Ladduban kwanciya bacci

Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.

Ladduban bacci da Musulmi ya kamata ya kula dasu domin kare kansa daga shaiɗanu, da kuma dacewa da Sunnar Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi wurin yin baccin sa.

1. Kada A kwanta kafin Sallar Isha’i: Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam ya kasance yana ƙin a kwanta kafin Sallar Isha’i. Bukhari: 568. Muslim: 648

2. Yin alwala kafin Bacci: yana da kyau kafin mutum ya kwanta ya tabbata yayi alwala, koda kuwa yana da janaba a jikin sa, idan ba zai samu daman yin wankan tsarƙi ba to sai yayi alwala.

Annabi yace: Idan kayi niyyan zuwa makwancin ka to kayi alwala, Alwala irin ta Sallah

Bukhari: 247. Muslim: 2710

3. Karkaɗe Shimfiɗa Kafin kwanciya: Annabi yayi umarni idan mutum yazo kwanciya to ya karkaɗe makwancin sa kafin ya kwanta. Wannan Hadisi Bukhari da Muslim sun rawaito shi. Bukhari: 6320. Muslim: 2714

4. Kwanciya a gefen dama: idan mutum yazo kwanciya to ya kwanta a gefen sa na dama. Babu laifi idan ya gaji ya juya gefen hagu ko ya kwanta da bayan sa, amma kada ya kwanta a kan cikin sa.

Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace: Idan kayi niyyan zuwa makwancin ka to kayi alwala, Alwala irin ta Sallah, sannan ka kwanta a gefen hanun ka na dama.

Bukhari: 247. Muslim: 2710

5. Ƙulle ƙofofi, da Kwanuka: kafin mutum ya kwanta ya ƙulle ƙofar gidan sa, sannan ya rufe duk wani kwano da yake buɗe.

Bukhari: 2380. Muslim: 2012

6. Kashe Fitilu Ko Gas: Kafin mutum yayi bacci ya kashe duk wani abu da zai iya janyo gobara kaman fitila ko Gas da makamantansu.

Bukhari: 6293. Muslim: 2015

7. Yin Addu’oi kafin bacci: Yana da matuƙar mahimmanci idan mutum zai kwanta ya karanta Addu’oi da suka inganta daga Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi.

Addu’oin da ake Karantawa:

  • Ayatul Kursiyyu: Bukhari ya rawaito shi mu’allaq: 959
  • Karanta Ƙulhuwallahu, da Falaƙ, da Nasi: sai ya haɗa hannayensa biyu sannan ya karanta wa’innan surori sai ya tofa ya shafe jikinsa dasu. Bukhari: 5018
  • Karanta Tasbihi da Tahmidi da Takbiri: kafin ayi bacci sai ayi tasbihi(Subhanallah) sau 33, ayi Tahmidi(Alhamdulillah) Sau 33, ayi Takbiri(Allahu Akbar) sau 34. Bukhari: 5361. Muslim: 2727

Click Here to Support our work

Leave a Reply

%d bloggers like this: