Haramun ne yin Magana Ranan juma’a a lokacin da Liman yake huɗuba

·

·

Domin neman ƙarin bayani danna nan

Wajibi ne masu jin huɗuban liman ranan juma’a suyi shiru, sannan kuma magana a lokacin da liman yake huɗuba haramun ne.
ba’a maida sallama,
ba’a gaida mai atishawa,
Yana halatta ayi wa Annabi salati a sirrance idan mai huɗubah ya ambaceshi.


Abu Huraira Allah ya ƙara masa yarda ya rawaito hadisi daga Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yace: idan kace wa Wanda kuke tare dashi yi shiru ranar juma’a bayan kuma liman na huɗuba, toh haƙiƙa kayi yasasshen zance.

Bukhari :934


wannan yake nuna girman lamarin, ta yadda koda kaga mutum na surutu sai ka nemi kace masa yayi shiru toh kaima kana da laifi, sai dai kayi masa nuni domin ya gane abinda yakeyi bai dace ba, kaman yadda aka rawaito lokacin da wani ya shigo Masallaci ranar juma’a annabi yana huɗuba sai yake tambayar annabi yaushe ne tashin Al-Qiyama, sai mutane sukayi masa nuni da cewa yayi shiru.

-Albaihaqi 3/221


Babu laifi yin magana kafin liman ya fara huɗuba, ko kuma bayan ya kammala kafin a fara sallah, dalili kuwa shine kaman yadda hadisin da muka kawo ya nuna cewa wannan haramci na samuwa ne a lokacin da liman yake huɗuba.

Haka nan babu laifi yin magana a lokacin da liman ya zauna bayan huɗuban farko kafin ya koma na biyu.


Leave a Reply

Latest updates
Categories