Kyautata alwala yana kankare zunubai

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Abu Huraira Allah ya ƙara masa yarda ya rawaito Annabi Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace:

Idan bawa Musulmi yayi alwala ya wanke fuskarsa, duk wani abu na zunubi da ya kalla da idanunsa zasu fice tare da wannan ruwa, haka nan idan ya wanke hannayensa, duk wani zunubi da ya aikata da wannan hannu zata fita da wannan ruwa, haka nan idan ya wanke ƙafafuwan sa, duk wani taku da yayi wurin aikata zunubi wannan zunubi zai fita da wannan ruwa. Har sai ya zamto ya fice tsaf daga zunubi

Sahih Muslim 244

إِذَا تَوَضَّأَ العَبْدُ المُسْلِمُ، أَوِ المُؤْمِنُ، فَغَسَلَ وَجْهَهُ خَرَجَ مِن وَجْهِهِ كُلُّ خَطِيئَةٍ نَظَرَ إِلَيْهَا بعَيْنَيْهِ مع المَاءِ، أَوْ مع آخِرِ قَطْرِ المَاءِ، فَإِذَا غَسَلَ يَدَيْهِ خَرَجَ مِن يَدَيْهِ كُلُّ خَطِيئَةٍ كانَ بَطَشَتْهَا يَدَاهُ مع المَاءِ، أَوْ مع آخِرِ قَطْرِ المَاءِ، فَإِذَا غَسَلَ رِجْلَيْهِ خَرَجَتْ كُلُّ خَطِيئَةٍ مَشَتْهَا رِجْلَاهُ مع المَاءِ، أَوْ مع آخِرِ قَطْرِ المَاءِ، حتَّى يَخْرُجَ نَقِيًّا مِنَ الذُّنُوبِ


Ta’aliƙi:

Wannan yana daga cikin falalolin Allah da yayi wa wannan Al’ummah ta yadda ya samar mata hanyoyi na tuba da kuma kankare zunubai masu yawa. Kyautata alwala yana daga ciki kamar yadda muka gani cikin wannan hadisi.

Haka nan raka’a biyu bayan mutum yayi alwala shima yana kankare zunubai kaman yanda Annabi yayi bayani cewa:

Wanda ya kyautata alwala yayi shi kamar yadda ya koyar ya tashi yayi sallah raka’a biyu baya tunanin wani abu cikin Sallar sa, Allah zai gafarta masa zunubansa baki ɗaya.

haka nan kuma Juma’a zuwa Juma’a shima Allah yana gafarta zunubai tsaƙaninsu,

Haka nan Azumin Aashura, Da kuma ranar Arafa.

Sai muyi ƙoƙari wurin ribatar wannan lokuta. Allah yasa mudace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories