Mahimman abubuwa daga khudbar Juma'an yau 20/12/1434 wanda ya dace da 25/10/2013 Masallacin Azeez Billah, zeiton

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Da sunan Allah mai rahama Mai jin kai.
Yau khudubarmu ta shafi Bin umarnin Allah da kuma Bin Umarnin manzon Allah(sallallahu alaihi wasallam) da koyi dashi.
Sannan kuma da tasirin aikin alheri a harkokin mumini..
Yana Daga Cikin tabbatuwar karbuwar ibada da tasirinta aganta tana canza halayen mutum. Shin ibadannan sallah ce, azumi, ko hajji. Bawai mutum yana sallah amma daga fitarsa a masallaci sai kaga mu’amallarsa sam bata da kyau baibar cin riba ba, bai bar wasu munanan abubuwa ba. To hakan ya zamto cewa ibadan batada tasiri akansa ba kenan.. Zai iya yiwuwa yanayin ibadanne domin kore zargin mutane, ko kuma Sauke nauyinta akansa. Ko kuma yana yinta ba yadda Allah(subhanahu wata’ala) ya tsara ba, kokuma ba yadda annabi muhammad(sallallahu alaihi wasallam) ya koyarba. Toh da zarar haka ta samu, toh hakika mutum bazai sami tasirin Aikin da yakeyi a jikinsa ba da mu’amalolinsa. Wannan cuta itace take damun al’ummar musulmai. Domin Inda musulmai zasu zamto cewa ibadun da sukeyi tana tasiri A jikinsu, toh da hakika da rayuwarsu ta canzu..
Sannan malam acan karshe yace kodashike akwai wasu yanzu masu da’awah ta cewa a rabe Addini da rayuwa. Ya zamto cewa addini dabam rayuwa dabam.. Wannan ba karamar Musiba bace wadda bai dace ta sami mazauni cikin zuciyar mumini ba. Ya kamata duk komai da mukeyi ya zamto koyi mukeyi. Cikin mu’amalla da ibada. Domin dominsa aka haliccemu…
Daga karshe ni kuma nace… Masu ikrarin rabe siyasa da addini kuji tsoron Allah. Wassalam..

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories