Lokacin yin Addu’ar Istikhara

·

·

Domin neman ƙarin bayani danna nan

Tambaya: wani lokaci ne ake yin Addu’ar Istikhara? Shin ana iya yi bayan Sallar farilla?

Amsa: Ana yin Addu’ar istikhara ne bayan Sallar nafila wanda akayi ta domin Istikhara. Kamar yadda Hadisin da yazo kan Addu’ar istikhara ya nuna.

Jabir ɗan Abdullahi Allah ya ƙara masa yarda yace:

Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana koya mana istikhara(Neman Zaɓin Allah) kamar yadda yake koya mana Sura acikin Alqur’ani. Yana cewa: “idan ɗaya daga cikin ku yayi nufin aikata wani lamari to yayi raka’oi guda biyu wanda ba ta farilla ba Sannan yace: “Sai ya ambaci Addu’ar Istikhara.

Sahihul Bukhari: 1162

Da wannan hadisin ne Wasu Maluma suke ganin duk wanda yake so yayi Istikhara to dole sai yayi Sallah keɓantacciya domin istikharar. Wacce ba ta farilla ba, ko Sunnoni wanda akeyi bayan Salloli da makamantansu.

Sheikh Ibnu Uthaymeen Allah yayi masa rahama yace:

Maluma Sun samu tsaɓani kan faɗin Manzon Allah “Yayi sallah raka’oi biyu wanda ba Farilla ba” shin idan yayi Sunnah Ratiba(Nafilolin bayan Sallolin farilla) ta wadatar dashi da abinda ake buƙata? Ko kuma dole ayi wa istikhara Sallah keɓantacciya?

Wa’inda suka tafi kan cewa Raka’oi biyun da ake buƙata ayi shine wanda ba ta farilla ba, saboda haka ya shafi dukkan wasu nafiloli, na Rawatib, da tahiyyatul masjid da sauran su. Saboda haka mutum zai iya yin Istikhara a bayan wa’innan nafiloli.

Wa’inda kuma suka tafi kan cewa dole sai dai ayi sallah keɓantacciya saboda Istikhara Wanda kuma maganar su itace tafi kusa da gaskiya a wuri na, suna tafiya kan cewa wa’innan nafilolin basu wadatar wa.

A duba Liqa’ul babil Maftuh: Haɗuwa ta 206

Haka nan yazo acikin Fatawa ta Lajnatud-da’imah

Ana Shar’anta wa Addu’ar Istikhara Sallah keɓantacciya saboda hadisi da aka rawaito daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallama. ” idan ɗaya daga cikin ku yayi nufin aikata wani lamari to yayi raka’oi guda biyu wanda ba ta farilla ba”

Allajnatud-da’ima: 6/158

A taƙaice: magana mafi inganci shine idan Mutum yana so yayi Addu’ar Istikhara to yayi sallah raka’a biyu keɓantacciya domin Yin Addu’ar Istikhara, idan ya kammala sai ya karanta Addu’ar bayan Yayi Sallama. Domin haka shi yafi dace wa da Hadisin. Allah shine mafi sani.

Domin Samun Addu’ar Istikhara danna nan

Leave a Reply

Latest updates
Categories