Mu kula da tsabtace hannayenmu kafin bacci

Danna nan domin shiga group na karatu Online

قال رسول الله صلى الله عليه وسلم ” من نام وفي يده غمر ولم يغسله فأصابه شيء فلا يلومن إلا نفسه

رواه أبو داود والترمذي وابن ماجه


Abu Huraira Allah ya ƙara masa yarda ya rawaito hadisi daga Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama yana cewa “Wanda yayi bacci a hanunsa akwai Gurbin Nama ko wani abin ci, bai wanke ba, wani abu ya sameshi to kada ya zargi kowa sai kansa

Wannan hadisi yana koya mana tsabta, ta yadda Annabi yayi gargadi ga masu kwanciya bayan sun ci abinci ba tare da sun wanke hannayensu ba cewa wani abu mummuna ka iya samunsu suna bacci, ta yadda ko wani abu mai dafi zai iya cizonsu ko makamancin haka, sai mu kula da tsabtace hannayenmu da kuma jikunanmu. Allah yasa mudace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories