Shin cin naman Rakumi yana warware Alwala?

·

·

Magana mafi inganci Shine Cin naman raƙumi yana warware alwala sabida dalilai kamar haka:

An rawaito daga Jabir Bin Sumrata Allah ya ƙara masa yarda: wani mutum ya tambayi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: Shin zanyi Alwala dun naci naman Tumakai? Sai Annabi yace Masa idan kaga dama kayi alwala, idan kaga dama kada kayi, Sai yace: Shin zanyi Alwala dun naci naman Raƙumi? Sai yace masa Eh kayi alwala idan kaci naman raƙumi.

Muslim: 360

Fuskar Hujjah da wannan Hadisi

Anan Annabi ya tabbatar wa wannan Sahabin cewa zai sake alwala idan yaci naman raƙumi, Sannan ya bashi zaɓi game da Naman tumaki. Wannan yake nuna wajabcin Alwala idan anci naman raƙumi.

Sannan an sake rawaito wa daga Bara’ Bin Aazib Allah ya ƙara masa yarda yace:

An tambayi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi game da alwala don anci naman raƙumi sai yace: Kuyi Alwala.

Abu Dawud: 184. Tirmidhi: 81

Wasu maluman suna ga basai mutum ya sake alwala ba don yaci naman Raƙumi Sabida Hadisin Abi Dawud wanda Sa’id Bin Harith daga Jabir Bin Abdullahi Allah ya ƙara musu yarda.

Ya tambaye shi game da nama da aka gasa, shin za’ayi alwala bayan anci? Sai Jabir yace ƙarshen Umarni da yazo daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallama game da nama da aka gasa shine Ba sai an sake alwala ba

Abu Dawud: 192

Sai dai Kamar yadda mukayi bayani a baya cewa Magana mafi inganci shine Cin naman Raƙumi yana karya alwala, sannan wannan Hadisi gamamme ne, shi kuma Hadisin Jabir da muka kawo a same keɓantacce ne. Ya keɓance naman raƙumi daga cikin sauran namomi da aka gasa. Idan muka ɗauka cewa wannan hadisi na ƙarshen ba’a shafe shi ba.

Sannan akwai wasu da suke kawo wani labari mara tushe suke danganta shi da wannan Hadisi, cewa wai:

Wata rana Annabi yana Huɗuba sai akayi hutu awurin sai wanda yayi yaji kunyan ya tashi, kuma a lokacin yaci naman raƙumi, Sai Wai Manzon Allah yace: Duk wanda yaci naman Raƙumi to yayi alwala, sai wasu mutane suka tashi dama sunci naman raƙumi sai suka fita sukaje sukayi alwala, acikinsu akwai wanda yayi wannan Hutun.

Wannan Labari bai inganta ba kamar yadda Sheikh Nasiruddin Albany ya faɗa Acikin Silsilatud-da’ifah: 3/268

Allah shine mafi sani.

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: