Fikhu: Sharrudan Sallah: Wajabci Da Inganci

Sallah yana daga cikin Rukunai na Musulunci, Wajibi ne akan kowani Musulmi ya tsayar da Sallah kamar yadda Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya koyar.

Sallah yana da sharruɗa wanda sai an samesu kafin Sallah ta zamto ta wajaba akan Mutum ko ta zamto karɓabbiya.

Sharuɗan Wajabci

Sallah tana wajaba akan Mutum ne idan ya cika wa’innan Sharuɗa.

  1. Musulunci: Mutum ya zamto Musulmi
  2. Balaga: Ya zamto mutum ya balaga
  3. Hankali: Ya zamto mutum na cikin hankalin sa
  4. Tsarki daga jinin haila da Jinin haihuwa

Sharuɗan ingancin Sallah

  1. Tsarƙi daga Hadasi da Najasa: Ya zamto mutum yana da tsarki, bai yi wani abin da ya warware masa alwala ba, haka nan babu najasa a jikinsa ko wurin Sallar sa.
  2. Shigan lokaci: ya zamto anyi Sallah acikin lokacin ta, kada ayi kafin lokaci, haka nan kada ayi bayan lokacin ta ya wuce
  3. Fuskantar Alƙibla
  4. Suturce Al’aura.

Click Here to Support our work

Leave a Reply

%d bloggers like this: