HUKUNCIN YIN KUNUTI CIKIN SALLOLIN FARILLAN NAN GUDA BIYAR(Dr.Ibrahim Jalo Jalingo)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

‘Yan’uwa Musulmi! Addinin
Musulunci ya halatta yin Kunuti cikin
sallolin farillan nan guda biyar
matukar wata musiba ta auka wa
Al’ummar Musulmi, ana kuma yin
Kunutin ne a raka’ar karshe bayan
liman ya ce SamiAllahu liman
hamidah. Kuma liman zai rika yin
Kunutin ne a bayyane mamu kuma
suna cewa Aameen, ko wannensu
kuma yana mai daga hannayensa
lokacin addu’ar Kunutin, in an gama
kuma sai a sake hannu ba tare da
shafar fuska ba saboda shafar fuska ba
ta inganta ba cikin addu’ar Kunuti.
Sannan babu wata ayyananniyar siga
ta addu’ar Kunuti illa dai kawai liman
ya yi addu’a a kan irin musibar da ake
ciki.
Ga kadan daga cikin hujjojin
wadannan bayanai da na yi:-
1- Imam Ahmad ya ruwaito cikin
Musnad hadithi na 2746, da Imam
Abu Dawuda cikin Sunan hadithi na
1442, da Imam Ibnu Khuzaimah cikin
Sahih hadithi na618, da Imamul
Baihaqii cikin Sunan hadithi na3222,
da Imam Hakim cikin Mustadrak
hadith na 820. Sannan Albani da
wasunsa sun inganta hadithin. Daga
Sahabi Abdullahi Dan Abbas Allah
Ya kara musu yarda ya ce:-
(( ﻗﻨﺖ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺷﻬﺮﺍ
ﻣﺘﺘﺎﺑﻌﺎ ﻓﻲ ﺍﻟﻈﻬﺮ ﻭﺍﻟﻌﺼﺮ ﻭﺍﻟﻤﻐﺮﺏ ﻭﺍﻟﻌﺸﺎﺀ
ﻭﺻﻼﺓ ﺍﻟﺼﺒﺢ ﻓﻲ ﺩﺑﺮ ﻛﻞ ﺻﻼﺓ ﺍﺫﺍ ﻗﺎﻝ ﺳﻤﻊ ﺍﻟﻠﻪ
ﻟﻤﻦ ﺣﻤﺪﻩ ﻣﻦ ﺍﻟﺮﻛﻌﺔ ﺍﻻﺧﺮﺓ ﻳﺪﻋﻮ ﻋﻠﻰ ﺍﺣﻴﺎﺀ ﻣﻦ
ﺑﻨﻲ ﺳﻠﻴﻢ ﻋﻠﻰ ﺭﻋﻞ ﻭﺫﻛﻮﺍﻥ ﻭﻋﺼﻴﺔ ﻭﻳﺆﻣﻦ ﻣﻦ
ﺧﻠﻔﻪ )).
Ma’ana: ((Manzon Allah mai tsira da
amincin Allah ya yi Kunuti wata guda
kuma a jere, cikin Azahar, da La’asar,
da Magariba, da Isha’i, da Sallar
Asuba, idan ya ce SamiAllahu liman
hamidah cikin raka’ar karshe, yana
mugunyar addu’a a kan wasu
unguwanni na Kabilun Banu Sulaim,
da Ri’il, da Zakwaan, da Usayyah,
mamun da ke baya kuma suna cewa
A’ameen)).
2- Imamul Bukhari ya ruwaito hadithi
na 4090, da Imamu Muslim hadithi na
1584 daga Sahabi Anas Dan Malik
Allah Ya kara musu yarda ya ce:-
(( ﺍﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﻨﺖ ﺷﻬﺮ ﻳﻠﻌﻦ
ﺭﻋﻼ ﻭﺫﻛﻮﺍﻥ ﻭﻋﺼﻴﺔ ﻋﺼﻮﺍ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ)).
Ma’ana: ((Annabi mai tsira da amincin
Allah ya yi Kunuti wata guda yana
la’antar Kabilun Ri’il, da Zakwaan, da
Usayyah, wadanda suka saba wa
Allah da ManzonSa)).
3- Imam Muslim ya ruwaito hadithi
na 1588 daga Sahabi Baraa’u Dan
Aazib Allah Ya kara masa yarda ya
ce:-
(( ﻗﻨﺖ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﻲ ﺍﻟﻔﺠﺮ
ﻭﺍﻟﻤﻐﺮﺏ)).
Ma’ana: ((Manzon Allah mai tsira da
amincin Allah ya yi Kunuti cikin
sallar Asuba, da Magariba)).
4- Imam Ahmad ya ruwaito cikin
Musnad hadithi na 12425 daga Sahabi
Anas Dan Malik Allah Ya kara musu
yarda ya ce:-
(( ﻓﻤﺎ ﺭﺍﻳﺖ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺟﺪ
ﻋﻠﻰ ﺷﻲﺀ ﻗﻂ ﻭﺟﺪﻩ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﻳﻌﻨﻲ ﺍﻟﻘﺮﺍﺀ، ﻓﻠﻘﺪ
ﺭﺍﻳﺖ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﻲ ﺻﻼﺓ
ﺍﻟﻐﺪﺍﺓ ﺭﻓﻊ ﻳﺪﻳﻪ ﻓﺪﻋﺎ ﻋﻠﻴﻬﻢ )).
Ma’ana: ((Ban taba ganin Manzon
Allah mai tsira da amincin Allah
zuciyarsa ta baci a kan wani abu ba,
kamar yadda na ga zuciyarsa ta baci
saboda kisan Mahaddata da aka yi.
Hakika na ga Manzon Allah mai tsira
da amincin Allah cikin sallar Asuba
ya daga hannayensa yana musu
mugunyar addu’a)).
*******************
FATAWOWIN IBNU TAIMIYAH
GAME DA KUNUTIN:
1- Shaikhul Islam Ibnu Taimiyah ya
ce cikin Majmuu’ul Fataawaa
23/108 :-
(( ﺍﻟﻘﻨﻮﺕ ﻣﺴﻨﻮﻥ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻨﻮﺍﺯﻝ، ﻭﻫﺬﺍ ﺍﻟﻘﻮﻝ ﻫﻮ
ﺍﻟﺬﻱ ﻋﻠﻴﻪ ﻓﻘﻬﺎﺀ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﻭﻫﻮ ﺍﻟﻤﺎﺛﻮﺭ ﻋﻦ
ﺍﻟﺨﻠﻔﺎﺀ ﺍﻟﺮﺍﺷﺪﻳﻦ )).
Ma’ana: ((Kunuti sunna ne lokacin da
wata musiba ta sauko, wannan zance
shi ne wanda Faqiihan Maluman
Hadithi ke kansa, shi ne kuma aka ciro
daga Khulafaa’ur Raashidiin)).
2- Shaikhul Islam Ibnu Taimiyah ya
sake cewa cikin Majmuu’ul Fataawaa
22/270:-
(( ﻓﻴﺸﺮﻉ ﺍﻥ ﻳﻘﻨﺖ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻨﻮﺍﺯﻝ ﻳﺪﻋﻮ ﻟﻠﻤﺆﻣﻨﻴﻦ
ﻭﻳﺪﻋﻮ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻜﻔﺎﺭ ﻓﻲ ﺍﻟﻔﺠﺮ ﻭﻏﻴﺮﻫﺎ ﻣﻦ
ﺍﻟﺼﻠﻮﺍﺕ ﻭﻫﻜﺬﺍ ﻛﺎﻥ ﻋﻤﺮ ﻳﻘﻨﺖ ﻟﻤﺎ ﺣﺎﺭﺏ
ﺍﻟﻨﺼﺎﺭﻯ ﺑﺪﻋﺎﺋﻪ ﺍﻟﺬﻱ ﻓﻴﻪ: ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻟﻌﻦ ﻛﻔﺮﺓ ﺍﻫﻞ
ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ )).
Ma’ana: ((An shar’anta ya yi Kunuti a
lokacin da wasu musibu suka sauko,
ya yi wa Muminai addu’ar alheri, ya yi
wa kafurai mugunyar addu’a a cikin
sallar Asuba da waninta daga cikin
Salloli. Haka Umar ya kasance yake
yin Kunuti a lokacin da yake yin yaki
da Nasara, da addu’arsan nan da a
cikinta yake cewa: Ya Allah Ka la’anci
Kafuran Ahlul Kitab)).
3- Shaikhul Islam Ibnu Taimiya ya
sake cewa cikin Majmuu’ul
Fataawaa21-155:-
(( ﻓﺎﻟﺴﻨﺔ ﺍﻥ ﻳﻘﻨﺖ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻨﺎﺯﻟﺔ ﻭﻳﺪﻋﻮ ﻓﻴﻬﺎ ﺑﻤﺎ
ﻳﻨﺎﺳﺐ ﺍﻟﻘﻮﻡ ﺍﻟﻤﺤﺎﺭﺑﻴﻦ)).
Ma’ana: ((Abin da yake Sunnah shi ne
ya yi Kunuti a lokacin da musiba ta
sauko, kuma ya yi addu’a wacce za ta
dace da halayyar mutanen da ake yaki
da su)).
Allah Ya taimake mu. Ameen.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories