Ladubban Tafiya zuwa Masallaci

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Maqala

Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.

Ga wasu daga cikin Ladubban zuwa Masallaci.

1. Yin Alwala kafin Zuwa Masallaci: Anaso Ayi alwala daga gida kafin a fita zuwa Masallaci.

Abu Huraira Allah ya ƙara masa yarda ya rawaito daga Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace:

Wanda yayi Alwala a gidan sa, sannan ya tafi zuwa ɗaki daga cikin ɗakunan Allah, domin ya sauƙe farali daga cikin farillan Allah, duk taku da zaiyi ɗaya zata kankare masa zunubansa ɗaya kuma zata ɗaukaka darajar sa.

Sahihu Muslim: 666

2. Tafiya Masallaci cikin Natsuwa: Anaso idan mutum zai je Masallaci to ya tafi a hankali acikin Natsuwa, kada yayi gudu ko yayi sauri wanda ya wuce ƙima.

An rawaito daga Abu Huraira Allah ya ƙara masa yarda yace:

Idan aka tada Sallah to kada kuzo kuna sauri, kuzo kuna tafiya a hankali, kuna cike da natsuwa, duk abinda kuka samu ku Sallata, abinda ya ƙubce muku kuma ku cika.

Sahihul Bukhari: 908. Sahihu Muslim: 602

3. Kada a Haɗa yatsun Hannu biyu a rinƙa motsa su: Hakanan ba’a so wanda yake hanyar zuwa Masallaci ya rinƙa wasa da yatsun sa, ya haɗa yatsun sa biyu yana motsa su, ko wani wasa na daban.

An rawaito daga Abi Huraira Allah ya ƙara masa yarda yace Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace:

Wanda yayi Alwala sannan ya fita yana niyyan zuwa Sallah to yana cikin Sallah ne har sai ya dawo gidan sa, kada yayi Haka(Ya rinƙa haɗa ƴan yastun sa yana motsa su, ko yana wasa dasu)

Addarimi: 1446. Ibnu Khuzaima: 439

4. Shiga Masallaci da Ƙafar Dama: ana so idan Mutum zai shiga Masallaci ya fara shiga da ƙafar dama,

Annabi ya kasance duk abinda zaiyi yana fara wa ne da gefen dama sai abubuwa kaɗan da aka rawaito tsaɓanin hakan kaman wurin shiga bayan gida ko cire takalmi.

Annabi ya kasance yana burge shi ya fara abubuwan sa daga gefen dama, wurin sanya takalmin sa, ko wurin gyara sumar kansa, ko wurin yin tsarkin sa. Haka nan cikin dukkan lamarin sa baki ɗaya.

Sahihul Bukhari: 168. Sahihu Muslim: 268

5. Yin Addu’a idan za’a shiga Masallaci ko za’a fita: Ana so idan Za’a shiga Masallaci ayi addu’a haka nan idan za’a fita ayi Addu’a. An rawaito Addu’oi mabanbanta daga Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi.

An ruwaito daga Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace:

Idan ɗaya daga cikin ku zai shiga Masallaci to yace: ” Allahumma iftah li abwaba rahmatik” idan zai fita yace: “Allahumma inni as’aluka min fadlik”

Sahihu Muslim: 713

Fassarar Addu’ar: Na shiga Masallaci; Ubangiji na Ka buɗe min ƙofofin Rahamar ka,

Na Fita Masallaci; Ubangiji na ina roƙon ka daga cikin falalar ka.

Wannan ɗaya ne daga cikin Addu’oi da aka rawaito daga Annabi.

Allah yasa mudace

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories