Bambanci tsakanin Maniyyi Da maziyyi wa wadiy da hukuncinsu

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Assalamu Alaikum warahmatullah wabarkatuh, yau a fagen Fiqhu zamu dubi abubuwa guda uku wanda suke da alaka da tsarki, abubuwan sune Maniyyi, da maziyyi da wadiy,

1.maniyyi: Shi wannan wani ruwa ne da yake fitowa lokacin Yin jima’i ko mafarki ko makamantansu, yana da kauri in na namiji ne, inkuma ta macece yana nan tsiriri kuma yana fita da karfi, yana bibiyar juna.
Hukuncin maniyyi: Akwai tsabani tsakanin maluma kan kasancewar maniyyi najasa ne ko ba najasa ba,
abinda ya dace mutum dai yayi in maniyyi ta shafi tufafinsa ko jikinsa shine in maniyyin bai bushe ba sai ya wanke wurin da ruwa, inkuma ya bushe sai ya kankareshi.
sannan hukuncin wanda maniyyin ta fito daga jikinsa, shine zaiyi wankan janaba, In maniyyin ya fito ta jima’i ne ko mafarki, hakanan mutumin daya farka daga bacci yaga maniyyi ajikinsa Shima zaiyi wanka. amma in mutum yayi mafarki ya tashi baiga wani maniyyi ajikinsa ba toh babu wani wanka akansa. hakanan mutumin da yake farke maniyyi ta fito ba tare da wata sha’awah ba, haka kawai ta fito kodun ciwo ko wahala, shima wannan babu wanka akansa.
2.Maziyyi: Shi Maziyyi wani ruwane da yake fita sakamakon tashiwar sha’awah, Yafi fitsari kauri, Sannan yana fita batare da jin dadi ko sanin mutum ba sai dai mutum inyaji tufafinsa ta dan jike,
Hukuncin maziyyi: Shi maziyyi najasane amma mai Sauki, Zai isar wurin tsarki daga gareshi jike inda ya taba ajikin tufafi da ruwa, sannan hukuncin wanda maziyyi ya fita daga jikinsa shine ya wanke farjinsa Da inda ya taba sannan in yana da alwala sai ya sake wata. shi maziyyi ba’a masa wanka.
3.Wadiy: Shi wadiy wani ruwa ne da yake fita a karshen fitsari ya bambanta da fitsari, Shima najasa ne, kuma in ya taba tufafi sai an wanke inda ya taba kaman fitsari, sannan a wanke farji, da kuma sake alwala. a takaice hukuncinsa hukuncin fitsari ne.
Wassalamu  Alaikum.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

5 responses to “Bambanci tsakanin Maniyyi Da maziyyi wa wadiy da hukuncinsu”
  1. Hassan Bako Dambatta Avatar
    Hassan Bako Dambatta

    Allah ya saka da alheri

  2. Fatima saidu Abubakar Avatar
    Fatima saidu Abubakar

    jazakallah bi khair brother.gaskiya na karu

  3. ibrahim umar Avatar

    Allah ya sakawa da malam gidan Aljanna

  4. Sulaiman Avatar
    Sulaiman

    Menene yake kawo wannan.idan mutum ya kwanta kuma yayi mafarkin saduwa da mace amma ya tashi bega maniyyi ba

  5. Mudassir Avatar
    Mudassir

    wannan yayi

Leave a Reply

Latest updates
Categories