Mas'alolin aure Fitowa ta 11(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Muna cikin bayani akan nau’ikan aure da musulunci ya tarar ana yi ya hana. Mun yi bayani akan auren shigari da auren kisan wuta.
TAMBAYA:
Mene ne auren mutu’a kuma mene ne hukuncinsa?
AMSA:
Malamai sun ce; ma’anar kalmar “mutu’a” a harshen Larabci ita ce:
الإنتفاع
Ma’ana:
Amfanuwa.
Kuma ana cewa:
تمتعت بكذا
Ma’ana:
Na amfanu da abu kaza.
Daga nan aka samu mutu’ar aure, da mutu’ar saki da kuma mutu’ar aikin hajji, domin dukkansu amfanuwa ne.
Amma ma’anarsa a shari’a shi ne; mutum ya auri mace zuwa wani lokaci, tare da ba ta wani abu, kuma wannan lokacin ya kasance sananne ne, ko ba sananne ba ne.
TARIHIN AUREN MUTU’A
Auren mutu’a yana daga cikin auren Jahiliyya. Mutum yana auren mace zuwa wani lokaci sannan ya rabu da ita, kuma ba sa ganin wani aibu akan yin hakan. Da addinin Musulunci ya zo sai ya yi shiru a kansa, har zuwa lokacin yakin Khaibar a shekara ta bakwai bayan hijira. Kamar yadda ya tabbata daga Sayyadina Aliyu radhiyallahu anhu ya ce:
أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم نَهَى عَنْ مُتْعَةِ النِّسَاءِ يَوْمَ خَيْبَرَ وَعَنْ أَكْلِ لُحُومِ الْحُمُرِ الإِنْسِيَّةِ.
Ma’ana:
Hakika Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya hana yin auren mutu’a, da kuma cin naman jakin gida a ranar yakin Khaibar.
Al’amarin ya ci gaba da gudana a kan haramci, har zuwa lokacin da aka yi Fat’hu Makka, sai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya halatta shi kwana uku, bayan wadannan kwanakin kuma ya haramta shi har zuwa tashin alkiyama.
LAFUZZAN DA MAZHABOBI HUDU SUKA YI AMFANI DA SU DON BAIYANA
MA’ANAR AUREN MUTU’A:
1-Malikiyya suka ce auren mutu’a shine: Kulla aure da lafazin da yake nuna iyakance masa wani lokaci. Kamar miji ya ce da waliyyin mace, ka aura min ita wata daya a kan kaza, ko kuma ya ce; na karbi auren ta zuwa wata daya akan kaza.
2-Shafi’iyya suka ce auren mutu’a shine; Kulla aure zuwa wani lokaci.
3-Hambaliyya suka ce auren mutu’a shine; Mutum ya auri mace zuwa wani lokaci, kuma lokacin ya zama sananne ne ko ba sananne ne ba.
4-Hanafiyya suka ce auren mutu’a shine; Mutum ya ce da mace, zan yi auren mutu’a da ke zuwa wani lokaci. Misali: kwana goma ko wata ko shekara. Ko kuma ya ce; ki ba ni dama na yi mutu’a da ke zuwa wani lokaci.
HUKUNCIN AUREN MUTU’A
Shi’a Imamiyya sun halatta shi. Sun kafa hujja a cewar su, da Al-Qur’ani da maganar wasu sahabbai da hujja ta hankali da kuma ijma’i.
1- Dalilinsu a cikin Al-Kur’ani mai girma shi ne: fadin Ubangiji subhanahu wa ta’ala cewa:
…فَمَا اسْتَمْتَعْتُمْبِهِ مِنْهُنَّ فَآتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ فَرِيضَةً… النساء: 24
Ma’ana:
… Abin da kuka ji dadi da shi daga gare su(mata), to, ku ba su ladansu na sadaki…
Sai suka dauki kalmar istimta’i a matsayin mutu’a, kalmar ujurahunna kuma suka dauke ta a matsayin ladan mutu’ar. Sannan suka ce abin da yake karfafa wannan ra’ayi nasu dangane da wannan ayar shi ne kira’ar Ubayyu Ibn Ka’ab da Abdullahi Ibn Abbas radhiyallahu anhuma inda suka karanta ayar kamar haka:
…فَمَا اسْتَمْتَعْتُمْبِهِ مِنْهُنَّ إِلَى أَجَلٍ …
Ma’ana:
Abinda kuka ji dadi da su(mata) zuwa wani lokaci…
Sai suka ce wannan ya bayyana karara cewa; ayar a kan mutu’a take magana.
2-Dalilinsu Daga Maganar Sahabbai Shine:
i- An rawaito cewa Ibn Abbas radhiyallahu anhu ya kasance yana ba da fatawa a kan yin mutu’a.
ii- An rawaito daga Jabir Ibn Abdullah radhiyallahu anhuma ya ce:
كُنَّا نَسْتَمْتِعُ بِالْقُبْضَةِ مِنَ التَّمْرِ وَالدَّقِيقِ الأَيَّامَ عَلَى عَهْدِ رَسُولِ اللَّه صلى الله عليه وسلم وَأَبِى بَكْرٍ حَتَّى نَهَى عَنْهُ عُمَرُ…
Ma’ana:
Mun kasance muna mutu’a da cikon tafi na dabino da gari (garin Alkama) a zamanin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama da Sayyadina Abubakar radhiyallahu anhu, har saida Sayyadina Umar radhiyallahu anhu ya hana…
Sai suka ce; tunda an yi auren mutu’a a zamanin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama da Halifa Abubakar radhiyallahu anhu, wannan ya nuna halaccin yinsa kenan, amma sai Halifa Umar radhiyallahu anhu ya hana.
3- Dalilinsu na hankali suka ce; Auren mutu’a amfani ne da ya kubuta daga kowace fuska ta muni, kuma ba a samu wata cutarwa tattare da shi ba. Duk kuwa abin da ya zama haka, to, ya halatta.
4- Dalilinsu na ijma’i kuwa: Suka ce dukkanin Ahlulbaiti sun tafi a kan halaccin yin auren mutu’a.
Tunda mun ji dalilansu, yanzu saura tattaunawa game da wadannan dalilai na su da suka gabata. Allah ya bamu ikon ci gaba. Wa sallallahu wa sallama ala Nabiyyina Muhammad wa ala a’lihi wa sahbihi ajma’iin.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories