Mas'alolin aure. Fitowa ta 5(Sheikh Abdulwahhab Abdullah )

Danna nan domin shiga karatu Online

TAMBAYA
Wane irin narko Shari`a ta yi tanadi ga wanda yake da ikon yin aure amma ya ki yi?
AMSA:
Shari’a ta nuna cewa wanda yake da ikon aure amma ya ki yi, ba tare da uzuri ba; to, ba zai kasance tare da Manzon Allah sallallah alaihi wa sallama. ba, domin hadisi ya tabbata daga Anas Ibn Malik radhiyallahu anhu,cikin tsawo cewa:
جاء ثلاث رهط إلى بيوت أزواج النبي صلى الله عليه و سلم يسألون عن عبادة النبي صلى الله عليه و سلم فلما أخبروا كأنهم تقالوها فقالوا أين نحن من النبي صلى الله عليه و سلم ؟ قد غفر الله له ما تقدم من ذنبه وما تأخر قال أحدهم أما أنا فإني أصلي الليل أبدا وقال آخر أنا أصوم الدهر ولا أفطر وقال آخر أنا أعتزل النساء فلا أتزوج أبدا فجاء رسول الله صلى الله عليه و سلم فقال ( أنتم الذين قلتم كذا وكذا ؟ أما والله إِني لأخشاكم لله وأتقاكم له لكني أصوم وأفطر وأصلي وأرقد وأتزوج النساء فمن رغب عن سنتي فليس مني
Ma’ana:
Wasu mutane guda uku sun zo gidan Manzon Allah sallallah alaihi wa sallama. suna tambayar matansa game da ibadarsa, da aka fada musu sai suka yi kamar sun ga karancinta (wato ibadar suka ga ba yadda suka yi tsammani ba), sai suka ce: ta ina za mu hada kanmu da Annabi mu wanda an gafarta masa abin da ya gabata daga zunubansa da wanda bai yi ba. Sai daya daga cikinsu ya ce: ni dai zan rika sallar dare har iya rayuwatzaa ba zan yanke ba, na biyun kuma ya ce: ni zan rika azumi har iya rayuwata ba zan yanke ba, na ukun kuma ya ce: ni zan nisanci mataye ba zan yi aure ba har iya rayuwata. Sai Manzon Allah sallallah alaihi wa sallama ya zo ya ce: ku ne kuke cewa kaza da kaza? To, wallahi na fi ku tsoron Allah, amma nakan yi azumi kuma nakan sha, nakan yi sallar dare kuma nakan yi bacci, sannan kuma ina auren mata, to, wanda baya kwadayi sunnata ba ya tare da ni.
Kuma yaya rayuwar wanda ba ya tare da Manzon Allah za ta kasance a nan duniya, ballantana kuma a lahira.
Feb 15 · Like · ReportAbdulQadir Muhammad Bello and 87 others like this.
View previous comments
Muhyiddin Garba
ALLAH KA KARAMANA ZAMAN LAFIYA DA NAMU MATAN ANIN.
Like · 1 · Feb 16
Rabiu Abdullahi Musa
Zai kasance mara nutsuwa a duniya alahira kuma danwuta alla yakiyaye.
Like · 1 · Feb 16
Salisu Muhammad Abdullahi
Ya Allah ka azirtamu daga falalarka muyi aure
Like · 1 · Feb 16
Sani Tukur
Jazakallahu Khairan…..
Like · 1 · Feb 16
Ibrahim Musa Gwale Kano
MAI UZURI KUMA TO, ALLAH YA BA SHI DAGA FALALAR DUNIYA A LAHIRA KUMA A ZA’BA MASA WADANDA MATAN YANZU YA KAMATA SU KWAIKWAYA – SON MIJI DON YA SO ALLAH, – AMANA, – YABAWA ALLAH DA GASKE, :::AAMEEN

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates