BAYANI AKAN AIKIN HAJJI Futowa ta 1(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

BAYANI AKAN AIKIN HAJJI
Futowa ta 1
WANDA HAJJI TA WAJABA A
KANSA
Aikin hajji yana wajaba ne akan
wanda Allah ya bashi iko.
Iko shine:
-lafiya
-guziri
-amincin hanya
Duk wanda Allah ya hada masa
wadannan abubuwa to, wajibine
ya gaggauta tafiya, matukar babu
wani uziri da zai hana shi, wannan
ita ce magana mafi rinjaye.
Dalili kuwa shine fadinsa
subhanahu wa ta‘ala;
ﻭ ﺳﺎﺭﻋﻮﺍ ﺇﻟﻰ ﻣﻐﻔﺮﺓ ﻣﻦ ﺭﺑﻜﻢ
Ma‘ana:
Ku yi gaggawar zuwa ga neman
gafara daga Ubangijinku…..
Da kuma fadinsa:
ﻓﺎﺳﺘﺒﻘﻮﺍ ﺍﻟﺨﻴﺮﺍﺕ
Ma‘ana;
Kuma kuyi tsere zuwa ga aiyukan
alheri….
Wadannan ayoyi na umarni ne
akan gaggautawa zuwa ga duk
wani aikin alheri da shari‘a ta yi
umarni da shi.
Wanda kuwa Allah ya bashi iko
amma bai je ba har ajali ya zo
masa, to, akwai barazana a kansa
domin butulcewa ni‘imar Allah da
ya yi.
Dalili kuwa shine fadinsa
subhanahu wa ta‘ala cewa;
ﻭﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺣﺞ ﺍﻟﺒﻴﺖ ﻣﻦ ﺍﺳﺘﻄﺎﻉ ﺇﻟﻴﻪ ﺳﺒﻴﻼ
ﻭﻣﻦ ﻛﻔﺮ ﻓﺈﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻏﻨﻲ ﻋﻦ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ
Ma‘ana:
Hakkin Allah ne akan mutane su
hajjaci dakin (Ka‘aba), ga wanda
ya sami ikon zuwa gare shi, kuma
wanda ya kafirta (ya butulcewa
Allah), to lallai Allah mawadaci ne
daga dukkan talikai.
WANDA YA MUTU BAI SAMU
DAMAR YIN AIKIN HAJJI BA:
Wanda bai samu damar yin aikin
hajji ba har ya mutu, za a iya yi
masa;
Ko yayi wasiyya akan ayi masa ko
bai yi ba,
Ko bakance ne ko ba shi ba,
Ba sai iyaye ba hatta dan uwa ana
iya yi masa,
Kuma namiji yana iya yiwa mace,
kuma mace tana iya yi wa namiji.
Dalilai suna da yawa, daga cikinsu
akwai hadisi da ya tabbata daga
Abdullahi Ibn Abbas radhiyallahu
anhuma, wata mace ta tambayi
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama akan bakance da
mahaifiyarta ta yi na yin hajji,
amma ba ta yiba har ta mutu, sai
ya ce:
ﺣﺠﻲ ﻋﻨﻬﺎ… ﺍﻟﺦ
Ma‘ana: ki yi mata hajjin (da bata
yi ba).
Haka kuma ya ruwaito cewa:
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya ji wani mutun yana
yiwa dan uwansa mai suna
Shubrumah hajji, sai ya tambaye
shi, ka yiwa kanka? Sai ya ce a‘a,
sai ya ce:
ﺍﺟﻌﻞ ﻫﺬﻩ ﻋﻦ ﻧﻔﺴﻚ ﺛﻢ ﺣﺞ ﻋﻦ ﺷﺒﺮﻣﺔ
Ma‘ana:
Ka sanya wannan ta zama ta ka,
sannan (a wata shekara) ka yiwa
Shubrumah.
Wannan ya nuna cewa wani yana
iya yiwa wani aikin hajji idan ya
mutu bai yi ba.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories