Liman yana dauke mantuwar Mamu

·

·

,

Domin neman ƙarin bayani danna nan

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wa barakaatuh

Yana daga cikin abinda limami yake ɗauke wa mamu: Kuskure da Mamtuwa.

Idan mamu yayi mantuwa a sallah, ko ƙari ne ko ragi to liman yana ɗauke masa. Sai dai idan ya mance farilla ce to anan liman bazai ɗauke masa ba dole sai ya sake wannan raka’ar da ya mance farillar aciki ko kuma ya sake sallar baki ɗaya idan Farillar da ya bari tana ɓata Sallah baki ɗaya. Kaman idan ya mance kabbarar harama.

Misali idan Mamu ya mance Tahiya ta farko baiyi ba to ba sai yayi Sujada ba’adi ba, limaminsa zai ɗauke masa. Amma misali idan mamu ya mance ƙabbarar harama to limaminsa bazai ɗauke masa anan, saboda kabbarar harama Farilla ce kuma liman baya ɗauke farilla wa mamun sa.

Yana daga cikin Dalilin da yake nuna haka ƙissar Mu’awiyah ibnul Hakam Assulami Allah ya ƙara masa yarda lokacin da aka haramta magana a Sallah shi bai sani ba da ya shiga Sallah tare da Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi sai wani yayi atishawa sai yace masa “yarhamukallah” har zuwa ƙarshen ƙissar. A ƙarshe da Annabi ya faɗa masa haramcin Yin Magana a Sallah bai umarce shi yayi sujadar Ba’adi ba. Wannan Hadisi Muslim ya rawaito shi a Hadisi 537

Sannan kuma maluma suka ce Sahabbai suna mantuwa a Sallah a Zamanin Annabi, in suna Sallah tare da Annabi, kuma ba’a rawaito cewa suna yin Sujadar Mantuwa ba. Wannan yake nuna cewa Liman yana ɗauke wa Mamu Mantuwar da yayi a Sallah.

Allah shine mafi sani.

Leave a Reply

Latest updates
Categories