Mas'alolin aure Fitowa ta 7Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Domin neman ƙarin bayani danna nan

TAMBAYA:
Wadanne irin mata ne Shari`a ta haramta auren su?
AMSA:
Ubangiji subhanahu wa ta’ala ya bayyana matan da ya haramta a aure su a littafinSa mai girma, inda yake cewa;
وَلَا تَنْكِحُوا مَا نَكَحَ آبَاؤُكُمْ مِنَ النِّسَاءِ إِلَّا مَا قَدْ سَلَفَ إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَمَقْتًا وَسَاءَ سَبِيلًا (22) حُرِّمَتْ عَلَيْكُمْ أُمَّهَاتُكُمْ وَبَنَاتُكُمْ وَأَخَوَاتُكُمْوَعَمَّاتُكُمْ وَخَالَاتُكُمْ وَبَنَاتُ الْأَخِ وَبَنَاتُ الْأُخْتِ وَأُمَّهَاتُكُمُ اللَّاتِي أَرْضَعْنَكُمْ وَأَخَوَاتُكُمْمِنَ الرَّضَاعَةِ وَأُمَّهَاتُ نِسَائِكُمْ وَرَبَائِبُكُمُاللَّاتِي فِي حُجُورِكُمْ مِنْ نِسَائِكُمُ اللَّاتِي دَخَلْتُمْ بِهِنَّ فَإِنْ لَمْ تَكُونُوا دَخَلْتُمْ بِهِنَّ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ وَحَلَائِلُ أَبْنَائِكُمُ الَّذِينَ مِنْ أَصْلَابِكُمْ وَأَنْ تَجْمَعُوا بَيْنَ الْأُخْتَيْنِ إِلَّا مَا قَدْ سَلَفَ إِنَّ اللَّهَ كَانَ غَفُورًا رَحِيمًا (23) وَالْمُحْصَنَاتُ مِنَ النِّسَاءِ إِلَّا مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ… النساء: 24-22
Ma’ana:
Kada ku auri matan da iyayenku maza suka aura, face abin da ya gabata, hakika (aikata hakan) ya kasance alfasha ne da abin ki, kuma hanyar ta munana. An haramta muku (auren) uwayenku, da `ya`yanku mata, da `yan’uwanku mata, da goggonninku, da innoninku, da `ya`yan dan uwa, da `ya`yan ‘yar uwa, da uwayenku wadanda suka shayar da ku, da `yan’uwanku mata na shayarwa, da uwayen matanku, da agololinku wadanda suke cikin gidajenku;(‘ya’ya mata ) na matanku wadanda kuka tara da su, idan kuma ba ku tara da su ba, to, babu laifi a kanku ku aure su (su agololin naku), da matan `ya`yanku na tsatso, kuma kada ku hada `yan’uwa biyu mata (ku aure su), face abin da ya gabata. Hakika Ubangiji ya kasance mai gafara ne kuma mai jin kai. Haka kuma an haramta muku (auren) katangaggun mata (wato matan da suke karkashin aure), saidai abin da kuka mallaka na daga kuyangi……….
Kuma hadisi ya tabbata daga Abu Huraira radhiyallahu anhu ya ce; Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce:
لاَ يُجْمَعُ بَيْنَ الْمَرْأَةِ وَعَمَّتِهَا وَلاَ بَيْنَ الْمَرْأَةِ وَخَالَتِهَا.
Ma`ana:
Ba a hada mace da goggonta (`yar’uwar mahaifinta) ko kuma mace da innarta ( `yar’uwar mahaifiyarta) (a karkashin igiyar auren miji daya).
Don haka a nan za mu fahimci cewa matan da shari`ar Musulunci ta haramta a aura sune kamar haka;
1- Mahaifiyar mutum ko kuma matan da mahaifinsa ya aura.
2- `Ya`ya mata da mutum ya haifa.
3- `Yan’uwa mata wadanda suke uwa daya uba daya da mutum, ko kuma uba daya, ko kuma uwa daya.
4- Goggo: wato kanwar mahaifi ko yayarsa, wadda suke daki daya, ko kuma uba daya, ko kuma uwa daya da shi.
5- Inna: wato kanwar mahaifiya ko kuma yayarta, wadda suke daki daya da mahaifiyarsa, ko kuma uba daya suke da ita. ko uwa daya.
6- `Ya`ya matan da `yan’uwansa suka haifa. Wato `ya`yan `yan’uwa wadanda suke uwa daya uba daya da shi, ko uwa daya ko uba daya da shi.
7- Matan da suka shayar da mutum nono a lokacin da yake bukatar shayarwa wato yayin da yake jariri.
8- `Yan’uwa mata ta bangaren shayarwa. Kuma dangantakar shayarwa tana haramta duk abin da dangatakar jini take haramtawa na aure. Misali, idan mace ta shayar da yaro ko yarinya, to, duk `ya`ya matan da suka haramta ga yaran da ta haifa sun haramta ga wadannan yaran da ta shayar. Wato abin nufi a nan shine duk yaron da mace ta shayar ana daukarsa kamar dan da ta haifa na cikinta ne a dangantakar aure, ko da ba ita ce ta haife shi ba.
9- Mahaifiyar mata, haramun ne a aure ta, matukar an daura aurensa da `yarta, ko da kuwa bai tara da `yar ba.
10- Agola: ita ce `yar matar mutun da ba shi ya haife ta ba, idan.kuma ya tara da mahaifiyarta, to, ta haramta a gare shi. Amma idan bai tara da mahaifiyarba, to, zai iya auren ta, bayan sun rabu da mahaifiyar ta ta ko ta rasu.
11- Matan da `ya`yan mutun na tsatsonsa suka aura, haramun ne ya aure su idan suka sake su ko suka mutu suka bar su. Amma `ya`yan da mutun ya raina, ko kuma matan `yan’uwa, ko matan ‘ya’yan ‘yan uwa, ba haramun ba ne a aure su, idan sun sake su ko sun mutu sun bar su. Sai dai a hakura da auren na su don kara, da gudun rikice-rikice a cikin dangi.
12- Haka kuma hada `yan’uwa mata biyu, kamar ya da kanwa, wadanda suke uwa daya uba daya, ko uwa daya, ko kuma uba daya. Amma idan aka saki daya, to, za a iya auren dayar, bayan waccan ta gama idda, ko idan rasuwa ta yi.
13- Sai kuma hada mace da goggonta ko kuma innarta, shi ma haramun ne, sai dai idan aka saki daya, to, za a iya auren dayar bayan waccan ta gama idda, ko idan ta rasu.
14- Haka kuma an haramta auren katangaggun mata (wato matan da suke karkashin aure), sai dai kuyangu wadanda aka ribace su a fagen yaki, to, wannan ya halatta a aure su koda suna da aure kafin a ribato su.
15- Da kuma auren mace fiye da hudu, shi ma haramun ne. Saboda hadisin da ya tabbata daga Abdullahi Ibn Abbas radhiyallahu anhu ya ce:
ما زاد على أربع فهو حرام كأمه وابنته وأخته
Ma’ana:
Wanda ya auri mace fiye da hudu, to, (ta biyar din) ta haramta a gare shi, kamar yadda mahaifiyarsa da `yarsa da `yar’uwarsa suka haramta a gare shi.
Wadannan mataye da aka jero a sama sune wadanda aurensu ya haramta ga mutum. A cikinsu akwai wadanda haramun ne har abada, sannan kuma akwai wadanda suke haramun ne zuwa wani lokaci. Sai dai kuma akwai wadansu dangogin aure da mutane suke tsammanin haramun ne, amma kuma a shari’ance ba haramun ba ne, ana barin su ne kawai don kara da gudun rashin jituwa da za su iya samuwa a sanadiyar hakan. Ga su kamar haka;
1- Mutum ya auri matar sirikinsa wadda ba ita ta haifi matarsa ba; wannan auren ba haramun ba ne. Dalili kuwa shi ne, an rawaito cewa:
وجمع عبد الله بن جعفر بين ابنة علي وامرأة علي
Ma’ana:
Abdullahi Ibn Ja’afar Ibn Abi Dalib radhiyallahu anhu (sirikin Sayyiduna Aliyu radhiyallahu anhu ne, bayan Sayyiduna Aliyu radhiyallahu anhu ya rasu, sai) ya hada (ya auri) matarsa (mai suna Laila Bint Mas’ud) kuma ya hada su da ‘yar saiyiduna Aliyu radhiyallahu anhu da yake aure.
2- Hada auren `yar wa da `yar kani a karkashin igiyar aure daya; shi ma wannan auren ba haramun ba ne. Dalili kuwa shine, an rawaito cewa:
وجمع الحسن بن الحسن بن علي بين ابنتي عم في ليلة
Ma’ana:
Alhasan Ibn Alhasan Ibn Aliy (Rahimahullah) ya hada (ya auri) ‘ya ‘yan baffanni biyu; ( `yar Muhammad Ibn Aliyu da `yar Umar Ibn Aliyu) a dare daya.
3- Haka kuma ko da tsautsayi zai sa mutum ya yi zina da mace (Allah ya kiyashe mu), to, babu laifi ya auri mahaifiyarta ko `yar’uwarta. Domin an rawaito hadisi daga Abdullahi Ibn Abbas radhiyallahu anhu ya ce:
إذا زنى بأخت امرأته لم تحرم عليه امرأته
Ma’ana:
Idan mutum ya yi zina da `yar’uwar matarsa, to, matarsa ba ta haramta a gare shi ba.
A cikin wani hadisin kuma Abdullahi Ibn Abbas radhiyallahu anhu cewa ya yi:
إذا زنى بها لم تحرم عليه امرأته
Ma’ana:
Idan mutum ya yi zina da (mahaifiyar matarsa), to, matarsa ba ta haramta a gare shi ba.
Allah ya kiyashe mu.

Leave a Reply

Latest updates
Categories