Hukuncin ɗaukan Yaro a Sallah alhali akwai Fitsari ko bayan gari acikin pampers nashi

Danna nan domin shiga karatu Online

Tambaya: Meye Hukuncin Sallar wanda ya ɗauki yaro acikin Sallarsa alhali kuma yaron yayi bayan gari a cikin pampers?

Amsa: Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.

Tsarƙi yana daga cikin Sharuɗɗan ingancin Sallah, Sallar mutum bata inganta har sai mutum ya tsarƙaƙe jikinsa, tufan sa da wurin yin sallar sa.

Saboda haka baya Halatta Mutum yayi Sallah alhali yana ɗauke da najasa sai dai idan bai sani ba.

Ibnu Qudama yace:

Idan da mai Sallah zai ɗauki kwalba dake ƙulle, da akwai najasa acikin sa Sallar sa bata yi ba.

Almugni: 1/403

Amma idan ya zamto yayi sallah da najasar a jikinsa ba tare da sanin sa ba to babu komi a kansa, kuma Sallar sa tayi

Idan kuma yana ɗauke da yaron ne sai yaron yayi fitsari ko bayan gari to sai ya ajiye shi yaci gaba da Sallar shi babu komi akan sa.

An rawaito Hadisi daga Abu sa’id Alkhudri Allah ya ƙara masa yarda yace:

Watarana Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana Sallah da Sahabban sa sai ya cire takalman sa ya sanya su a gefensa na hagu, lokacin da Sahabban sa suka ga haka suma sai suka cire takalman su suka jefar, bayan da suka kammala Sallah sai Annabi ya tambaye su meyasa kuka jefar da takalman ku? Sai suka ce masa munga ka jefar da takalman ka ne shi yasa muma muka jefar, sai Annabi yace musu: Jibrilu ne yazo ya bani labari cewa akwai Najasa a jikin su. Idan ɗaya daga cikinku yazo Sallah to ya duba idan yaga wani Najasa ko ƙazanta a jikin Takalmin sa to ya goge yayi Sallah aciki.

Abu Dawud: 650. Ahmad: 11169

Wannan Hadisi yana nuna Mana idan mutum yayi Sallah da najasa a jikinsa bai sani ba Sallar sa tayi. Domin da Sallar ba ta yi ba da Annabi zai katse Sallar ne ya sake sabo, amma baiyi haka ba.

A taƙaice: idan Mutum yayi Sallah yana ɗauke da yaro a hannunsa ko a bayan sa kuma yana sane da  Akwai Fitsari ko Bayan gari acikin pampers na yaron to Sallarsa ta ɓaci. 
Idan kuma yayi bai sani ba babu komai a kansa. Idan kuma yana cikin Sallan ne yaron yayi bayan gari ko fitsari to sai ya ajiye yaron a ƙasa yaci gaba da Sallar sa.

Allah shine mafi sani

Domin turo tambaya danna nan.

Idan akwai kuskure da ka hango acikin wannan Amsa danna nan domin tuntuɓar mu

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates