in sun ga wasu sun yi taro
ba su yi ba sai su rika jin
haushinsu, kai su ma rika zaginsu
da yi musu jumhuru daban
daban!!!
RADDI:-
Idan wani ya kafa hujja da hadithin
Abdullahi Dan Umar wanda Tirmizi
ya ruwaito cikin Sunan hadithi na
3,502, da kuma Nasaa’i cikin
Sunan hadithi na 10,234 cewa:-
(( ﻗﻠﻤﺎ ﻛﺎﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﻘﻮﻡ
ﻣﻦ ﻣﺠﻠﺲ ﺣﺘﻰ ﻳﺪﻋﻮ ﺑﻬﺆﻻﺀ ﺍﻟﺪﻋﻮﺍﺕ ﻷﺻﺤﺎﺑﻪ :
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻗﺴﻢ ﻟﻨﺎ ﻣﻦ ﺧﺸﻴﺘﻚ ﻣﺎ ﺗﺤﻮﻝ ﺑﻪ ﺑﻴﻨﻨﺎ ﻭﺑﻴﻦ
ﻣﻌﺎﺻﻴﻚ، ﻭﻣﻦ ﻃﺎﻋﺘﻚ ﻣﺎ ﺗﺒﻠﻐﻨﺎ ﺑﻪ ﺟﻨﺘﻚ، ﻭﻣﻦ
ﺍﻟﻴﻘﻴﻦ ﻣﺎ ﺗﻬﻮﻥ ﺑﻪ ﻣﺼﺎﺋﺐ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ، ﻭﻣﺘﻌﻨﺎ
ﺑﺎﺳﻤﺎﻋﻨﺎ ﻭﺍﺑﺼﺎﺭﻧﺎ ﻭﻗﻮﺗﻨﺎ ﻣﺎ ﺍﺣﻴﻴﺘﻨﺎ، ﻭﺍﺟﻌﻠﻪ
ﺍﻟﻮﺍﺭﺙ ﻣﻨﺎ، ﻭﺍﺟﻌﻞ ﺛﺎﺭﻧﺎ ﻋﻠﻰ ﻣﻦ ﻇﻠﻤﻨﺎ،
ﻭﺍﻧﺼﺮﻧﺎ ﻋﻠﻰ ﻣﻦ ﻋﺎﺩﺍﻧﺎ، ﻭﻻ ﺗﺠﻌﻞ ﻣﺼﻴﺒﺘﻨﺎ ﻓﻲ
ﺩﻳﻨﻨﺎ، ﻭﻻ ﺗﺠﻌﻞ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﺍﻛﺒﺮ ﻫﻤﻨﺎ ﻭﻻ ﻣﺒﻠﻎ ﻋﻠﻤﻨﺎ،
ﻭﻻ ﺗﺴﻠﻂ ﻋﻠﻴﻨﺎ ﻣﻦ ﻻ ﻳﺮﺣﻤﻨﺎ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Kadan ne za a ce
Mnazon Allah mai tsira da amincin
Allah ya tashi daga wata majalisa
ba tare da ya yi wa Sahabbansa
addu’a da wadannan addu’o’i ba:
Ya Allah Ka ba mu wani abu na
tsoronKa da zai shiga tsakaninmu
da sabonKa, da wani abu na
da’arKa da zai kai mu aljannarKa,
da wani abu na yakini da zai kai
saukaka mana musibun Duniya, ka
jiyarda mu dadi da jinmu, da
ganinmu, da karfinmu matukar dai
Ka rayar da mu, Ka zamar da shi
mai gado gare mu, Ka sanya
ramuwar gayyarmu a kan wanda
ya zalunce mu, Ka taimake mu a
kan wanda ya nuna mana kiyayya,
kada Ka sanya musibarmu a cikin
addininmu, kada Ka sanya Duniya
mafi girman hamminmu, ko iya
matukar ilminmu, kada Ka dora
wanda ba ya tausaya mana a
kanmu)). Intaha.
Idan wani ya kafa hujja da wannan
hadithin to sai a ce da shi: Shi
wannan hadithin abin da kawai ya
ce shi ne: “Yan lokuta kadan ne za
ce Annabi ya tashi daga wata
majalisa ba tare da ya yi wa
sahabbansa addu’a ba” hadithin
bai ce Annabi yana ce wa
sahabbansa ne: ku yi salati goma-
goma sannan ya rika yin addu’a su
kuma suna cewa: ameen ba!!!
Babu wani magabaci da ya yi wa
hadithin wannan fahimta, babu
kuma wani malami daga cikin
masu yi wa hadithai sharhi -a iya
sanina- da ya yi wa hadithin
wannan fahimta, babu daya daga
cikin maluman Da’awah da Aqidah
da ya yi wa hadithin wannan
fahimta!!! Sannan ko shakka babu
da da wannan surar ce Annabi
yake yin addu’ar to da an nakalto
mana ita, saboda sura ce mai jan
hankulan mutane sosai, domin
kowa ya kan bar abin da yake yi ne
domin ya saurari mai yin addu’a
bayan ya yi salati sannan kuma ya
rika fadar ameen.
Sannan a cikin hadithin an ce:-
(( ﻣﻦ ﻣﺠﻠﺲ))
Watau: daga ma ko wace majlisa.
Ke nan wannan ya hada da
majalisar tattauna lamuran duniya
na yau da gobe, da majalisar wani
darasi, da majalisar koma mene
ne. In da kuwa lalle yana yin
addu’ar ne a bisa surar da muke yi,
to da kuwa an nakalto mana ita.
Sannan kuma da Malumanmu na
Da’awah da Aqidah ba su hana yin
addu’a cikin irin ita wannan surar
ba a farko ko karshen majalisar
wani darasi, ko majalisar karatun
Kur’ani ba, da sauransu.
Sannan abu na biyu shi ne: Mene
ne ya hada tsakanin cewa Annabi
yana yi wa Sahabbansa addu’a
cikin mafi yawan majalisu, da
kuma cewa Annabi yana addu’ar
bude taro da rufe taro cikin jam’i, in
ba ta’assubanci da son zuciya ba?
Ga misali: Abu Dawuda ya ruwaito
hadithi na 3,203, da Tirmizi hadithi
na 1,024, da Nasa’ii hadithi na
1,986’ da Ibnu Majah hadithi na
1,498, da Ahmad hadithi na 17,581
daga Sahabi Abu Hurairah da
waninsa cewa Annabi mai tsira da
amincin Allah ya kasance yana yi
wa Sahabbai rayayyu da matattu
maza da mata manya da yara
addu’a cikin sallar janaza. Ga ma
yadda nassin yake:-
(( ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﺤﻴﻨﺎ ﻭﻣﻴﺘﻨﺎ ﻭﺻﻐﻴﺮﻧﺎ ﻭﻛﺒﻴﺮﻧﺎ
ﻭﺫﻛﺮﻧﺎ ﻭﺍﻧﺜﺎﻧﺎ ﻭﺷﺎﻫﺪﻧﺎ ﻭﻏﺎﺋﺒﻨﺎ. ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻣﻦ ﺍﺣﻴﻴﺘﻪ
ﻣﻨﺎ ﻓﺎﺣﻴﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻻﻳﻤﺎﻥ ﻭﻣﻦ ﺗﻮﻓﻴﺘﻪ ﻣﻨﺎ ﻓﺘﻮﻓﻪ ﻋﻠﻰ
ﺍﻻﺳﻼﻡ. ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻻ ﺗﺤﺮﻣﻨﺎ ﺍﺟﺮﻩ ﻭﻻ ﺗﻀﻠﻨﺎ ﺑﻌﺪﻩ .((
ﺍﻧﺘﻬﻰ.
Ma’ana: ((Ya Allah Ka gafarta wa
rayayyunmu da matattunmu, da
kanananmu da manyanmu, da
mazanmu da matanmu, da
halartattunmu da wadanda ba sa
nan daga cikinmu. Ya Allah wanda
Ka raya shi daga cikinmu to Ka
raya shi a kan Imani, Wanda kuma
Ka matar daga cikinmu to Ka matar
da shi a kan Musulunci. Ya Allah
kada Ka haramta mana ladansa,
kada kuma Ka batar da mu
bayansa)). Intaha.
A nan addu’a ce da Annabi yake yi
wa Sahabbansa, rayayyu da
matattu, amma kuma shi kadai
yake yin ta ba ma dole ba ne
jama’ar da ke tare da shi su abin
da yake fada, kuma babu salatin
Annabi goma-goma a cikinta, babu
kuma fadar ameen daga sauran
jama’a. Lalle yadda ita wannan
addu’ar take to haka ma addu’ar:-
(( ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻗﺴﻢ ﻟﻨﺎ ﻣﻦ ﺧﺸﻴﺘﻚ ﻣﺎ ﺗﺤﻮﻝ ﺑﻪ ﺑﻴﻨﻨﺎ ﻭﺑﻴﻦ
ﻣﻌﺎﺻﻴﻚ……)).
take, wannan shi ya sa ma su
wadannan kalmomi ba sa canja
wa, kamar yadda wadancan su ma
ba sa canjawa.
Sannan abu na biyu shi ne: Akwai
gurare da yawa da Annabi mai
tsira da amincin Allah yake yi wa
Sahabbai addu’a, to amma
maluman Sunnah ba su fahimci
cewa addu’ar jam’i ne yake yi ba.
Misali:-
1-Hadithi na 5108 da Abu Dawud
ya ruwaito, na 4623 da Abu Ya’ala
ya ruwaito cikin Musnad, na 140 da
Ibnul Jaaruud ya ruwaiton cikin
Muntaqa daga A’isha Allah Ya kara
mata yarda ta ce:-
((ﻛﺎﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﺆﺗﻰ
ﺑﺎﻟﺼﺒﻴﺎﻥ ﻓﻴﺪﻋﻮ ﻟﻬﻢ ﺑﺎﻟﺒﺮﻛﺔ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Manzon Allah mai tsira
da amincin Allah ya kasance ana
zuwa masa da yara yana musu
addu’ar samun albarka)). Intaha.
Wannan hadithin Albanii ya
inganta shi cikin Alkalimut Tayyib
1/162. Lalle a nan hadthin ba ya
nufin jam’in addu’a Annabi yake yi
watau ya umurci mutane su daga
hannu suna cewa Ameen shi kuwa
yana Ddu’a.
2-Hadithi na 502 da Bukharii ya
ruwaito cikin Al’adabul Mufrad, da
hadithi na 9969 da Baihaqii ya
ruwaito cikin Shu’abul Iman cewa:-
(( ﺟﺎﺀﺕ ﺍﻟﺤﻤﻰ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﻓﻘﺎﻟﺖ: ﺍﺑﻌﺜﻨﻲ ﺍﻟﻰ ﺍﺛﺮ ﺍﻫﻠﻚ ﻋﻨﺪﻙ. ﻓﺒﻌﺜﻬﺎ ﺍﻟﻰ
ﺍﻷﻧﺼﺎﺭ ﻓﺒﻘﻴﺖ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﺳﺘﺔ ﺍﻳﺎﻡ ﻭﻟﻴﺎﻟﻴﻬﻦ ﻓﺎﺷﺘﺪ
ﺫﻟﻚ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﻓﺎﺗﺎﻫﻢ ﻓﻲ ﺩﻳﺎﺭﻫﻢ ﻓﺸﻜﻮﺍ ﺫﻟﻚ ﺍﻟﻴﻪ،
ﻓﺠﻌﻞ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﺪﺧﻞ ﺩﺍﺭﺍ ﺩﺍﺭﺍ
ﻭﺑﻴﺘﺎ ﺑﻴﺘﺎ ﻳﺪﻋﻮ ﻟﻬﻢ ﺑﺎﻟﻌﺎﻓﻴﺔ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Zazzabi ya zo gurin
Annabi mai tsira da amincin Allah
sai ya ce: aika ni zuwa ga mutanen
da suka fi soyuwa gare ka. Sai ya
aika da shi zuwa ga Ansarawa, ya
je ya zauna a cikinsu yini shida da
dare shida, hakan ya tsananta a
kansu, sai ya je musu cikin
unguwarsu, sai suka yi masa
kukan wannan zazzabin. Sai
Annabi mai tsira da amincin Allah
ya rika shiga bangare bangare,
gida gida yana musu addu’ar
samun lafiya)). Intaha. Wannan
hadithin Albaanii ya inganta shi
cikin Silsilah Sahihah lamba na:
2502. A nan ma babu wani mai
sharhin hadithai da ya ce addu’ar
jam’i aka yi Annabi na addu’a
saura jama’a na cewa: ameen.
3-Hadithi na 1668 da Malik ya
ruwaito cikin Muwattaa, da hadithi
na 17,959 da Tabaraanii ya
ruwaito cikin Almu’ujamul Kabir, da
hadithi na 9,503 da Abdur Razzaq
ya ruwaito cikin Musannaf daga
Abu Burdah cewa:-
(( ﺍﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﻮﻡ ﺣﻨﻴﻦ ﺃﺗﻰ
ﺍﻟﻘﺒﺎﺋﻞ ﻳﺪﻋﻮ ﻟﻬﻢ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Annabi mai tsira da
amincin Allah ya je wa Kabilu a
ranar yakin Hunain yana musu
addu’a)). Intaha. Mai littafin
Majma’uz Zawaa’id 5/407 ya ce:
Mazajen isnadin Mazajen Buharii
da Muslim ne, in banda Abdullahi
Ibnul Mugiirah shi kuwa thiqah ne.
A nan ma babu wanda ya ce
Annabi ya je yana addu’ar ne
sannan ya umurci Kabilun da su
rika cewa: ameen.
4- Hadithi na 4,546 da Haakim ya
ruwaito cikin Mustadrak daga
Waliid Dan Uqbah cewa:-
(( ﻟﻤﺎ ﻓﺘﺢ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻣﻜﺔ
ﺟﻌﻞ ﺍﻫﻞ ﻣﻜﺔ ﻳﺄﺗﻮﻥ ﺑﺼﺒﻴﺎﻧﻬﻢ ﻓﻴﻤﺴﺢ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻋﻠﻰ ﺭﺅﻭﺳﻬﻢ ﻭﻳﺪﻋﻮ ﻟﻬﻢ .((
ﺍﻧﺘﻬﻰ.
Ma’ana: ((Lokacin da Manzon Allah
mai tsira da amincin Allah ya bude
Makka, mutanen Makka sun yi ta
kawo yaransu Manzon Allah yana
ta shafan kawunansu yana musu
addu’a)). Intaha. A nan ma babu
wani mai sharhin hadithi da ya ce:
Annabi ya ce su yi ta cewa ameen
ne a lokacin da yake yi wa yaran
nasu addu’a. watau babu wanda
ya ce addu’ar jam’i Annabi ya yi.
AMSA KAN WATA MAGANAR
KUMA
Idan wani ya kafa hujja da
wadannan Nassosi kamar:-
(( ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ ﺟﺎﺀﻭﺍ ﻣﻦ ﺑﻌﺪﻫﻢ ﻳﻘﻮﻟﻮﻥ ﺭﺑﻨﺎ ﺃﻏﻔﺮﻟﻨﺎ
ﻭﻻﺧﻮﺍﻧﻨﺎ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺳﺒﻘﻮﻧﺎ ﺑﺎﻹﻳﻤﺎﻥ.(( ﺍﻟﺤﺸﺮ:١٠ .
Ma’ana: ((Wadanda suka zo daga
bayansu suna cewa: Ya
Ubangijinmu! Ka gafarta mana, da
kuma ‘yan’uwanmu wadanda suka
riga mu yin Imani)). Intaha. Da
kuma:-
(( ﻗﻞ ﻣﺎ ﻳﻌﺒﺆ ﺑﻜﻢ ﺭﺑﻲ ﻟﻮﻻ ﺩﻋﺎﺅﻛﻢ.(( ﺍﻟﻔﺮﻗﺎﻥ:
٧٧.
Ma’ana: ((Ka ce: Ubangijina ba ya
kulawa da ku, in ba domin
addu’arku ba)). Intaha. Da kuma:-
(( ﻭﺍﺫﺍ ﺳﺎﻟﻚ ﻋﺒﺎﺩﻱ ﻋﻨﻲ ﻓﺎﻧﻲ ﻗﺮﻳﺐ ﺃﺟﻴﺐ ﺩﻋﻮﺓ
ﺍﻟﺪﺍﻉ ﺍﺫﺍ ﺩﻋﺎﻥ.(( ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ: ١٨٦ .
Ma’ana: ((Idan bayiNa suka
tambaye ka labariNa to Ni kusa
Nake, kuma ina amsa addu’ar mai
addu’a in ya kira Ni)). Intaha. Da
kuma sauran Nassosi masu kama
da haka ya ce kuma: Lalle mu
muna hana a yi sa Musulmi addu’a
ne, alhalin Allah Ya ce a roke Shi
zai kuma amsa!!!
Farko dai sai a ce da su tarihi ne
yake maimaita kan sa, tsakanin
maluman Sunnah da kuma masu
bidi’a da bautar son zuciya. Misali:
lokacin da Shehu Uthmanu Dan
Fodiyo ya ce cikin littafin shi
Ihya’us Sunnah shafi na 102:-
(( ﻭﻣﻦ ﺫﻟﻚ ﺍﻟﺪﻋﺎﺀ ﺩﺑﺮ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﺑﻜﻴﻔﻴﺔ ﻣﻌﻠﻮﻣﺔ
ﻭﻫﻮ ﺍﻥ ﻳﺪﻋﻮ ﺍﻻﻣﺎﻡ ﻭﻳﺆﻣﻦ ﺍﻟﻨﺎﺱ، ﻭﻫﻮ ﺑﺪﻋﺔ
ﻣﻜﺮﻭﻫﺔ ﻓﻲ ﻣﺬﻫﺐ ﻣﺎﻟﻚ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Daga cikin wannan
akwai addu’a bayan Salla a bisa
wani yanayi sananne, shi ne kuwa:
Liman yana addu’a Mamu suna
cewa ameen. Shi wannan bidi’a ce
makruuhiya a cikin mazhabar
Imam Malik)). Intaha. A lokacin da
Shehu Dan Fodiyo da kuma ire-
irensa suka fadi haka saboda
neman jama’a su yi Musuluncisu
kamar yadda Annabi da Sahabbai
suka yi an samu wasu masu
ta’assubanci wadanda kiyayya da
hasada suka cika zukatansu, da
suka ki yin aiki da wannan bayani
na ilmi da so wa Musulmi alheri,
suka koma suna ta kafa hujja da
irin wadannan dalilai aammah,
wadanda masu ilmi sun san cewa
ba za nuni a kan bigiren da aka yi
sabani a kan shi. Kamar dai
mutumin da za ka ce da shi: ka
daina yin Salatul fatih ka rika yin
Salatin da Annabi mai tsira da
amincin Allah ya koya wa
Sahabbai. Sannan shi kuma ya
rika gaya wa jama’a cewa: Kai din
nan ka hana a rika yi wa Annabi
salati!!! Ko kuma ka ce a daina
zikirin bidi’ah na ihu da bugun kirji,
ko bisa wani adadi wanda ba
Shari’a ce ta bayyana ba. Sai kuma
a ce: Kai din nan wai ka hana a yi
wa Allah zikiri duk kuwa da cewa
Nasosi da yawa sun yi umurni da
yin hakan!!
Na biyu sai a ce da su: Irin wannan
tuhumar ba sabon lamari ba ne ga
Maluma masu da’awah wadanda
suke kokarin maida mutane a kan
Sunnar Annabi mai tsira da
amincin Allah cikin dukkan
lamuransu. Imam Abdur Razzaq ya
ruwaito cikin littafinsa Musannaf
atharii na 4,755 da kuma Imamul
Baihaqii a cikin Assunanul Kubra
atharii na 4,621 daga Sa’id Dan
Musayyib cewa:-
((ﺍﻧﻪ ﺭﺃﻯ ﺭﺟﻼ ﻳﺼﻠﻲ ﺑﻌﺪ ﻃﻠﻮﻉ ﺍﻟﻔﺠﺮ ﺍﻛﺜﺮ ﻣﻦ
ﺭﻛﻌﺘﻴﻦ ﻳﻜﺜﺮ ﻓﻴﻬﺎ ﺍﻟﺮﻛﻮﻉ ﻭﺍﻟﺴﺠﻮﺩ، ﻓﻨﻬﺎﻩ، ﻓﻘﺎﻝ:
ﻳﺎ ﻣﺤﻤﺪ! ﻳﻌﺬﺑﻨﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺼﻼﺓ؟ ﻗﺎﻝ: ﻻ ﻭﻟﻜﻦ
ﻳﻌﺬﺑﻚ ﻋﻠﻰ ﺧﻼﻑ ﺍﻟﺴﻨﺔ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Ya ga wani mutum yana
salla fiye da raka’a biyu bayan
fitowar alfijir yana yawaita ruku’i da
sujjada cikin sallar, sai ya hana
shi. Sai mutumin ya ce: Ya Abu
Muhammad! Yanzu a kan salla ne
Allah zai azabtar da ni? Sai ya ce:
A’a zai azabtar da kai ne a kan
sabawa Sunnah)). Intaha. Sheik
Albani bayan ya kawo wannan
magana cikin littafinsa Irwa’ul Galil
2/236 kuma ya inganta isnadinta
sai ya ce:-
(( ﻭﻫﺬﺍ ﻣﻦ ﺑﺪﺍﺋﻊ ﺃﺟﻮﺑﺔ ﺳﻌﻴﺪ ﺑﻦ ﺍﻟﻤﺴﻴﺐ ﺭﺣﻤﻪ
ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ، ﻭﻫﻮ ﺳﻼﺡ ﻗﻮﻱ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﺒﺘﺪﻋﺔ ﺍﻟﺬﻳﻦ
ﻳﺴﺘﺤﺴﻨﻮﻥ ﻛﺜﻴﺮﺍ ﻣﻦ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﺑﺎﺳﻢ ﺍﻧﻬﺎ ﺫﻛﺮ
ﻭﺻﻼﺓ، ﺛﻢ ﻳﻨﻜﺮﻭﻥ ﻋﻠﻰ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺍﻧﻜﺎﺭ ﺫﻟﻚ
ﻋﻠﻴﻬﻢ، ﻭﻳﺘﻬﻤﻮﻧﻬﻢ ﺑﺎﻧﻬﻢ ﻳﻨﻜﺮﻭﻥ ﺍﻟﺬﻛﺮ ﻭﺍﻟﺼﻼﺓ !!
ﻭﻫﻢ ﻓﻲ ﺍﻟﺤﻘﻴﻘﺔ ﺍﻧﻤﺎ ﻳﻨﻜﺮﻭﻥ ﺧﻼﻓﻬﻢ ﻟﻠﺴﻨﺔ ﻓﻲ
ﺍﻟﺬﻛﺮ ﻭﺍﻟﺼﻼﺓ ﻭﻧﺤﻮ ﺫﻟﻚ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Wannan yana daga cikin
kyawawan jawaban Sa’idu Dan
Musayyib Allah Madaukakin Sarki
Ya yi masa rahama, sannan kuma
shi makami ne mai karfi a kan ‘yan
bidi’a da suke ganin kyawun da
yawa daga cikin bidi’o’i da sunan
cewa: Ai zikiri ne, da Salla! Sannan
kuma su yi wa Ahlus Sunnah
inkarin inkarin da suke yi musu,
kuma su tuhumce su da cewa:
Suna hana zikirin Allah da kuma
Salla!! Wanda kuma a gaskiyar
al’amari su suna musu inkarin
barin Sunnah ne da suka yi cikin
Zikirin da kuma Sallar, da abin da
ya yi kama da haka)). Intaha.
Muna rokon Allah Madaukakin
Sarki ya nuna mana gaskiya
gaskiya ce ya kuma ba mu ikon
aiki da ita. Ya kuma nuna mana
karya karya ce ya ba mu ikon guje
mata. Ameen.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

5 responses to “HUKUNCIN MAIDA BUDE TARO KO RUFE SHI DA ADDU'A CIKIN JAM'I(Dr Ibrahim Jalo Jalingo)”
 1. Adam abualamin Avatar
  Adam abualamin

  Mall allah yasakada alheri yakaramana rikoda sunnar annabi s.A.W.

 2. Albany Dabai Avatar
  Albany Dabai

  Jazaakumul Lahu khairan

 3. Umar Avatar
  Umar

  Allah ya saka da alheri.

 4. zainab sani abdullahi Avatar
  zainab sani abdullahi

  mallam tambayata anan shine menene hukuncin wadanda basa du’a al-majlis naga itama sunah ce amai makon haka sai dunga wadan aduoin nasu?

 5. Yakubu Muhammad Avatar
  Yakubu Muhammad

  Jazakallahu khair

Leave a Reply

Categories
Latest updates