Mas'alolin aure Fitowa ta 21(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Wasu daga cikin ku da suke bin
mu a wannan darasi, za su so su yi
tambaya akan wadan su al’adu da
ake yi a lokacin aure, kamar kamu
da mata suke yi, hudubar da ake
yiwa amarya kafin a kai ta, da
kuma kabaki da ake yi bayan an
gama daura aure ta bangaren
ango, da kuma yadda walima take
a sunnah, da yadda magabata
suke gabatar da bukukuwan aure,
amma a yau za mu fara da abinda
ya shafi kamu.
TAMBAYA:
Shin kamun amarya ya sabawa
shari`a ko al’adarmu ta gari?
AMSA:
Babu laifi a yi kamun amarya,
domin a yi mata ado da kwalliya ko
a koya mata yadda za ta gyara
kanta a gidan miji, matukar ba a
saka maguzanci da munanan
al’adu a ciki ba, kamar yi wa
amarya wanka tsirara a kan turmi
ko yin turgeza da yin wakoki na
batsa da sauransu. Domin hadisi
ya tabbata daga Nana A’isha ﺭﺿﻲ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ta ce:
…ﻓﺄﺗﺘﻨﻲ ﺃﻣﻲ ﺃﻡ ﺭﻭﻣﺎﻥ ﻭﺇﻧﻲ ﻟﻔﻲ ﺃﺭﺟﻮﺣﺔ
ﻭﻣﻌﻲ ﺻﻮﺍﺣﺐ ﻟﻲ ﻓﺼﺮﺧﺖ ﺑﻲ ﻓﺄﺗﻴﺘﻬﺎ ﻻ ﺃﺩﺭﻱ
ﻣﺎ ﺗﺮﻳﺪ ﺑﻲ ﻓﺄﺧﺬﺕ ﺑﻴﺪﻱ ﺣﺘﻰ ﺃﻭﻗﻔﺘﻨﻲ ﻋﻠﻰ ﺑﺎﺏ
ﺍﻟﺪﺍﺭ ﻭﺇﻧﻲ ﻷﻧﻬﺞ ﺣﺘﻰ ﺳﻜﻦ ﺑﻌﺾ ﻧﻔﺴﻲ ﺛﻢ ﺃﺧﺬﺕ
ﺷﻴﺌﺎ ﻣﻦ ﻣﺎﺀ ﻓﻤﺴﺤﺖ ﺑﻪ ﻭﺟﻬﻲ ﻭﺭﺃﺳﻲ ﺛﻢ
ﺃﺩﺧﻠﺘﻨﻲ ﺍﻟﺪﺍﺭ ﻓﺈﺫﺍ ﻧﺴﻮﺓ ﻣﻦ ﺍﻷﻧﺼﺎﺭ ﻓﻲ ﺍﻟﺒﻴﺖ
ﻓﻘﻠﻦ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺨﻴﺮ ﻭﺍﻟﺒﺮﻛﺔ ﻭﻋﻠﻰ ﺧﻴﺮ
ﻃﺎﺋﺮﻓﺄﺳﻠﻤﺘﻨﻲ ﺇﻟﻴﻬﻦ ﻓﺄﺻﻠﺤﻦ ﻣﻦ ﺷﺄﻧﻲ ﻓﻠﻢ
ﻳﺮﻋﻨﻲ ﺇﻻ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭ ﺳﻠﻢ
ﺿﺤﻰ ﻓﺄﺳﻠﻤﺘﻨﻲ ﺇﻟﻴﻪ ﻭﺃﻧﺎ ﻳﻮﻣﺌﺬ ﺑﻨﺖ ﺗﺴﻊ ﺳﻨﻴﻦ
Ma’ana:
… Hakika mahaifiyata Ummu
Ruman ta zo ta same ni alhali ina
lilo tare da kawayena, sai ta kira ni
da karfi, sai na je wurinta ban san
abin da take nufi ba, sai ta kama
hannuna har ta kaini gida, ina ta
haki yayin da na koma cikin
hayyacina, sai ta samu ruwa ta
wanke mini fuskata da kaina,
sannan sai ta shigar da ni gida,
muna shiga sai ga wasu mataye
daga matayen Madina a cikin
gidan, sai suka ce Allah ya sanya
alheri da albarka da rabauta a
cikinsa, sai ta damka ni a
hannunsu, sai suka yi mini
kwalliya, ban farga ba sai ga ni a
wajen Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama a lokacin hantsi,
sai suka mika masa ni a lokacin ina
da shekara tara.
2- Haka kuma hadisi ya tabbata
daga Nana Asma’u Bint Yazid ﺭﺿﻲ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ta ce:
…ﺍﻧﻲ ﻗﻴﻨﺖ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﻟﺮﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭ
ﺳﻠﻢ ﺛﻢ ﺟﺌﺘﻪ ﻓﺪﻋﻮﺗﻪ ﻟﺠﻠﻮﺗﻬﺎ ﻓﺠﺎﺀ ﻓﺠﻠﺲ ﺇﻟﻰ
ﺟﻨﺒﻬﺎ ﻓﺄﺗﻰ ﺑﻌﺲ ﻟﺒﻦ ﻓﺸﺮﺏ ﺛﻢ ﻧﺎﻭﻟﻬﺎ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭ ﺳﻠﻢ ﻓﺨﻔﻀﺖ ﺭﺃﺳﻬﺎ ﻭﺍﺳﺘﺤﻴﺖ ﻗﺎﻟﺖ
ﺃﺳﻤﺎﺀ ﻓﺎﻧﺘﻬﺮﺗﻬﺎ ﻭﻗﻠﺖ ﻟﻬﺎ ﺧﺬﻱ ﻣﻦ ﻳﺪ ﺍﻟﻨﺒﻲ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭ ﺳﻠﻢ ﻗﺎﻟﺖ ﻓﺄﺧﺬﺕ ﻓﺸﺮﺑﺖ
ﺷﻴﺌﺎ …
Ma’ana:
… Na yi wa Nana A’isha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻨﻬﺎ kwalliya na kaiwa Manzon
Allah sallallahu alaihi wa sallama
ita, don ya duba kwalliyarta. Sai
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya zo ya zauna kusa da
ita, sai aka kawo masa kwaryar
nono, sai Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama ya sha sannan
ya mika mata, sai kunya ta kamata,
sai ta sunkuyar da kanta, sai Nana
Asma’u ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ta ce: sai na yi
mata tsawa kuma na ce da ita ki
karba daga hannun Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama, sai
(Nana Asma’u ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ) ta ce:
sai (Nana A’isha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ) ta
karba ta sha dan kadan …
3- Kuma hadisi ya tabbata daga
Anas Ibn Malik radhiyallahu anhu
cewa; yayin da ake dawowa daga
Khaibar, Ummu Sulaim ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ
ta yi wa Nana Safiyya ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ
kwalliya ta mikawa Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ita a
ranar tarewarta da daddare.
Saboda haka wadannan hadisai
sun nuna mana cewa idan har
kamu shine a killace mace a yi
mata ado ko a koya mata yadda za
ta tsabtace jikinta yayin da za a
kaita gidan miji, to, wannan babu
laifi a cikinsa, musamman a yanzu
da mafi yawan `yan mata ba a
damu da koya musu yadda za su yi
ado ko kwalliya ko gyara ko
tsaftace jikinsu ba, idan ka ga sun
yi tsafta, to, sai idan za a fita
unguwa, wanda hakan kuma ci
baya ne ba kadan ba, Allah shi ne
mafi sani.
TAMBAYA:
Mene ne matsayin hudubar da ake
yiwa amarya a ranar da za a kai ta
gidan miji?
AMSA:
Shari`a ba ta hana yin hakan ba,
matukar za a yi nasiha kyakkyawa
ga ango da amarya, a kan riko da
addini da riko da igiyar aure bisa
da’a ga Allah subhanahu wa ta’ala
da bin Sunnar Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama da rike
amana da yin hakuri da juna da
kyakkyawar zamantakewa
tsakaninsu. Domin ya tabbata
cewa Anas Ibn Malik radhiyallahu
anhu ya kasance yayin da duk zai
aurar da `yarsa yana yi wa angon
nasiha da cewa:
Ka rike ta da kyautatawa da igiyar
Allah.
Kuma ya tabbata cewa Abdullahi
Ibn Abbas da Abdullahi Ibn Umar
radhiyallahu anhuma da sauran
magabata na kwarai, duk suna yin
haka.
A nan muke nasiha da a daina yin
munanan hudubobi kamar yadda
tsofaffi da wasu dangin amarya
sukan yi cewa, kada ta sakarwa
mijinta jiki ya raina ta, ko kuma
fadarsu cewa: Duk wadda ta riki
namiji uba za ta mutu marainiya!
Da dai sauran munanan
shawarwari, domin wannan ba ya
haifar da komai face rage soyayya,
da haifar da tsana da rigingimu da
ka iya kaiwa ga mutuwar aure tun
da wuri. Allah Ya fahimtar da mu,
amin.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories