HUKUNCE-HUKUNCEN HAJJI Fitowa ta 2(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Danna nan domin shiga karatu Online

HUKUNCE-HUKUNCEN HAJJI
Fitowa ta 2
WANDA YA SAMU IKON ZUWA
HAJJI AMMA IYAYENSA BASU
SAMU IKON ZUWA BA
Mutumin da Allah ya bashi ikon
zuwa hajji amma iyayensa basu
samu ikon zuwa ba, zai fara sauke
nauyin da ke kansa ne, saboda
fadin Allah subhanahu wa ta‘ala:
ﻭﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺣﺞ ﺍﻟﺒﻴﺖ ﻣﻦ ﺍﺳﺘﻄﺎﻉ ﺇﻟﻴﻪ ﺳﺒﻴﻼ
Ma‘ana:
Kuma hakki ne na Allah akan
mutane su hajjanci dakin (Ka‘aba)
ga wanda ya samu ikon zuwa gare
shi…
Tunda dai shine Allah ya baiwa iko
ba su ba, to, shine hajjin ta wajaba
a kansa.
A bayanin da ya gabata, an ji cewa
mutun na iya yiwa iyayensa ko ‘yan
uwansa hajji idan sun mutu basu yi
ba, amma sai idan ya yiwa kansa.
Muna ganin iyayen mu mata suna
yawan yin dawafi da niyyar Allah
ya kai ladan ga iyayensu,
maimakon su yi musu addu‘a,
wannan bai zo a sunnah ba.
Idan kuma Allah ya horewa mutun
ta yadda zai iya biyawa kansa tare
da wani ko wasu, to, iyaye sune a
gaba da matansa ko ‘ya ‘yansa da
sauransu.
HUKUNCIN ZUWA HAJJI DA
KUDIN ADASHI
Mutumin da ya dauki adashin da
ana binsa ragowar zubi, zai iya
tafiya hajji idan abokan adashinsa
sun yarda, idan basu yarda ba to,
sai ya hakura har sai ya gama
zubi, domin hukuncinsa, hukuncin
wanda ake bi bashi ne. Allah bai
kallafawa bawa zuwa hajji da
kudin bashi ba, sai dai idan masu
bashin sun lamunce masa.
WANDA AKA BIYAWA HAJJI DA
KUDIN HARAM, KO KUDIN
GWAMNATI
Bai halatta ba a biyawa mutun
hajji, ko shi ya biyawa kansa da
kudin haram, kamar kudin sata, ko
kudin riba (interest), ko kudin giya
da makamantansu, saboda hadisi
ya tabbata daga Abu Hurairata
radhiyallahu anhu, daga Manzon
Allah sallal lahu alaihi wa sallama
ya ce:
ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﻃﻴﺐ ﻻ ﻳﻘﺒﻞ ﺇﻻ ﻃﻴﺒﺎ
Ma‘ana:
Hakika Allah tsarkakakke ne, kuma
ba ya karba sai tsarkakakke.
Saboda haka wanda aka biyawa
hajji da dukiyar haram, hajjinsa ba
karbabbe ba ne. Wallahu a‘alam.
Amma wanda gwamnati ta biyawa
hajji daga baitul mali don ya
cancanta, ba don siyasa, ko
dangantaka ba, ko kuwa aka biya
masa don ilmantar da alhazai, ko
kula da lafiyar su da sauran aiyuka,
ko kuma shugaban ya biya masa
ne daga kudinsa na halal, wannan
babu laifi.
Wa sallallahu wa sallama ala
Nabiyiina Muhammadin wa ala
Aalihi wa Sahbihi ajma’in.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates